Najeriya Ta Jawo wa Kanta, Amurka Ta Shirya Dakike duk Wani Tallafi ga Ƙasar

Najeriya Ta Jawo wa Kanta, Amurka Ta Shirya Dakike duk Wani Tallafi ga Ƙasar

  • Majalisar Wakilan Amurka ta amince da kudirin dakatar da duk tallafin Amurka ga ƴan Najeriya da kasar baki daya
  • Masana sun gargadi cewa idan kudirin ya zama doka, shirye-shiryen HIV, tarin fuka, zazzabin cizon sauro, rigakafi da lafiyar mata da yara za su shiga hadari
  • Sun bukaci gwamnatin Najeriya ta inganta tsaro, karfafa dangantaka da Amurka, tare da samar da hanyoyin cikin gida domin daukar nauyin lafiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington DC, US - Majalisar Wakilan Amurka ta amince da kudirin dakatar da kashi 100 cikin 100 na tallafin da Amurka ke bai wa Najeriya.

Wannan matakin ya biyo bayan zargin kashe Kiristoci da tabarbarewar tsaro duk da cewa kudirin bai zama doka ba tukuna.

Amurka ta shirya janye dukkan tallafinta ga Najeriya
Shugaba Bola Tinubu da takwaransa na Amurka, Donald Trump. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Donald J Trump.
Source: Getty Images

Amurka ta shirya ƙuntata wa Najeriya

Kara karanta wannan

Trump ya kara tsaurara matakan kasuwanci, ya laftawa Najeriya haraji

Idan Majalisar Dattawan Amurka ta amince da shi kuma Shugaba Donald Trump ya sanya hannu, masana sun ce hakan na iya jefa Najeriya cikin babbar matsalar jin kai da kiwon lafiya, cewar Vanguard.

Dan majalisar Gregory Steube ne ya gabatar da gyaran kudirin yayin nazarin kasafin Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka na shekarar kasafin 2027, inda ya ce masu biyan harajin Amurka ba za su tallafa wa gwamnatin da ta kasa kare Kiristoci ba.

Sabon kudirin ya sauya tsohon shirin dakatar da rabin tallafi zuwa cikakken dakatarwa har sai Sakataren Harkokin Wajen Amurka ya tabbatar Najeriya ta dauki matakan dakile hare-hare tare da hukunta masu laifi.

Tsawon fiye da shekaru 20, Najeriya ta kasance cikin manyan kasashen da ke karbar tallafin Amurka.

Kasar ta samu dala biliyan 1.16 a 2022, dala biliyan 1.02 a 2023, sannan kusan dala miliyan 767 a 2024, cewar Punch.

Zargin kisan Kiristoci a Najeriya zai jawowa kasar matsala
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Twitter

Yawan tallafin da Amurka ke ba Najeriya

Tallafin ya taimaka wajen kula da fiye da mutane miliyan 1.5 masu dauke da HIV, ba da magungunan zazzabin cizon sauro ga yara miliyan 2.2 da yi wa 'yan mata miliyan 13 rigakafin HPV.

Kara karanta wannan

Kotu ta ɗaure wani mutumi a gidan kaso bayan kisan ƴar majalisa da mijinta

Haka kuma Amurka ta tallafa wajen gwajin tarin fuka ga mutane miliyan 19.8, horas da jami'an lafiya, bunkasa noma, ilimi, ruwa, tsafta, gyaran tsaro da zuba jari masu samar da ayyukan yi.

A bangaren tsaro, Amurka ta bayar da dala miliyan 40 na tallafin soja, ta horas da jami'an rundunar Najeriya, sannan ta tallafa wajen samar da tsarin gargadin rikice-rikice da gyaran bangaren shari'a.

Shugaban PHSAI, Barrista Ayo Adebusoye, ya ce duk da cewa kudirin bai zama doka ba, ya kamata gwamnatin Najeriya ta dauke shi a matsayin babban gargadin diflomasiyya.

Ya ce matsalar ba ta shafi addini kadai ba, domin Musulmai, Kiristoci, manoma, ma'aikatan agaji da sauran 'yan Najeriya ne ke fuskantar hare-haren ta'addanci da garkuwa da mutane.

Ta'addanci: Trump ya yaba wa Tinubu

Mun ba ku labarin cewa Donald Trump na Amurka ya yaba wa shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu kan jajircewarsa wajen yaki da ’yan ta’adda.

Shugaban na Amurka ya ce dangantakar Amurka da Najeriya na da muhimmanci wajen yaki da ta’addanci.

Donald Trump ya ce Amurka za ta ci gaba da tattaunawa da Najeriya kan hadin gwiwar tsaro domin dakile ayyukan 'yan ta'adda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.