Majalisar Amurka Ta Gabatar da Kudurin da Zai Jawo Babbar Matsala ga Najeriya

Majalisar Amurka Ta Gabatar da Kudurin da Zai Jawo Babbar Matsala ga Najeriya

  • Majalisar Wakilan Amurka ta amince da kudirin dakatar da gaba daya tallafin da kasar ke bai wa Najeriya har sai tsaro ya inganta
  • Dan majalisar wakilai a Amurka, Gregory Steube ya zargi gwamnatin Najeriya da gaza kare rayuka da dukiyoyin al'umma
  • Har yanzu kudirin bai zama doka ba, domin yana bukatar kammala matakan majalisa kafin zartar da shi a hukumance

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Amurka - Majalisar Wakilan Amurka ta amince da wani gyaran kudiri da ke neman a dakatar da duk wani tallafin da ake bai wa Najeriya.

Majalisar na son dakatar da tallafin har sai gwamnatin Najeriya ta dauki ingantattun matakai wajen dakile tashe-tashen hankula da kuma hukunta masu aikata miyagun laifuffuka.

Gregory Stuebe.
Dan Majalisar Amurka, Gregory Stuebe, wanda ya gabatar da kudirin dakatarda tallafin da kasar ke ba Najeriya Hoto: Pool
Source: Getty Images

An gabatar da kudirin a Majalisar Amurka

Ɗan majalisa mai wakiltar mazabar Florida ta 17, Gregory Steube, ne ya gabatar da kudirin a ranar Laraba da ta wuce, kamar yadda The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

'Amfanin da soke ba da tallafin Amurka zai yi ga Najeriya' in ji Jigon APC

Daga bisani mambobin majalisar wakilan ta Amurka suka amince da shi ta hanyar kada kuri'ar murya.

Tun a watan Afrilu ne majalisar ta fara gabatar da kudirin da ke neman a dakatar da kashi 50 cikin 100 na tallafin Najeriya har sai Ministan Harkokin Wajen Amurka ya tabbatar gwamnatin Najeriya ta dauki matakan kare rayuka.

Dalilin neman dakatar da tallafin Najeriya

Da yake kare kudirinsa, Steube ya ce dakatar da rabin tallafin kawai tamkar lada ne ga gwamnatin Najeriya duk da gazawarta wajen kare rayukan al'umma.

Ya ce:

"Ina goyon bayan kudirin da ke neman a kara yawan tallafin da za a dakatar daga kashi 50 cikin 100 zuwa 100%. Najeriya ta fuskanci mummunar matsalar tsaro wadda gwamnatin kasar ta gaza magancewa."

Zargin ana cin zarafin Kiristoci

Steube ya yi zargin cewa Kiristoci da sauran tsiraru masu bin addinI suna ci gaba da fuskantar hare-hare daga masu tsattsauran ra'ayin Islama.

A cewarsa:

"Ana ci gaba da sace mata da 'yan mata Kiristoci, ana cin zarafinsu, ana azabtar da su har ma ana kashe su. Ana kona coci-coci, ana kuma rusa garuruwa baki daya."

Kara karanta wannan

Masanin da ya yi tsayuwar daka yana kare Musulunci a Amurka ya rasu

Tinubu da Trump.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da shugaban Amurka, Donald Trump Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Ya ce idan sharuddan da aka gindaya suna da muhimmanci har za a dakatar da rabin tallafin, to ya kamata a dakatar da dukkan tallafin da ake turawa Najeriya baki daya.

A rahoton PM News, Dan majalisar ya ce bai dace kudin harajin Amurkawa ya rika zuwa ga gwamnatocin da suka kasa kare 'yancin addini, yaki da ta'addanci da kuma kare rayukan fararen hula ba.

Sai dai duk da amincewar Majalisar Wakilai da wannan gyaran kudiri, har yanzu bai zama doka ba, domin akwai sauran matakan majalisa da kuma amincewar hukumomin da suka dace kafin ya fara aiki.

Wani malamin lafiya da ke ayyukan riga-kafi a Katsina, Shu'aibu Sa'adu ya ce dakatar da tallafin Amurka a Najeriya musamman a bangaren lafiya babbar barazana ce.

Da yake hira da wakilin Legit Hausa, ya ce wanda aka dakatar a kwanakin baya kadai ya kawo tangarda a harkokin riga-kafi, yana mai cewa bai kamata a rike gaba daya tallafin ba.

Kara karanta wannan

Tinubu ya sanya hannu kan wata sabuwar doka, ta shafi harkokin kudade a intanet

"Ina kyautata zaton kusan mafi yawan tallafin da muke samu ta bangaren riga-kafi yana zuwa ne daga Amurka, bani da tabbas amma lokacin da aka ce sun rage 50% akwai magungunan da aka daina kawo mana.
"Don haka muna kira ga gwamnatin Najeriya ta dauki matakin magance matsalar tsaro domin komai ya ci gaba da tafiya daidai," in ji shi.

Amurka ta kara jan hankalin Najeriya

A baya, kun ji cewa gwamnatin Amurka ta bukaci Najeriya ta kara kaimi wajen kare Kiristoci daga hare hare tare 'yan bindiga da sauran 'yan ta'adda.

Haka kuma gwamantin kasar ta bukaci a hanzarta dawo da mutanen da rikice-rikice suka raba da muhallansu zuwa gidajensu lami lafiya.

Ta isar da wannan sako ne yayin ziyarar da Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Amurka mai kula da nahiyar Afrika, Frank Garcia, ya kai Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262