An Gano Kasashe 3 da Gwamnatin Tinubu Ta Yi Nazarinsu don Kafa Ƴan Sandan Jihohi
- Sufeto Janar na 'Yan Sanda, Olatunji Disu, ya ce kwamitin da ya tsara tsarin 'yan sandan jihohi ya yi nazarin yadda ake gudanar da su a kasashe uku
- Disu ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta na da yakinin cewa kafa 'yan sandan jihohi zai bada gudunmawa wajen kare rayuwa da dukiyoyi
- Ya ce an kammala tsarin farko cikin kwanaki 17, kuma yanzu ana ci gaba da tattaunawa domin ƙara masa inganci kafin aiwatar da shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida
Abuja - Sufeto Janar na Rundunar 'Yan Sandan Najeriya, Olatunji Disu, ya bayyana cewa kwamitin da rundunar ta kafa domin tsara tsarin 'yan sandan jihohi ya yi nazarin yadda ake gudanar da irin wannan tsari a ƙasashen Indiya, Amurka da Pakistan.
Disu ya bayyana hakan ne a wani taron bitar da aka gudanar a Abuja ranar Alhamis domin wayar da kan manyan jami'an rundunar kan shirin kafa 'yan sandan jihohi da kuma tattauna yadda za a aiwatar da sabon tsarin.

Source: Twitter
Ya ce kwamitin ya gudanar da cikakken bincike kan yadda ƙasashen da ke amfani da tsarin 'yan sandan jihohi ke tafiyar da harkokinsu domin samar da tsarin da zai dace da yanayin Najeriya, in ji rahoton Punch.
Kudurin gwamnati kan kafa 'yan sandan jihohi
A cewar Sufeto Janar ɗin, gwamnatin tarayya ta riga ta yanke shawarar kafa tsarin 'yan sandan jihohi, saboda haka ya zama wajibi rundunar ta taka rawar da ta dace wajen ganin an aiwatar da shi cikin nasara.
Ya ce:
"Za mu tattauna kan wani muhimmin batu da ya shafi 'yan sandan jihohi. Batu ne da yake jan hankali a Najeriya da sauran sassan duniya.
"Muna jagorantar ɗaruruwan jami'ai da dole su fahimci abin da tsarin 'yan sandan jihohi yake nufi domin rage fargabar da ake da ita game da wannan tsari."
Disu ya ƙara da cewa kafa 'yan sandan jihohi ba batun rundunar kaɗai ba ne, illa wani muhimmin shiri ne na gwamnatin tarayya da ya shafi makomar tsaron ƙasa.
Yadda aka shirya tsarin cikin kwanaki 17
Sufeto Janar ɗin ya tuna cewa a lokacin da aka fara tattauna batun, wasu sun yi ra'ayin cewa babu buƙatar rundunar ta samar da nata tsarin tunda gwamnati ta riga ta yanke hukunci.
TVC News ta rahoto cewa, Disu ya ce daga ƙarshe an amince da kafa kwamitin domin samar da tsarin da zai taimaka wajen aiwatar da manufar cikin tsari.
A cewarsa:
"Na yi farin ciki da muka amince da kafa kwamitin. Mun kammala tsarin farko cikin kwanaki 17 kacal, kuma wannan shi ne tubalin abin da ake tattaunawa a kai a yau."

Source: Twitter
Ya yi magana kan kwamitin gwamnoni
Disu ya bayyana cewa Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya ta riga ta kafa nata kwamitin kan batun kuma ta kusa kammala aikinta kafin rundunar 'yan sanda ta fara nata aikin.
Sai dai ya ce duk da jinkirin da aka samu, kwamitin rundunar ya yi saurin kammala aikinsa, kuma tsarin da ya samar ne ake amfani da shi wajen ci gaba da tattaunawa kan kafa 'yan sandan jihohi.
Ya kuma buƙaci mahalarta taron su yi nazari mai zurfi kan tsarin tare da bayar da shawarwari da za su ƙara inganta shi domin samar da tsarin da zai yi wa Najeriya amfani.
Ba ruwan 'yan sandan jihohi da zaben 2027
A wani labari, mun ruwaito cewa, gwamnatin Kano ta ce 'yan sandan jihohi ba za su kasance da alaka da zabukan 2027 ba kamar yadda wasu ke fargaba ba.
Hadimin Gwamna a kan kafafen yada labarai, Ahmed S Aruwa ya tabbatar wa Legit cewa akwai dalilan da suka sa dole aka kirkiri yan sandan jihohi.
Ya bayyana cewa jami'an rundunar jihohi ba za su shafe na tarayya da ake da ita ba, saboda haka zai yi wahala a gansu kan akwatunan zabe.
Asali: Legit.ng


