Gwamna Bago Ya Sanya Dokar Hana Fita Ta Sa'o'i 24 bayan Mutuwar Matasa 37 a Ofishin NSCDC

Gwamna Bago Ya Sanya Dokar Hana Fita Ta Sa'o'i 24 bayan Mutuwar Matasa 37 a Ofishin NSCDC

  • Gwamna Umar Bago ya sanya dokar hana fita na tsawon sa’o’i 24 a Minna, babban birnin jihar Neja bayan zanga-zanga kan mutuwar masu haƙar ma’adinai 37
  • An ce masu zanga-zangar sun lalata kadarorin gwamnati, banki, ofisoshin jam’iyyun siyasa da kasuwancin masu zaman kansu
  • Bago ya ce dokar za ta fara aiki nan take bayan sallar Juma’a domin dawo da zaman lafiya da hana ci gaba da lalata kadarori

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Niger, Nigeria - Gwamnan Jihar Neja, Umar Bago, ya sanya dokar hana fita na tsawon sa’o’i 24 a birnin Minna bayan barkewar zanga-zanga kan mutuwar matasa masu hakar ma'adanai

Ana zargin masu zanga-zangar sun lalata kadarorin gwamnati da na masu zaman kansu sakamakon mutuwar masu haƙar ma’adinai 37 da ake zargi a hannun Hukumar Tsaro da Kare Fararen Hula ta Najeriya (NSCDC).

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Shugaba Tinubu ya ɗauki zafi kan kutuwar matasa 37 a ofishin hukumar NSCDC

Bago.
Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago Horo: Mohammed Umaru Bago
Source: Twitter

Gwamna Bago ya sanar da dokar a ranar Juma’a yayin wani taron manema labarai, inda ya ce za ta fara aiki nan take bayan sallar Juma’a, kamar yadda Leadership ta rahoto.

Me ya jawo sanya dokar hana fita

A cewar gwamnan, matakin ya zama dole bayan da masu zanga-zangar suka lalata wasu wuraren gwamnati, banki, ofisoshin jam’iyyun siyasa da wuraren kasuwanci masu zaman kansu.

“Nan take bayan sallar Juma’a, za mu sanya dokar hana fita na sa’o’i 24 a nan,” in ji Bago.

Ya lissafa wasu daga cikin kadarorin da rahotanni suka ce lamarin ya shafa, yan mai cewa:

“Kamfanin Sufuri na Jihar, duk motocin bas ɗin da muke da su a can an lalata su. An kai wa bankin Sterling, an lalata ofisoshin jam’iyyu, an lalata kasuwancin mutane."

Bago ya ce lamarin ya tsananta har masu lalata kadarori suka mamaye tituna, lamarin da ya sa aka ga buƙatar takaita zirga-zirga domin hana ƙarin barna da dawo da doka da oda.

Kara karanta wannan

Gwamnan Najeriya da ke biyan ma'aikatan shi N500,000 a wata

Gwamna Bago ya yi kira ga jama’a

Gwamnan ya roƙi mazauna jihar Neja da su rungumi zaman lafiya tare da nuna haƙuri yayin da ake ƙoƙarin daidaita al’amura, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Bago.
Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago yana jawabi a wurin taro a Minna Hoto: Mohammed Umaru Bago
Source: Facebook

Dokar hana fitan ta biyo bayan zanga-zangar da aka gudanar a wasu sassan jihar kan mutuwar masu haƙar ma’adinai da ake zargi, waɗanda NSCDC ta tsare.

Tun da farko, Bago ya tabbatar da cewa matasa 37 da ake zargi sun mutu a hannun NSCDC. Ya ce ana gudanar da gwaje-gwajen ƙwararru da na likitoci, ciki har da binciken gawawwaki, domin gano yanayi da kuma musabbabin mutuwar.

Tinubu ya dauki matakin bincike

Kun ji cewa Bola Ahmed Tinubu ya bada umarnin gudanar da bincike na gaskiya kan mutuwar mutanen da ake zargi da haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba a hannun NSCDC.

Shugaban kasar ya kuma ce bai kamata wani ɗan ƙasa ya rasa ransa yana hannun gwamnati saboda sakaci, cin zarafi, rashin tausayi ko gazawar jami’i wajen sauke nauyin da ke kansa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262