An Farmaki Magoya Bayan Kwankwaso da Obi a Wurin Gangamin Siyasa, Bidiyo Ya Fito

An Farmaki Magoya Bayan Kwankwaso da Obi a Wurin Gangamin Siyasa, Bidiyo Ya Fito

  • An ruwaito cewa wasu ’yan daba sun kai hari kan tawagar masu goyon bayan Peter Obi da Rabiu Kwankwaso a Warri, Jihar Delta
  • Esther Umoh, mai ɗaukar hotunan Obi, ce ta bayyana zargin, tana cewa mutanen da ake zargin ’yan daba ne masu goyon bayan 'yan siyasa
  • Wani bidiyo da aka wallafa tare da zargin ya nuna mutane suna gudu yayin da ake cikin rudani, amma ba a bayar da bayanin hukuma kan lamarin ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Delta - An ruwaito cewa an kai hari kan wasu magoya bayan ɗan takarar shugaban ƙasa na Nigeria Democratic Congress (NDC), Peter Obi, da abokin takararsa, Rabiu Kwankwaso, yayin wani aikin yaƙin neman zaɓe a Warri, Jihar Delta.

Ana dai zargin wasu 'yan daban siyasa ne suka farmaki magoya bayan na jam'iyyar NDC, lokacin da suke gudanar da wani gangami.

Kara karanta wannan

Dickson: Jagoran NDC na kasa ya fadi dalilin kin shiga APC, ya aika sako ga Kwankwaso da Obi

An farmaki magoya bayan Obi da Kwankwaso
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Peter Obi a wurin taron NDC Hoto: Hon. Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Esther Umoh, mai ɗaukar hotunan Peter Obi, ce ta bayyana lamarin a wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X.

An zargi ’yan daban siyasa da kai harin

Umoh ta yi zargin cewa wasu ’yan daba da aka ɗauki nauyinsu saboda siyasa sun kai hari kan mambobin tawagar yaƙin neman zaɓen yayin da suke gudanar da gangami a Warri.

Ta ce waɗanda abin ya shafa sun haɗa da mambobin tawagar ɗan takarar gwamnan Delta na jam’iyyar, da kuma magoya bayan ƙungiyoyin Obidient da Kwankwasiyya.

“Tun da safiyar yau, an ruwaito cewa wasu ’yan daba da aka ɗauki nauyin siyasa sun buɗe wuta kan @MamaPee__, @Drmopaul, @dchrisiyovwaye, ɗan takarar gwamnan Delta, mambobin tawagarsa da sauran magoya bayan Obidient da Kwankwasiya da suka fita yaƙin neman zaɓe a Warri,” In ji ta.

Bidiyo ya nuna mutane suna gudu

Umoh ta wallafa wani bidiyo tare da zargin harin, wanda ya nuna wasu mutane suna gudu yayin da ake cikin wani yanayi na rudani.

Kara karanta wannan

Tirkashi: ADC ta bankado makarkashiyar da ake kullawa a Arewa gabanin zaben 2027

A cikin bidiyon, an ji wata murya tana cewa:

“Ku kalli ’yan daban, sun zo ne domin su kawo mana hari. Dole mu fuskance su. Mun shirya tsaf domin su.”

Sai dai bayanin da aka bayar bai fayyace ko akwai wadanda suka jikkata ko suka rasa rayukansu ba.

Ana ci gaba da shirye-shiryen zaɓen 2027

Rahoton harin ya zo ne yayin da magoya bayan Peter Obi da Rabiu Kwankwaso ke ci gaba da ƙara kaimi wajen shirye-shiryen babban zaɓen 2027.

Ana gudanar da tafiyar Obi da Kwankwaso ne ƙarƙashin tutar NDC, yayin da mambobin ƙungiyoyin Obidient da Kwankwasiyya ke taka rawa wajen faɗaɗa tsarin siyasar tasu.

A baya-bayan nan, ƙungiyar masu goyon bayan Obi da Kwankwaso ta sanar da kafa kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa mai mambobi 59, wanda ya ƙunshi masu kula da harkoki da daraktoci daga sassa daban-daban na ƙasar.

Kalli bidiyon a nan:

An farmaki magoya bayan Obi da Kwankwaso a Delta
Taswirar jihar Delta, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Kwankwaso ya yi Allah wadai da kisan Dan Shagamu

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana matuƙar damuwarsa kan kisan shahararren mai sharhin siyasa a kafafen sada zumunta, Ibrahim Khalil Dan Shagamu.

Kwankwaso ya buƙaci hukumomin Kano su gudanar da bincike cikin tsanaki domin gano waɗanda suka aikata kisan tare da gurfanar da su a gaban kotu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng