Matatar Dangote Ta Fito da Tsari, duk Wanda Ya Sayi Hannun Jari Zai Iya Samun Kyauta Mai Gwabi
- Matatar Dangote ta bullo da hanyar da duk wanda ya sayi hannun jarinta guda 10 zai iya samun karin guda daya kyauta
- Ta bayyana cewa za ga ba masu zuba jari da suka cancanta ƙarin guda ɗaya na kan kowane hannun jari 10 da suka riƙe na tsawon watanni 12
- Shirin zai bai wa masu zuba jari damar samun ƙarin kaso biyu cikin shekaru biyu na farko bayan fara sayar da hannun jarin kamfanin a kasuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Lagos, Nigeria - Matatar Dangote za ta raba wasu hannayen jari kyauta ga masu zuba jari da suka cika sharuddan da ta gindaya.
Matatar ta ce za ta ba masu zuba jari da suka cancanta guda ɗaya kan kowane hannun jari 10 da suka riƙe na tsawon watanni 12 a shekaru biyu na farko bayan fara hada-hadar hannayen jarin.

Kara karanta wannan
"Bana son a kara kirana wanda ya fi kowa kudi a Afrika"; Dangote ya fadi sunan da yake so

Source: Facebook
Dangote ba fara sayar da hannun jari
Premium Times ta ce Chuka Eseka, Shugaba na kamfanin Vetiva Capital Management, da ke jagorantar harkar sayar da hannun jarin matatar Dangote, ne ya bayyana hakan ranar Litinin.
Matatar Dangote ta buɗe damar shigar da bukatun sayen hannun jari ranar Litinin, 14 ga watan Satumba, 2026, wanda zai ɗauki tsawon wata guda domin tara jari daga masu zuba jari a faɗin Afirka.
Bisa ga takardar tsarin, matatar Dangote za ta sayar da hannun jari na yau da kullum guda biliyan 4.1, inda aka sanya farashin kowane guda daya a N525, kuma za a rufe saye a ranar 13 ga Oktoba.
Yadda mutane za su samu kyauta
A cewar Eseka, ƙarƙashin shirin ƙarfafa gwiwar masu zuba jari, masu zuba jari da suka sayi aƙalla kaso 10 kuma suka riƙe su ba tare da katsewa ba na tsawon watanni 12 za su samu ƙarin guda ɗaya kyauta.
Mutanen da suka ci gaba da riƙe hannun jarin na wasu watanni 12 za su samu ƙarin kaso na biyu, wanda zai ba waɗanda suka cancanta damar samun ƙarin hannun jari biyu cikin shekaru biyu.
Eseka ya ce an tsara shirin ne domin ƙarfafa gwiwar ‘yan Najeriya su shiga cikin wannan kasuwsnci tare da ci gaba da riƙe hannun jarin na dogon lokaci.
“Shiri ne na ƙarfafa gwiwar mutane, domin ka cancanta, dole ne ka sayi aƙalla guda 10. Idan ka riƙe waɗannan guda 10 ba tare da sayar ba ba na tsawon watanni 12, za ka samu ƙarin guda ɗaya.
“Idan kuma ka ci gaba da riƙe su na wasu watanni 12 bayan haka, za ka samu ƙarin kaso ɗaya. Don haka za ka iya samun ƙarin hannun jari biyu daga wannan shirin na ƙarfafa gwiwar masu zuba jari,” in ji shi.
Eseka ya bayyana cewa mutanen da suka sayi hannun jarin a kasuwar hannun jaribayan an fara sayar da shi a kasuwa ba za su cancanci samun ƙarin hannun jarin ba.

Source: Getty Images
Hannun jarin matatar Dangote zai yi daraja
Kun ji cewa Attajiri Aliko Dangote ya ce hannayen jarin matatar Dangote da za a fara sayarwa kan N525 na iya kai wa N10,000 kowace guda daya nan gaba.
Dangote ya kuma tabbatar wa kananan masu zuba jari da ke shirin shiga sayar da hannayen jarin matatar a karon farko, IPO, cewa za a ba su fifiko wajen rabo.
Asali: Legit.ng
