Wike ya caccaki faston da ya cire tsoro ya fadawa Tinubu gaskiya

Wike ya caccaki faston da ya cire tsoro ya fadawa Tinubu gaskiya

  • Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ce Cardinal John Onaiyekan bai kasance wanda bai goyon bayani wani bangare ba a a lokacin babban zaben 2023
  • Wike ya ce ya kamata shugabannin addini su rika yaba wa gwamnati idan ta yi abin kirki tare da sukar inda ta gaza
  • Ministan ya dage cewa wasu shugabannin addini sun fito fili sun goyi bayan wasu 'yan takara a zaben shugaban kasa na 2023

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Ministan babban birnin tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya kalubalanci tsohon Archbishop na Cocin Katolika na Abuja, Cardinal John Onaiyekan.

Wike ya ce malamin addinin bai kasance wanda bai goyi bayan wani bangare ba a lokacin babban zaben Najeriya na shekarar 2023.

Wike ya soki Cardinal Onaiyekan
Nyesom Wike na jawabi ga manema labarai Hoto: @OlayinkaLere
Source: Facebook

Ministan ya bayyana haka ne a yayin ganawarsa da manema labarai ranar Talata, 4 ga watan Agustan 2026 yayin da yake martani kan ce-ce-ku-cen da suka biyo bayan kalaman Onaiyekan, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan

Wike zai hana sana'ar acaba da masu adaidaita sahu aiki a birnin Abuja

Onaiyekan ya ragargaji Tinubu

Kalaman Cardinal Onaiyekan sun biyo bayan wata ganawa da Shugaba Bola Tinubu ya yi da mambobin taron Bishof-bishof na Katolika a Najeriya (CBCN).

Bayan ganawar, Cardinal Onaiyekan a wata hira ya ce mutanen da ke kewaye da Shugaba Tinubu suna gabatar masa da “kyakkyawan hoto” game da halin da kasar ke ciki.

Ya kuma nuna cewa shugaban kasar ya fi mayar da hankali kan tabbatar da nasara a zaben shugaban kasa na 2027, The Punch ta kawo labarin.

Fadar shugaban kasa ta soki Onaiyekan kan bayyana bayanan ganawar da aka yi a sirrance, tana mai cewa hakan cin amanar amana ne.

Wike ya nemi daidaito

Da yake martani kan lamarin, Wike ya ce ya kamata kalaman shugabannin addini a bainar jama'a su kasance masu daidaito.

Ya yi gargadin cewa yawan sukar gwamnati ba tare da amincewa da nasarorin da ta samu ba na iya sa a dauki maganganun a matsayin masu alaka da siyasa.

Kara karanta wannan

Faston da ya buga da Tinubu a fadar shugaban kasa ya sake magana

“Idan ana kallon wani shugaban addini ko kuma ana ganin yana goyon bayan wani bangare, kuma hakan ya fito fili, zai yi matukar wahala mutane su rika ganin irin wadannan kalamai suna da amfani.”
“Na san matsayar Cardinal Onaiyekan. Dukkanmu mun sani, ba boyayyen abu ba ne, wanda yake goyon baya. Kowa ya sani.”

- Nyesom Wike

Ya bukaci a yaba wa gwamnati

Ministan FCT ya ce duk da cewa ya dace a soki gwamnati idan akwai bukatar hakan, ya kamata shugabanni su kuma amince da bangarorin da aka samu ci gaba.

“Ba wai a ko da yaushe za ka rika cewa komai ba daidai ba ne. Babu wanda ya taba jin ka ce gwamnati ta yi wannan abu da kyau.”
“Abin da nake kokarin fada shi ne, a matsayinka na shugaba, ka yaba wa gwamnati idan ta yi abin kirki a wasu bangarori. Ka soki gwamnati ka ce, ga abin da kuka yi da kyau, amma ya kamata ku inganta wadannan sauran bangarori.”

- Nyesom Wike

Wike ya caccaki Onaiyekan
Nyesom Wike na jawabi a wajen taro Hoto: Kashim Shettima
Source: Facebook

Wike ya ce idan kalaman wani mutum mai daraja a bainar jama'a suna kasancewa marasa kyau a ko da yaushe, gwamnati za ta iya ganin sukar ta samo asali ne daga adawar siyasa, ba tsaka-tsaki ba.

Kara karanta wannan

Fadawa Tinubu 'gaskiya' na neman jefa malaman addini a cikin matsala

Dalilin rashin farin jinin Wike

A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana dalilin da ya sa ba ya samun farin jini a tsakanin ma'aikatan gwamnati.

Wike ya ce hakan ya samo asali ne daga matakan da ya dauka na rufe hanyoyin da ake amfani da su wajen karkatar da kudaden jama'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng