Malam Murtala Bello Ya Faɗi Shirinsu da Aka Kai wa Sheikh Lukuwa Hari a Sokoto
- Babban malamin Musulunci a Sokoto, Murtala Bello Asada, ya fusata kan harin da aka kai wa Sheikh Musa Lukuwa bayan sallar Juma’a
- Asada ya yi kira ga Musulmi su kasance cikin shiri, yana mai cewa za su mayar da martani idan aka kai wa malami hari
- Sheikh Musa Lukuwa ya kwantar da hankalin mabiyansa, yana mai cewa yana cikin koshin lafiya kuma babu wata matsala da take damunsa bayan harin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Sokoto - Babban malamin musulunci a Sokoto, Malam Murtala Bello Asads ya magantu kan abin da ya faru a Sokoto.
Murtala Bello ya bayyana fushinsa kan farmaki da aka kai wa Sheikh Musa Lukuwa bayan sallar Juma'a a Sokoto.

Source: Facebook
Malamin ya bayyana haka ne a cikin wani bidiyo da wakilin Legit Hausa a shafinsa na Facebook a yau Juma'a 11 ga watan Satumbar 2026.

Kara karanta wannan
An dauki mummunan mataki kan malamin addini bisa zargin batanci ga iyayen manzon Allah
Yadda aka kai wa Sheikh Lukuwa hari
An tabbatar da cewa an caka wa Sheikh Musa Lukuwa wuka ne jim kaɗan bayan ya kammala jagorantar Sallar Juma’a a wani yanki na birnin Sokoto ranar Juma’a.
Rahotanni sun ce harin ya biyo bayan zargin wasu kalaman batanci da aka danganta wa malamin game da iyayen Annabi Muhammad (SAW).
anda ake zargin ya kai harin ya mutu bayan wasu daga cikin mabiyan Sheikh Lukuwa sun far masa, yayin da malamin ke karɓar magani a asibiti.
Murtala Bello ya bayyana cewa sun shirya tsaf domin daukar mummunan mataki idan har wani abu ya faru da babban malamin Musulunci a Sokoto.
A cewarsa:
"Don haka yan uwa Musulmi idanun mu a bude suke, wallahi duk wanda ya lashe mana malami sai mun kashe shi.
"Allah madaukakin Sarki ya ce duk wanda ya aika muku, ku afka masa gwargwadon yadda ya yi muku."

Source: Original
Martanin Sheikh Lukuwa bayan kai masa hari
Sheikh Lukuwa ya yi martani bayan kai masa hari jim kaɗan bayan kammala sallar Juma'a a Sokoto.
Malamin ya ba masoya hakuri tare da yi masu albishir cewa babu abin da ke damunsa a yanzu inda ya yi godiya na musamman ga al'umma da suka nuna masa goyon baya.
Malamin ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo da shafin Murtala Bello Asada ya saka a Facebook da yammacin yau Juma'a 11 ga watan Satumbar 2026.
Ya ce:
"Jama'a kowa ya kwantar da hankalinsa ina cikin koshin lafiya, lafiya lau ban da wata matsala.
"'Lafiya lau nake jin jiki na, Allah ya bani kariya kuma da godiya da ƙoƙarin da kuka yi, amma lafiya lau nake ban da wata matsala, Allah ya saka muku da alheri."
Murtala Bello ya yi magana da Turji
A baya, mun ba ku labarin cewa fitaccen malamin addinin musuluncin nan na Sakkwato, Sheikh Murtala Bello Asada ya tattauna da Bello Turji ta wayar tarho.
Wannan na zuwa ne yayin da ake yada rahotannin cewa kasurgumin dan bindigar ya shirya mika duka makamansa don a zauna lafiya.
Sheikh Asada ya yi magana da Turji ne domin tabbatar da aniyarsa ta neman zaman lafiya kuma sun yi hira mai tsayi kan hakan.
Asali: Legit.ng

