Sanata Yari Ya Fadi Dalilin da Ya Sa Arewa ba Za Ta Juyawa Tinubu Baya ba a 2027
- Abdulaziz Yari ya ce ya kamata ’yan Arewa su mara wa Tinubu baya a 2027 saboda yadda ya taimaka wajen ganin Muhammadu Buhari ya kammala wa’adinsa
- Yari ya tuna cewa Tinubu ya ƙi tsayawa takara a 2019, yana mai cewa lokacin Arewa ne, sannan ya ci gaba da goyon bayan Buhari
- Daraktan yaƙin neman zaɓen na APC ya ce kwamitin ba ya neman Tinubu ya yi wa'adi biyu saboda tsarin karba-karba kawai, sai don ganin ya ci gaba da ayyukansa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Legas - Darakta-Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na APC, Abdulaziz Yari, ya yi magana kan tazarcen Shugaba Bola Tinubu.
Sanata Yari ya ce babu wani dalilin da zai sa ’yan Arewa su ƙi goyon bayan Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.

Source: Twitter
Yari ya bayyana hakan ne ranar Litinin a Legas, lokacin da ya jagoranci mambobin kwamitin zuwa fadar Oba na Legas, Rilwan Akiolu, cewar rahoton jaridar TheCable.
Yari ya tuna da goyon bayan Tinubu ga Buhari
Tsohon gwamnan na Zamfara ya ce Tinubu ya taka muhimmiyar rawa wajen ganin marigayi Shugaba Muhammadu Buhari ya samu damar zama shugaban ƙasa da kuma sake lashe zaɓe.
Ya ce saboda haka ya kamata ’yan Arewa su rama wannan alheri ta hanyar mara wa Tinubu baya domin ya sake lashe zaɓen 2027.
“A gare mu da muke Arewa, ina ganin lokaci ya yi da za mu rama wa Tinubu saboda ya ba Arewa damar kammala cikakken wa’adinta.” In ji shi.
Ya tuna cewa a shekarar 2019 wasu masu neman mulki a cikin APC sun yi ƙoƙarin shawo kan Tinubu ya tsaya takarar shugaban ƙasa.
Sai dai Sanata Yari ya ce Tinubu ya yi watsi da matsin lambar, yana mai cewa lokacin Arewa ne.
“Tinubu ya goyi bayan Buhari”
Sanata Yari ya ce Tinubu ya bayyana cewa muddin Buhari zai fito ya nemi goyon bayan jama’a domin sake zaɓensa, zai ci gaba da mara masa baya.
Ya ce Tinubu ya cika wannan alkawari, domin ya ci gaba da goyon bayan Buhari a lokacin da yake buƙatar hakan.
Saboda haka, Yari ya ce babu wani uzuri da zai sa ’yan Arewa su ƙi goyon bayan Tinubu a ƙoƙarinsa na neman wa’adin mulki na biyu.
“Za mu tabbatar da tafiyar Tinubu ta ci gaba”
Sanata Yari ya ce babu dalilin da zai sa yankin Arewa ya ƙi goyon bayan Tinubu domin ya ci gaba da ayyukan da ya fara tare da kammala wa’adinsa.
Ya ce saƙon da yake fitowa daga Arewa shi ne cewa Tinubu na iya dogaro da mutanen yankin wajen ganin tafiyarsa ta siyasa ta ci gaba.

Source: Facebook
Sanata Yari ya yabi Shugaba Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanata Abdulaziz Yari, ya ce babu wani ɗan takarar shugaban ƙasa da ya kai Shugaba Bola Ahmed Tinubu nagarta.
Sanata Yari ya ce duka yan takarar da ke ƙalubalantar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027 ba su kai shi cancanta da ƙwarewa ba.
Asali: Legit.ng

