An Fito da Bayanin Yadda duk Wanda Ya Sayi Hannun Jarin Matatar Dangote Zai Samu Alheri

An Fito da Bayanin Yadda duk Wanda Ya Sayi Hannun Jarin Matatar Dangote Zai Samu Alheri

  • Aliko Dangote ya ce masu zuba jari a matatar Dangote na iya zama miloniya cikin shekara daya ko biyu idan darajar hannayen jarin ta tashi sosai
  • An sanya farashin hannayen jarin matatar kan N525 kowanne, amma Dangote ya ce zai iya tashi zuwa tsakanin N5,000 da N10,000
  • Dangote ya bukaci masu zuba jari su rike hannayen jarinsu domin cin gajiyar ribar da kamfanin zai rika rabawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Shugaban Kamfanin Dangote, Aliko Dangote, ya ce wadanda suka zuba jari tare da rike hannayen jarin matatarsa na iya zama miliyoniya cikin shekara daya ko biyu.

Hamshakin attajirin ya ce mutane na iya samun makudan kudi idan farashin hannayen jarin matatar fetur da suka saya ya samu gagarumar karin daraja a kasuwar duniya.

Kara karanta wannan

Yadda Dangote ya yi shekara 36 yana zaune a gida 1 ba tare da sauya shi ba

Dangote.
Attajirin dan kasuwa da ya fi kowa arziki a nahiyar Afirka, Alhaji Aliko Dangote Hoto: Dangote Group
Source: Getty Images

Dangote ya bayyana hakan ne a wata hira da Arise TV da aka watsa ranar Talata, yayin da yake magana kan fara sayar da hannayen jarin matatar (IPO) a Kasuwar Hannayen Jari ta Najeriya (NGX).

Ana sayar da hannayen jarin matatar Dangote kan N525 kowanne, amma Dangote ya nuna kyakkyawan fata cewa farashin zai iya tashi zuwa tsakanin N5,000 da N10,000, gwargwadon yanayin kasuwa.

Yadda yan Najeriya za su samu kudi

Da aka tambaye shi ko yana sa ran farashin hannun jarin da aka ssys kan N525 zai kai kusan N10,000, Dangote ya ce: “Ina rokon Allah haka ya kasance, eh.”

Da aka tambaye shi ko wannan hasashensa ne, sai ya ce:

“Eh, zai iya kaiwa haka, ka sani, ya danganta da inda kasuwar take. Na taba ganin hannun jari da aka saka a 100 ya tashi zuwa 1,000.”
“Amma namu, zai iya kaiwa watakila 5,000, 10,000. Don haka, abin da kake dubawa shi ne, idan ka zuba kamar N100,000, cikin shekara daya ko biyu, kana magana ne kan zama miloniya.”

Kara karanta wannan

Masu shirin sayen hannun jari a matatar Dangote na cikin matsala, SEC ta fitar da sanarwa

Ya bukaci a rike hannayen jari

Dangote ya bukaci mutane da su rike hannayen jarinsu maimakon sayar da su da wuri, yana mai cewa za su iya cin gajiyar ribar da za a rika rabawa masu hannayen jari a tsawon lokaci.

“To, me ya sa kake son sayar da shi? Ka ci gaba da rike shi, za ka rika karbar kudi,” in ji shi.
Matatar Dangote.
Wani bangaren matatar mai ta Dangote da ke jihar Legas a Najeriya Hoto: @Dangotegroup
Source: Facebook

Yadda aka fara sayar da hannun jarin

Kalaman sun zo ne bayan masu zuba jari sun yi tururuwa zuwa Kasuwar Hannayen Jari ta Najeriya ranar Litinin, yayin da aka fara shigar da bukatun mallakar hannun jari a matatar Dangote.

Mafi karancin adadin da mutum zai iya saya shi ne hannun jari 10, wadanda darajarsu ta kai N5,250. An bude damar ne ranar 14 ga Satumba, 2026, kuma ana sa ran rufe ranar 13 ga Oktoba, 2026.

SEC ta gargadi masu zuba jari

A wani labarin, kun ji cewa hukumar SEC ta gargadi mutanen da ke niyyar zuba jari a matatar Dangote da su guji fadawa hannun yana damfara da shafukan bogi.

A wata sanarwa da ta fitar, SEC ta gargadi masu zuba jari da su yi taka tsan-tsan domin gujewa fadawa hannun manhajojin yan damfara wajen sayen hannun jarin matatar mai ta Dangote.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262