Gwamnatin Anambra Ta Fallasa Peter Obi Ana tsakar Takarar Shugaban Kasa

Gwamnatin Anambra Ta Fallasa Peter Obi Ana tsakar Takarar Shugaban Kasa

  • Gwamnatin Charles C. Soludo ta samu nasarar rage bashin jihar da 83% ba tare da sake karbar wani aron kudi ba
  • Ana cire wa Anambra kudi kai tsaye daga kason FAAC a kowane wata saboda bashin da su Peter Obi suka karbo
  • Kwamishinan kudi ya ce sun biya tsofaffin basussukan kwangiloli da hakkokin ma'aikata a tsawon shekaru hudu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Anambra - Gwamnatin jihar Anambra ta ce har yanzu tana faman biyan bashin da gwamnonin da suka gabata suka ci.

Daga cikin gwamnatocin baya da suka aro kudi a jihar Anambra har da ta Peter Obi wanda ya yi mulki har sau biyu a katse.

Peter Obi
'Dan takaran NDC, Peter Obi da Gwamnan Anambra, Charles Soludo Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Anambra: An zargi gwamnatocin baya da cin bashi

A yammacin Litinin rahoto ya zo daga Premium Times, aka ji kwamishinan kudin Anambra yana kuka da sha’anin bashin jihar.

Kara karanta wannan

'Kashe kashe ya yi yawa': An taso gwamna a gaba sai ya bar kujerarsa

Izuchukwu Okafor ya ce har yau ana cire wa jihar Anambra kudi daga kason da ta ke samu daga rabon FAAC saboda an ci bashi.

Kalaman Mista Izuchukwu Okafor sun ci karo da abubuwan da Peter Obi ya rika fada musamman bayan ya bar gwamnati a 2014.

Tsohon gwamnan ya dade yana ikirarin bai ci bashi lokacin da ya mulki mutanen Anambra ba.

Kwamishinan ya bayyana haka a wani shiri na Voice of Ndi Anambra, kuma yanzu tattaunawar tana ta zagaya wa a kafar Facebook.

Sa-in-sar Willie Obiano da Peter Obi

Sa’ilin da Willie Obiano ya zama gwamna a Anambra a 2014, ya yi da’awar cewa an bar wa jihar nauyin bashin fiye da N180bn.

Mutanen Peter Obi sun karyata shi, suna cewa sun bar dukiya a lalitar gwamnati, kuma sun narka kudin jihar a harkar kasuwanci.

An sha jin magoya bayan Obi suna cewa ya bar $150m a asusun gwamnati, amma alkaluman DMO sun nuna bashinsa aka gada.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya shiga maganar kashe Dan Shagamu a Kano, ya yi kira ga hukuma

Ofishin tattara bashi na kasa (DMO) ya nuna akwai bashin $30m da N3bn da ake bin Anambra a bankunan waje da na gida lokacin.

Gwamnatin Soludo ya jika wa Obi aiki

Daily trust ta ce wannan zance ya kara dawo wa da Charles Soludo ya karbi mulki daga hannun Willie Obiano a shekarar 2022.

Kwamishinan kudin ya ce a kowane wata ana ganin yadda ake zaftare masu kasonsu daga rabon FAAC saboda basussukan baya.

“Kowane wata yayin tarukan mu, idan aka duba rahoton rabon kuɗi FAAC, za a ga cewa ana cire ɗumbin kuɗi masu yawa daga rabonmu saboda bashin da gwamnatocin da suka gabata suka ci a baya.
“An karbo aron kudin nan ne a zamanin Peter Obi, Willie Obiano da sauran tsofaffin gwamnoni.

Gwamna Soludo bai ci bashi a mulkinsa ba

Okafor ya ce gwamnatin Charles Soludo kuwa ba ta taba karbo aro a wani banki ba, a karshe ma yana biyan bashin makudan kudin da ya gada ne.

Kwamishinan ya ce sun rage bashin da ake bin su da kusan 83% kuma duk da haka suna biyan 'yan kwangila da bashin fansho da giratuti.

Kara karanta wannan

Karin kudin fetur babu makawa yayin da ake wayyo lita ta haura N1300

'Dan takaran NDC, Peter Obi
Peter Obi yana kamfe a LP da hoton Gwamna Charles Soludo a Anambra Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Kwaye zanin da Gwamnan Anambra ya yi wa Obi

Kwanaki aka ji Gwamnan Anambra, Charles Soludo, ya caccaki Peter Obi da cewa bai ba jam’iyyar LP damar yin kamfe ba da yake ofis.

Soludo ya bayyana cewa gwamnatinsa ta kyale Obi ya yi amfani da kayayyakin gwamnati sau biyu a jihar kyauta ba tare da biyan ko sisi ba.

Ya kare matakin gwamnatinsa na cire allunan tallan 'yan adawa, yana mai cewa sun bi doka ne wajen daukar wannan matakin gabanin zabe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng