Matsala ga Tinubu: Ana Ganin Atiku Zai Lashe Jihohi 19 a Arewa da 3 Kudu a Zaben 2027
- Kenneth Okonkwo, ya hango cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar zai lashe dukkan jihohi 19 na Arewa a zaben 2027
- Okonkwo, wanda shi ne mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben Atiku, ya ce ADC ta samu gagarumar karbuwa a fadin Arewa
- Ya kuma yi hasashen cewa Atiku zai samu nasara a jihohi uku na Kudu maso Yamma, wato Osun, Ondo da Ogun
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Kenneth Okonkwo, kakakin yakin neman zaben Atiku Abubakar, ya yi hasashen cewa dan takarar ADC zai lashe dukkan jihohi 19 na Arewa da kuma jihohi uku a Kudu maso Yamma a zaben 2027.
A cewarsa, jam’iyyar ADC, wadda ake sa ran Atiku zai tsaya takara a karkashinta, ta riga ta samu isasshen goyon baya a fadin Arewa.

Source: Facebook
Okonkwo ya bayyana hakan ne yayin wata hira da shirin Democracy Today na tashar AIT ranar Litinin, inda yake tantance damar manyan ’yan takarar zaben mai zuwa.
Atiku zai lashe jihohin Arewa 19
“Bari in gaya muku hanyar da Atiku zai bi ya yi nasara. Jihohi 19 na Arewa sun koma ADC, babu shakka a kan haka,” in ji shi.
Okonkwo ya danganta hasashen karuwar goyon bayan adawa da takaicin da jama’a ke nunawa kan manufofin tattalin arzikin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Ya kawo mafi karancin albashi da karin farashin man fetur a matsayin misalan matsin tattalin arzikin da ’yan Najeriya ke fuskanta.
“Wannan gwamnati ba bu hankali a matakan da ta dauka. Ba ta tare da jama’a, kuma jama’a sun fahimci hakan saboda kana biyan mutum N70,000 a matsayin mafi karancin albashi, yayin da man fetur ya mai kusan kai N1,500,” in ji shi.

Kara karanta wannan
Daukar doka hannu: Matasa sun kashe tsoho dan shekara 80 bisa zargin aikata maita
Ya kara da cewa halin da tattalin arzikin kasar ke ciki ya kara wahalar da ma’aikata wajen biyan bukatunsu na yau da kullum.
Ya hango nasara Kudu maso Kudu
Tsohon jigon LP ya kuma yi hasashen cewa adawa za ta samu karin nasara a yankin Kudu maso Kudu, yana mai cewa abokin takarar Atiku na mataimakin shugaban kasa zai jawo musu goyon baya a yankin.
A rahoton Vanguard, Okonkwo ya kara da cewa:
“A Kudu maso Kudu, za mu yi nasara a wasu jihohi, kuma za mu samu fiye da biyu. Sannan za mu samu fiye da kashi 25 cikin 100 a dukkan jihohin Kudu maso Kudu, domin waye ba zai so dan yankinsa ya zama mataimakin shugaban kasa ba?”
Okonkwo ya kara yin hasashen cewa adawa za ta lashe jihohi uku a Kudu maso Yamma, inda ya ambaci Osun, Ondo da Ogun a matsayin jihohin da suke da damar lashewa.

Source: Twitter
ADC ta ja hankalin INEC kan zaben 2027
Kun ji cewa ADáC ta buƙaci INEC ta hana malaman jami’a da aka san suna da ra’ayin siyasa zama jami’an tattarawa da haɗa sakamakon zaɓen 2027.
Sanarwar ta biyo bayan rahotannin cewa sama da manyan malaman jami’a 600 daga jami’o’in gwamnati da ke Arewacin Najeriya sun fito fili sun nuna goyon bayansu ga Bola Tinubu
Asali: Legit.ng
