Wasu Malaman Musulunci Sun Fada Tarkon Yan Bindiga a Hanyar Dawowa daga Taron APC

Wasu Malaman Musulunci Sun Fada Tarkon Yan Bindiga a Hanyar Dawowa daga Taron APC

  • Rahotanni daga Zamfara sun ce ‘yan bindiga sun sace wasu malaman addinin Musulunci shida bayan sun dawo daga gidan Sanata Abdul’aziz Yari
  • Bayanai sun nuna cewa Malaman sun je gidan tsohon gwamnan Zamfara da ke Talaka Mafara ne domin halartar taron addu’a
  • An ce malaman sun fito ne daga ƙananan hukumomin Bakura da Talata Mafara kuma sun fada tarkon yan bindiga ne a hanyar komawa gida

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Zamfara, Nigeria - Rahotannin da ke shigowa daga Zamfara sun ce ‘yan bindiga sun sace wasu malaman addinin Musulunci dhida da aka gayyata zuwa gidan Sanata Abdul’aziz Abubakar Yari.

An ruwaito cewa an gayyaci malaman zuwa gidan Sanata Yarinda ke Talata Mafara a yau, Asabar, 12 ga Satumba, 2026 domin yin addu'a da godiya bisa nada shi Daraktan yakin neman zaben shugaban kasa na APC.

Kara karanta wannan

An fara fito da abubuwan da Tinubu ya shirya yi a Najeriya idan ya lashe zaben 2027

Malamai.
Malaman addinin musulunci a taron da Sanata Abdulaziz Yari ya shirya a gidansa da ke Zamfara Hoto: @Danbakatsina50
Source: Twitter

Wani mai amfani da shafin X wanda ke yawan kawo labaran da suka shafi matsalar tsaro a sassan Najeriya, Bakatsine ya tabbatar da aukuwar lamarim a wani sako da ya wallafa.

Sunayen wasu malamai da aka sace

Rahotannin sun ce malaman da aka ruwaito cewa yan bindiga sun sace sun haɗa da:

  • Limamin Juma’a na farko a masallacin Dogon Madacci, Imam Yahuza
  • Magawata Abdullahi, limamin Juma’a na biyu, Dogon Madacci
  • Malam Shehu Dakko
  • Imam Bala Fagon
  • Na’ibi Tasi’u, Tungar Nagudai

An ce malaman sun kasance a gidan Sanata Yari ne domin halartar taron addu’a. Sun fito ne daga wasu garuruwa da kauyuka da ke ƙananan hukumomin Bakura da Talata Mafara.

Lamarin ya tada hankulan mutane

Lamarin ya jefa mutane cikin matuƙar damuwa, musamman ganin cewa rahotanni sun ce an sace malaman ne yayin da suka je gidan Sanata Yari, tsohon gwamnan Zamfara, kuma Darakta-Janar na yaƙin neman zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu na 2027.

Kara karanta wannan

Melaye ya yi gagarumin gargadi ga Tinubu idan EFCC ta kuskura ta cafke Atiku

A daidai lokacin da matsalar tsaro ke ƙara jefa al’ummomi a faɗin Zamfara cikin mawuyacin hali, wannan lamari ya sake haifar da tambayoyi masu tsanani kan tsaron jama’a a wuraren taruwar mutane.

’Yan bindiga sun sace limaman Musulunci shida a kan hanyar Dakko–Damri da ke ƙaramar hukumar Bakura ta Jihar Zamfara.

Zamfara.
Taswirar jihar Zamfara da ke Arewa maso Yammacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Yan sanda sun fara bincike

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya reshen Jihar Zamfara ta ce ta fara bincike domin gano malaman Addinin Musulunci shida da aka sace a kan hanyarsu ta zuwa Talata Mafara a Zamfara.

Rahotanni dai sun ce malaman suna hanyarsu ta komawa gida bayan zuwa wani taron addu’a na Jam’iyyar APC a Zamfara.

A rahoton TRT Hausa, ‘yan sandan sun ce tuni suka baza jami’ansu domin ceto malaman da aka sace.

Sojoji sun ragargaji yan bindiga a Zamfara

Kun ji cewa rundunar sojin Najeriya ta kai farmakin sama kan wata maboyar ‘yan ta’adda a Yankuzo da ke Ƙaramar Hukumar Tsafe ta jihar Zamfara.

Majiyoyin yankin sun ce lamarin ya faru ne a yammacin ranar 7 ga Satumban 2026, lokacin da jiragen yaƙin soji guda biyar suka gudanar da wani farmaki na haɗin gwiwa a yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262