Masu Shirin Sayen Hannun Jari a Matatar Dangote na cikin Matsala, SEC Ta Fitar da Sanarwa
- Hukumar SEC ta gargadi mutanen da ke niyyar zuba jari a matatar Dangote da su guji fadawa hannun yana damfara da shafukan bogi
- Matatar hamshakin attajirin ta bude damar sayar da hannayen jari, inda ta kayyade farashin kowane hannun jari kan N525
- SEC ta bukaci masu zuba jari su yi amfani da bankuna da manhajajun da aka amince da su kawai wajen sayen hannayen jarin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Hukumar Kula da Harkokin Kasuwannin Hannayen Jari (SEC) ta yi gargadi ga yan Najeriya da sauran masu shirin sayen hannun jari a matatar Dangote.
A wata sanarwa da ta fitar jiya Litinin, SEC ta gargadi masu zuba jari da su yi taka tsan-tsan domin gujewwa fadawa hannun manhajojin yan damfara wajen sayen hannun jarin matatar mai.

Kara karanta wannan
Matatar Dangote ta fito da tsari, duk wanda ya sayi hannun jari zai iya samun kyauta mai gwaɓi

Source: Facebook
Leadership ta ce matatar Dangote ta bude damar sayen hannayen jarin ne a ranar Litinin, 14 ga watan Satumba, ,2026, inda kamfanin ya shirya cefanar da hannayen jari biliyan 4.1 kan N525 kowane guda daya.
Dalilin sayar da hannun jarin Dangote
Ana sa ran za a yi hada-hadar hannun jarin matatar Dangote har zuwa ranar 13 ga Oktoba, 2026, bisa sharuddan da aka bayyana a cikin takardar bayanan tayin (Prospectus).
Wannan ya bai wa jama’a dama a karon farko su mallaki kaso a matatar Dangote, wadda ita ce mafi girma a Afirka, kuma daya daga cikin manyan ayyukan masana’antu a duniya.
Ana sa ran tayin hannayen jarin zai tara kusan Naira tiriliyan 2.15, wanda zai sanya shi cikin manyan tayin hannayen jari da aka taba gudanarwa a Afirka.
Za a yi amfani da kudaden da aka samu wajen tallafa wa tsare-tsaren bunkasa matatar na dogon lokaci, fadada ayyukanta, zuba jari a dabarun kasuwanci da kuma samar da karin riba ga masu hannayen jari da sauran masu ruwa da tsaki.
SEC ta gargadi masu zuba jari
Bayan wannan ci gaba, hukumar SEC ta gargadi masu zuba jari da su yi watsi da dandamalin da ba a amince da su ba wadanda ke neman karbar kudinsu ta hanyar damfara.
Ta shawarci masu zuba jari da suka cancanta su sayi hannayen jarin ta hanyoyi da manhajojin da aka amince da su, ciki har da NGX Invest, bankunan kasuwanci da aka ware da kuma dandamalin zuba jari da aka ba da izini.
Masu zuba jari na nuna sha’awa
Gargadin SEC ya zo ne yayin da mutane da dama suka nuna sha’awar zuba jari a matatar Dangote da ke jihar Legas.
An tsara wannan tsari ne domin fadada damar shiga kasuwar hada-hadar hannayen jari da kuma bai wa karin mutane damar mallakar hannayen jarin matatar.

Source: Facebook
SEC ta bukaci jama’a masu zuba jari da su kasance cikin taka-tsantsan tare da amfani da bankuna da sauran manhajojin da aka amince da su kawai wajen shiga tayin hannayen jarin.
Matatar Dangote za ta raba kyauta
Kun ji cewa matatar Dangote ta bullo da hanyar da duk wanda ya sayi hannun jarinta guda 10 zai iya samun karin guda daya kyauta
Ta bayyana cewa za ga ba masu zuba jari da suka cancanta ƙarinNguda ɗaya na kan kowane hannun jari 10 da suka riƙe na tsawon watanni 12
Asali: Legit.ng

