Juyin Mulki: Ma'aikacin Aso Villa Ya Tona Yadda aka Shirya Kutsa wa Fadar Shugaban Kasa

Juyin Mulki: Ma'aikacin Aso Villa Ya Tona Yadda aka Shirya Kutsa wa Fadar Shugaban Kasa

  • Wani ma’aikacin fadar shugaban ƙasa ya bayyana rawar da ya fara taka wa a shirin juyin mulki da aka so kitsa wa domin hambarar da gwamnatin Bola Tinubu
  • Wanda ake zargi Zekeri Umoru ya tabbatar wa da kotu cewa shi ne wanda aka nema da ya tara sojoji da jami’an DSS domin shirin juyin mulkin har cikin Aso Villa
  • Ya yi bayani dalla-dalla a kan shirin da aka fara yi wajen kashe wutar lantarkin Aso Rock Villa domin sauƙaƙa aiwatar da shirin bayan ya shiga da sojojin a boye

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Wani mutum mai suna Zekeri Umoru, da ake zargi da hannu a yunkurin juyin mulki, ya shaida wa kotu cewa an tattauna yadda za a kashe wutar lantarki a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja domin taimaka wa shirin.

Kara karanta wannan

1975: Yakubu Gowon ya fadi sunayen wadanda suke da hannu a yi masa juyin mulki

Umoru, wanda ma’aikaci ne a sashen kula da gyare-gyare na kamfanin Julius Berger Nigeria a cikin Aso Villa, ya bayyana hakan ne a cikin wani bidiyo da aka kunna a gaban Mai Shari’a Joyce Abdulmalik ta Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.

An so shiga har Aso Villa don hambarar da Tinubu
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu a wani taro Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Getty Images

A rahoton da jaridar Daily Trust ta fitar, Zekeri Umoru ya ce sai da ya gargadi masu shirya lamarin cewa kashe wutar lantarki a Aso Villa zai jawo bincike kai-tsaye tare da kama ma’aikatan da ke bakin aiki a lokacin.

Juyin mulki: Yadda aka shirya shiga Aso Villa

Daily Post ta wallafa cewa Umoru ya ce Kanal Mohammed Ma’aji, wanda ake zargi da jagorantar shirin juyin mulkin, ya ba shi kuɗi ta hannun sufeto Ahmed Ibrahim domin ya nemo mutane daga cikin ma’aikatan.

Ya ce mutanen da ake son ya tattara sun haɗa da sojoji, jami’an hukumar tsaron farin kaya, SSS da kuma ma’aikatan Julius Berger.

A cewarsa, Ma’aji ya bayyana masa cewa yana son samun hanyar shiga Aso Villa, kuma zai iya yin hakan ta amfani da ƙarfi ko da waɗanda za a nema daga ciki sun ƙi ba da haɗin kai.

Umoru ya ƙara da cewa daga baya sufeto Ahmed Ibrahim ya nemi Naira miliyan 100 daga Ma’aji domin samar da hanyar shiga Aso Rock Villa ta hanyar motar asibiti, amma Ma’aji ya ƙi saboda ya ce kuɗin sun yi yawa.

Kara karanta wannan

Tana ƙasar waje: Lauyan Sadiya Farouk ya fadi abin da ya hana ta zuwa kotu

An tsorata ma'aikacin Aso Villa kan shirin juyin mulki

Wanda ake zargin ya ce duk da haka Ma’aji ya nace cewa zai iya shiga fadarr da ƙarfi, duk kuwa da cewa “za a zubar da jini.”

Umoru ya bayyana cewa daga baya ya fara jin tsoron shirin, har ya yi ƙoƙarin mayar da kuɗin da aka ba shi saboda ya fahimci cewa shiga Aso Villa ba wasan yara ba ne.

An so a kashe wutar lantarkin Villa gabanin juyin mulki
Kayan samar da wutar lantarkin kamfanin TCN Hoto: Transmission Company of Nigeria
Source: Twitter

Ya musanta zargin cewa yana da wata hanya ta shiga cibiyar samar da hasken rana ta Villa domin lalata wutar lantarki.

Game da dalilin da ya sa bai kai rahoton tattaunawar ga hukumomi ba, Umoru ya ce Ahmed Ibrahim ne ya hana shi bayan ya umarce shi da ya goge saƙonni tare da gujewa tuntuɓar Ma’aji saboda ana gudanar da bincike a ofishinsu.

Mai Shari’a Abdulmalik ta ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 21 ga watan Mayu domin ci gaba da shari’ar tantance ko an samu bayanan waɗanda ake tuhuma ta sahihiar hanya.

Kara karanta wannan

Abin da Trump ya ce game da shirin kai wa Iran sabon hari

Gwamnatin Tarayya ta hannun ofishin Antoni Janar na Tarayya ta gurfanar da mutum shida kan tuhume-tuhume 13 da suka haɗa da cin amanar ƙasa, ta’addanci da kuma zargin safarar kuɗi ko tallafa wa ta’addanci.

Daga cikin waɗanda ake tuhuma akwai tsohon Manamin Janar Mohammed Ibrahim Gana, Erasmus Ochegobia Victor, Ahmed Ibrahim, Zekeri Umoru, Bukr Kashim Goni da Abdulkadir Sani.

Yadda aka ba malami kudi don juyin mulki

A baya, kun samu labarin cewa an gurfanar da daya daga cikin malaman Musulunci, Sheikh Bukar Kashim Goni da ake zargi da hannu a yunkurin yi wa Bola Ahmed Tinubu juyin mulki.

A zaman kotun da aka yi, Sheikh Bukar Goni ya tabbatar da cewa daya daga cikin wanda ake zargi da yunkuirin kifar da gwamnati ya tura masa kudi yayin da ake ci gaba da kitsa shirin.

Sai dai malamin ya yi karin haske game da tura masa kudin, inda ya ki yarda da cewa yana da hannu a cikin yunkurin kifar da shugaba Bola Tinubu tare da fitar da bayanan da suka zo gabansa kan batun.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng