'Yan Sanda Sun Saki Sunayen Mutane 2 da Ke ba 'Yan Bindiga Bayanai a Bauchi

'Yan Sanda Sun Saki Sunayen Mutane 2 da Ke ba 'Yan Bindiga Bayanai a Bauchi

  • Rundunar 'yan sandan Bauchi ta kama wasu matasa biyu da ake zargi da ba 'yan bindiga bayanan sirri domin satar mutane a Alkaleri
  • Ana zargin matasan sun taimaka wajen harin da aka kai wani mutum mai shekara 46, wanda ya samu raunin harbin bindiga yayin ƙoƙarin tserewa
  • Kwamishinan 'yan sanda ya tabbatar da an miƙa shari'ar zuwa sashen binciken manyan laifuka tare da kira ga jama'a su ci gaba da ba da sahihan bayanai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida

Bauchi - Rundunar 'yan sandan jihar Bauchi ta sanar da kama wasu matasa biyu da ake zargi da yi wa masu garkuwa da mutane aikin leƙen asiri a ƙaramar hukumar Alkaleri.

Rundunar ta ce kamen na daga cikin matakan da take ɗauka domin yaƙi da satar mutane da sauran manyan laifuka a faɗin jihar.

Kara karanta wannan

Sojoji sun gano inda aka boye gawar shugaban al'umma da aka hallaka a Imo

'Yan sanda sun kama masu ba 'yan bindiga bayanai a Bauchi
An gabatar da mutane 2 da aka kama a Bauchi bisa zargin ba 'yan bindiga bayanai. Hoto: Bauchi State Police Command
Source: Facebook

Yadda aka kai hari a jihar Bauchi

Kakakin rundunar, SP Nafiu Habib, ya ce wasu 'yan bindiga da ba a tantance ba sun kai hari gidan wani mutum mai shekara 46 a ƙauyen Gwanar Dutse da ke gundumar Gwana da misalin ƙarfe 5:00 na safiyar ranar 31 ga Yulin 2026, in ji rahoton Tribune.

A cewarsa, maharan sun yi ƙoƙarin yin garkuwa da mutumin, amma ya samu raunin harbin bindiga a cinyarsa ta dama yayin da yake ƙoƙarin tserewa.

An garzaya da shi Babban Asibitin Kashere, inda ake kula da lafiyarsa, kuma rahotanni sun nuna yana samun sauƙi.

'Yan sanda sun kama waɗanda ake zargi

SP Habib ya ce jami'an 'yan sanda da ke Gobirawo, ƙarƙashin jagorancin jami'in da ke kula da ofishin, sun kama mutum biyu da ake zargi da hannu a harin da misalin ƙarfe 3:28 na ranar 2 ga Agustan 2026.

Waɗanda aka kama sun haɗa da Idi Riga mai shekara 18 daga ƙauyen Gwanar Dutse da kuma Murtala Sani mai shekara 22 daga Rifta Unguwan Jauro Musa da ke unguwar Gobirawo.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Mutanen gari sun sassara wata mata da adda har ta mutu a Bauchi

Binciken farko ya nuna cewa waɗanda ake zargin sun amsa cewa suna ba maharan bayanan sirri da ke taimaka musu wajen gudanar da hare-hare.

An miƙa bincike zuwa SCID

Rundunar ta ce ana tsare da waɗanda ake zargin, yayin da aka miƙa lamarin zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuffuka na Jihar Bauchi (SCID) domin zurfafa bincike da kuma gurfanar da su a kotu idan bincike ya kammala.

Rundunar 'yan sanda ta kama mutum 2 bisa zargin ba 'yan bindiga bayanai a Bauchi
Taswirar jihar Bauchi, inda aka kama mutum 2 bisa zargin ba 'yan bindiga bayanai. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Kwamishinan 'yan sandan jihar, CP Sani-Omolori Aliyu, ya sake tabbatar wa al'ummar Bauchi cewa rundunar ta himmatu wajen kawar da masu aikata laifuka daga jihar.

Ya kuma buƙaci jama'a su kasance masu lura tare da ci gaba da bai wa jami'an tsaro sahihan bayanai a kan lokaci domin taimakawa wajen yaƙi da miyagun laifuka.

An kashe wata mata a Bauchi

A wani labari, mun ruwaito cewa, wasu da ake zargi sun kashe wata mata a Bauchi bayan sun zarge ta da maita, tare da raunata mijinta da wasu yara biyu.

Rundunar 'yan sanda ta kama mutum guda, yayin da take ci gaba da farautar wasu mutum biyu da ake zargi da hannu a kashe matar mai suna Hafse Ubale mai shekara 30.

Kwamishinan 'yan sandan Bauchi ya yi Allah wadai da kisan, yana mai gargadin jama'a su guji ɗaukar doka a hannunsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com