Babban Malami a Najeriya Ya Zargi Wasu Mutane da Daukar Nauyin 'Yan Bindiga, Ya Fadi Dalili

Babban Malami a Najeriya Ya Zargi Wasu Mutane da Daukar Nauyin 'Yan Bindiga, Ya Fadi Dalili

  • Babban limamin coci a Najeriya, Archbishop Leonard Bature Kawas ya hango dalilin wasu mutane na daukar nauyin ’yan bindiga
  • Limamin cocin ya zargi wasu madu daukar nauyin ayyukan ta'addanci da kokarin bata wa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu suna
  • Kawas ya ce babu wanda ya bai wa malaman addinin kirista kudi domin su goyi bayan Tinubu ya zarce zuwa wa'adi na biyu a 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Shugaban Majalisar Manyan Bishof-bishof ta Najeriya, Archbishop Leonard Bature Kawas, ya zargi wasu masu hannu a daukar nauyin ta'addanci.

Fitaccen limamin cocin ya zargi wasu mutane da daukar nauyin ’yan bindiga, masu garkuwa da mutane da ayyukan ta’addanci domin bata sunan gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Shugaba tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu yana magana a wsta liyafa da aka shirya a Aso Rock Hoto: @OfficialABAT
Source: Facebook

Kawas ya yi wannan zargin ne yayin da yake kare matakin da malaman coci-coci suka dauka na goyon bayan Tinubu, a wata hira da shirin Morning Brief na Channels TV ranar Talata.

Kara karanta wannan

Duk da sace malamai maza, malaman addini mata sun goyi bayan Tinubu

Malamin coci ya zargi wasu mutane

Malamin ya ce goyon bayan da suka bai wa shugaban kasar ba shi da wata alaka da kudi, yana mai jaddada cewa babu wani kudi da aka bai wa bishof-bishof din da ya ke jagoranta domin su goyi bayan Tinubu.

“Tinubu bai ba mu ko Naira daya ba da sunan mu goyi bayansa. Babu ko Naira daya da aka ba mu. Mun yi hakan ne bisa la’akari da abubuwan da ke faruwa a kasarmu.
"Wasu mutane na zagon kasa ta hanyar daukar nauyin ’yan bindiga, garkuwa da mutane da sauran wadannan abubuwa domin bata wa Tinubu suna,” in ji shi.

Ya kwatanta lamarin da Jonathan

Kawas ya kwatanta halin da ake ciki da abin da ya ce ya faru a lokacin gwamnatin tsohon Shugaba Goodluck Jonathan, yana mai cewa an yi irin wannan kokari wajen nuna Jonathan cikin mummunan hali.

Ya ce limamam coci-coci din sun gamsu cewa wasu mutane na amfani da matsalar rashin tsaron da kasar ke fuskanta wajen kawo cikas da kuma bata sunan gwamnatin Tinubu.

Kara karanta wannan

Malam Murtala Bello ya faɗi shirinsu da aka kai wa Sheikh Lukuwa hari a Sokoto

Malamin ya ce saboda haka ne suka yanke shawarar cewa Tinubu ne dan takarar da ya kamata su goyi baya.

Kawas.
Babban limamim coci a Najeriya, Leonard Bature Kawas da Shugaba Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Da yake amsa tambayar ko ya kamata kudi su yi tasiri kan goyon bayan siyasa, Kawas ya ce rashin samun wata fa’ida ta kudi ba zai hana limamam coci goyon bayan dan takarar da suka yi imanin ya dace ba.

“Idan muka shiga siyasa, kuma wata albarka ta samu daga ciki, to madalla. Amma idan albarkar ba ta zo ta bangaren kudi ba, hakan ma ba matsala ba ne muddin mun gamsu cewa wannan shi ne dan takarar da ya dace,” in ji shi.

An yi hasashen nasarar Tinubu a 2027

Kun ji cewa Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar Edo, Kassim Afegbua, ya yi hasashen cewa Shugaba Bola Tinubu zai lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Rahotanni sun nuna cewa Afegbua ya ce Atiku Abubakar zai zo na biyu, yayin da Peter Obi zai zo na uku a fafatawar da za a yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262