An Rincabe da Fada a Hormuz, Iran Ta Harbo Jirgin Yakin Amurka
- Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci na Iran (IRGC) sun ce sun kakkabo wata jirgi mara matuki kirar MQ-1 a sararin samaniyar yammacin mashigar Hormuz
- Rundunar IRGC ta ce sabon tsarin kariyar sararin samaniyarta ne ya gano tare da lalata jirgin a safiyar Litinin, yayin da yake shawagi a yankin
- Lamarin ya faru ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun takaddama kan tsaron mashigar Hormuz, wadda ke da matukar muhimmanci wajen safarar man fetur
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci na Iran (IRGC) sun yi ikirarin kakkabo wata babbar jirgi mara matuki kirar MQ-1 a sararin samaniyar yammacin mashigar Hormuz.
IRGC ta ce jirgin an gano shi ne da safiyar Litinin ta hanyar tsarin hadadden kariyar sararin samaniyar Iran, kafin a lalata shi.

Source: Getty Images
IRGC ta lalata jirgin Amurka
Roya News ta wallafa cewa sashen hulda da jama'a na IRGC ne ya fitar da sanarwar da kafafen yada labaran gwamnatin Iran suka wallafa.
Sanarwar ta ce an kakkabo jirgin ne a safiyar Litinin ta amfani da wani sabon tsarin kariyar sararin samaniya na rundunar IRGC.
IRGC ta bayyana cewa tsarin ya yi aiki ne karkashin jagorancin hadadden tsarin kare sararin samaniyar kasar.
A cikin sanarwar, IRGC ba ta bayyana kasar da jirgin ya fito daga gare ta ko kuma wanda ke sarrafa shi ba.
Haka kuma, ba a bayyana karin bayanai kan takamaiman tsarin makamin kariyar sararin samaniyar da aka yi amfani da shi wajen kakkabo jirgin ba.
Lamarin ya faru ne yayin da ake ci gaba da samun ayyukan leken asiri daga sama da kuma rikice-rikicen da suka shafi jirage marasa matuka a wannan muhimmiyar hanyar ruwa.

Source: Facebook
Iran na shirin babban atisaye
Kamfanin dillancin labarai na CNB ya wallafa wani sako mai cike da sirri, inda ya sanar da wani abin da ya kira "babban atisaye" da ake shirin gudanarwa.
An wallafa sakon ne tare da wani bidiyo na dakika 48 da aka samar ta hanyar fasahar AI, wanda ya nuna dubban mutane suna taruwa a birnin Tehran.
Bidiyon ya nuna mutane, ciki har da likitoci, injiniyoyi, dalibai, sojoji da iyalai, suna tafiya a titunan birnin kafin su taru a dandalin Azadi.
Sakon ya danganta atisayen da mutane 313,000 da aka bayyana a matsayin masu kishin kare Iran, tare da alakanta shi da kokarin hada magoya bayan Basij, wata kungiyar sa-kai ta rundunar sojin Iran.
Houthi sun hari Saudi
A wani labarin, kunji cewa mayakan Houthi sun kammala kwace dukkan gabar tekun Yemen da ke kan Bahar Maliya, bayan sun kwace birnin tashar jiragen ruwa na Mocha tare da mamaye tsibirin Mayyun.
Mayakan na Houthi yanzu suna kusan kilomita 20 daga gabar Afirka, lamarin da ya ba su damar mamaye yankin mashigar Bab al-Mandab, wadda ke da matukar muhimmanci ga zirga-zirgar jiragen ruwa a Bahar Maliya.
Kungiyar IOM ta ce sama da mutane 2,000 sun tsere daga Yemen zuwa Djibouti cikin sa'o'i 24, inda wadanda suka isa birnin Obock ke samun abinci da ruwa, duk da cewa ana bukatar karin tallafi.
Asali: Legit.ng

