Abin da Ake Tsoro Ya Zama Gaskiya, 'Yan Sanda Sun Tabbatar da Sace ‘Yan NYSC
- ‘Yan bindiga sun tare wasu motoci a kan hanyar Owerri zuwa Onitsha da sanyin safiyar Alhamis
- An sace wasu su ne yayin da suke tafiya a cikin motar bas daga Ibadan zuwa sansanin hukumar NYSC
- Jami'an tsaro sun tura runduna kuma tun an yi nasarar ceto wasu wadanda abin ya shafa a nan take
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Imo - Rundunar ‘yan sandan Najeriya na reshen jihar Imo sun tabbatar da cewa an sace wasu masu bautar kasa (NYSC).
Jami’an tsaron sun shaida cewa ‘yan NYSC suna cikin mutanen da aka dauke su a kan titin Owerri zuwa Onitsha ranar Alhamis.

Source: Getty Images
'Yan bindiga sun tare motoci a jihar Imo
The Cable ta rahoto Kakakin ‘yan sandan Imo, Okoye Henry yana mai bayyana haka a wani jawabi na musamman da ya fitar.
Sai dai abin farin cikin shi ne, Okoye Henry ya shaida cewa an yi nasarar ceto mutane 10 daga cikin wadanda aka yi gaba da su.
Zuwa lokacin da ya fitar da jawabi, ya ce ana bincike ne domin ba a iya tantance adadin mutanen da aka sace a babbar hanyar ba.
An ga bidiyon dauke fasinjoji a Owerri
A safiyar Alhamis aka ji labari ‘yan bindiga sun tare wata mota mai cin fasinjoji 18, suka wuce da mutanen ciki zuwa jeji.
Wani bidiyo da ya karade dandalin X da ya fi shahara da Twitter, ya ce matafiyan suna hanyar zuwa Abia da Akwa Ibom ne.
Wasu matafiyan da aka tare suna tafiya ne cikin mota mai tambarin gwamnatin jihar Abia.
Okoye Henry ya ce da kimanin karfe 6:30 abin da ya rutsa da motar, kuma babu shakka a ciki akwai masu yi wa kasa hidima.
Ban da ‘yan NYSC din akwai wasu fasinjoji da suke kan hanyar Uyo daga Ibadan, wasu kuma za su je garin Bende a jihar Abia.
'Yan sanda sun ce an ceto fasinjoji 10
Rahoton Channels ya ce da samun labarin abin da ya faru, ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro suka dauki matakin gaggawa.
Jawabin ya ce sanadiyyar wannan yunkuri ne aka ceto mutane 10 da kuma wadannan manyan motoci biyu kafin a je ko ina.
"Wadanda aka ceto sun kubuta kuma suna cikin aminci ana kula da su.
"Ba a iya tantance adadin mutanen da aka yi gaba da su ba, amma za a sanar da jama’a da zarar an tabbatar."
- Okoye Henry
Kakakin ‘yan sandan ya ce Kwamishina na Imo da sauran manyan jami’an tsaro sun je wurin domin gane wa kansu abin da ya faru.

Source: Getty Images
Direbobin Keke napep suna wayyo Allah
Ana da labari wasu direbobin Keke Nape da suka zabi Bola Tinubu suna cizon yatsa a yanzu, kuma sun kagara zaben 2027 ya zo.
Abin da ya fi damun su shi ne yadda fetur ya tashi daga N200 zuwa kusan N1500 a cikin shekaru uku da gwamnati mai ci ta yi.
Wannan ya sa suka ce da su za a yi aikin TinubuMustGo a jihar Kano a zaben 2027 kuma za su fadakar da fasinjoji su guji APC.
Asali: Legit.ng

