Da Gaske Tinubu Ya Roƙi Trump Ya Rufa Masa Asiri kan Zargin Safarar Ƙwaya?

Da Gaske Tinubu Ya Roƙi Trump Ya Rufa Masa Asiri kan Zargin Safarar Ƙwaya?

  • An yi ta yada wasu wasiku da aka ce Bola Tinubu yana rokon Shugaba Donald Trump kan zargin safarar kwayoyi
  • Bincike ya gano cewa wasiƙun suna ɗauke da tambura da sa hannu da ba su dace da takardun Fadar Shugaban Ƙasa ba
  • Haka kuma, gwaje-gwajen fasahar tantance hotuna sun nuna alamun AI, yayin da mai taimakawa Tinubu kan yaɗa bayanai ya ce wasiƙun na bogi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Yayin da ake ci gaba da dakon bayanai kan zargin Bola Tinubu a Amurka game safarar kwayoyi an fara yada wasu wasiku.

Wasu masu amfani da kafafen sada zumunta sun fara yaɗa wasiƙun da ake zargin Tinubu ya aika wa Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya, Antonio Guterres, da Shugaban Amurka, Donald Trump.

Kara karanta wannan

Nigeria @66: Cikakken jawabin da Tinubu ya yi wa 'yan Najeriya a ranar samun 'yancin kai

An yaɗa cewa Tinubu ya roki Trump kan tona masa asiri
Shugaba Donald Trump na Amurka da Bola Tinubu. Hoto: @aonanuga1956, @RealDonaldTrump.
Source: Twitter

Jita-jitar da ake yada wa kan Tinubu

Ɗaya daga cikin wasiƙun da aka wallafa a Facebook, wadda aka ce an aika wa Guterres, ta ƙunshi roƙon a yi amfani da ofishinsa wajen tattaunawa da gwamnatin Amurka, musamman Trump, domin a soke ko rufe shari’ar.

An yi zargin cewa Tinubu ya roƙi shugabannin biyu su sa a dakatar da fitar da wasu fayilolin da suka shafi tsoffin binciken laifukan miyagun ƙwayoyi da kuma mutuwar Moshood Abiola da Sani Abacha.

Wata wasiƙa makamanciya ta bayyana inda aka rubuta tare da roƙon hukumomin Amurka su yi taka-tsantsan wajen fitar da bayanan.

Wasu masu amfani da kafafen sada zumunta sun yi martani daban-daban kan wasiƙun, inda wasu suka ɗauke su a matsayin hujjar cewa Tinubu ya amince da cewa yana da shari’ar miyagun ƙwayoyi a Chicago.

An ƙaryata cewa Tinubu ya roki Trump kan rufa masa asiri
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya ya yi tagumi a taro. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Abin da bincike ya gano kan yada jita-jitar

Sai dai shafin Dubawa ta gudanar da bincike kan ikirarin, saboda batun ya shafi diflomasiyya, shari’ar da ke gudana a Amurka da kuma manyan jami’an gwamnati.

Kara karanta wannan

Kasa za ta yi saiti, Tinubu ya juyo kan abin da ya fi damun yan Najeriya

An gudanar da binciken kalmomi ta Google, shafin X na Fadar Shugaban Ƙasa da kuma kundin labaran manyan kafafen yaɗa labarai na Najeriya.

Binciken bai gano wata kafar yaɗa labarai da ta bayar da rahoton cewa Tinubu ya aika irin waɗannan wasiƙu ga Majalisar Ɗinkin Duniya ko gwamnatin Amurka ba.

An kuma duba wasiƙun da hannu, inda ta gano bambance-bambance a ƙira da tsarin rubutu, tare da tambarin da bai yi daidai da takardun hukuma na Fadar Shugaban Ƙasa ba.

Wasiƙun sun ƙunshi wani tambari da hoton Tinubu, tambarin Najeriya da manyan rubuce-rubuce, yayin da wannan ya bambanta da tsarin wasiƙun hukuma da Fadar Shugaban Ƙasa ke amfani da su.

Bugu da ƙari, sa hannun da aka sanya a wasiƙun bai yi daidai da sa hannun Tinubu da ake gani a saƙonnin shugaban ƙasa na hukuma ba.

Haka kuma, lauyoyin Tinubu sun gabatar da hujjojin shari’a a gaban kotu kan wasu tanade-tanaden doka da ke hana fitar da bayanai, maimakon amfani da wasiƙun sirri zuwa ƙasashen waje.

An yi amfani da kayan aikin InVID-WeVerify wajen binciken sahihancin wasiƙun, inda aka gano alamun cewa wasiƙar da aka aika wa Guterres ta kasance abin da aka samar da fasahar AI.

Kara karanta wannan

‘Yan Sanda sun fadi hakikanin dalilin kama masu sanye da rigar #TinubuMustGo

Sakamakon binciken ya nuna cewa kashi 88 cikin 100 na wasiƙar da aka aika wa Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya na iya kasancewa an samar da ita ta hanyar AI.

A ƙarshe, an gano cewa ikirarin da ke cewa Bola Ahmed Tinubu ya rubuta wasiƙu ga Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya da Donald Trump yana roƙon kada a saki bayanan nasa ba gaskiya ba ne.

Bukatar Bola Tinubu ga kotun Amurka

Mun ba ku rahoton cewa Shugaba Bola Tinubu ya roki alfarma a bukatar Ma’aikatar Shari’a ta Amurka na neman karin kwanaki 10 kan zargin safarar kwayoyi.

Alkalin kotun Amurka Beryl Howell ya amince da karin kwanaki hudu kacal, inda ta tsawaita wa’adin zuwa 21 ga Agusta.

Lamarin ya samo asali ne daga bukatar Aaron Greenspan ta FOIA, yayin da kotun ta umarci FBI da DEA su fitar da bayanan bincikensa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.