An Kama Shugaban Kungiyar Magoya bayan Peter Obi da Kwankwaso
- ’Yan sanda sun kama Elijah Noah, kodinetan OK Movement na Akwa Ibom, yayin wani tattakin Ranar ’Yancin Kai a Uyo
- ’Yan sanda sun ce sun kama mutane takwas bisa zargin aikata abubuwan da ka iya kawo cikas ga zaman lafiyar jama’a
- Rundunar ta musanta cewa an yi harbe-harbe, tana mai cewa jami’an da aka tura sun nuna kwarewa da kamewa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Akwa Ibom, Nigeria - Rundunar ’yan sandan Jihar Akwa Ibom ta kama kodinetan OK Movement na jihar, Elijah Noah, yayin wani gangamin Ranar ’Yancin Kai a Uyo.
An tattaro cewa jami’an ’yan sanda dauke da makamai da dama ne suka kama Noah, yayin da aka harba hayaki mai sa hawaye a lokacin da magoya baya suka taru domin gangamin.

Source: Twitter
Daily Trust ta ce wasu bidiyoyi da ke yawo a kafafen sada zumunta sun nuna jami’an ’yan sanda sun kewaye Noah tare da jan shi zuwa wata motar ’yan sanda kafin su tilasta masa shiga cikinta.
Dalilin kama kodinetan OK Movement
Lamarin ya faru ne a daidai lokacin da harkokin siyasa suka kara zafi tsakanin magoya bayan NDC gabanin babban zaben 2027.
Wata mai amfani da kafar X mai suna Esther Umoh ta yi ikirarin cewa laifin da Noah ya aikata kawai shi ne zuwa wurin da aka shirya fara wannan gangami.
Umoh ta ce:
“Laifinsa kawai shi ne ya zo ya duba wurin da za a fara muzaharar,” yayin da ta zargi Gwamnatin Jihar Akwa Ibom da zama mai tafiya ba bisa tsarin dimokuradiyya ba.
Yan sanda sun kama mutum 8
Sai dai Rundunar ’yan sandan Jihar Akwa Ibom ta bayyana cewa an kama mutane takwas bisa aikata abubuwan da ka iya kawo cikas ga zaman lafiyar jama’a da kuma zargin kin bin umarnin jami’an tsaro.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar, DSP Timfon John, ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis a Uyo
Ya ce wadanda ake zargin suna taimaka wa ’yan sanda wajen binciken da ake gudanarwa, kuma za a gurfanar da duk wanda aka samu da laifi bisa tanadin doka.

Source: Twitter
Yan sanda sun musanta harbe-harbe
John ya bayyana cewa ba a yi harbe-harbe ba yayin lamarin, yana mai jaddada cewa jami’an da aka tura sun gudanar da aikinsu cikin kwarewa da kamewa, kuma babu bindigar da aka harba.
Kakakin yan sandan ya ce:
“Don kauce wa shakku, Jihar Akwa Ibom tana cikin kwanciyar hankali. Ba a samu rahoton harbe-harbe ba, ba a samu rahoton raunin harsashi ba, kuma an kama mutane takwas dangane da rikicin.”
“Rundunar ’yan sandan Jihar Akwa Ibom na ci gaba da jajircewa wajen kare rayuka da dukiyoyi, kuma za ta ci gaba da daukar duk matakan da doka ta amince da su domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a fadin jihar.”
Yan sanda sun kama kakakin PDP
Kun ji cewa jami’an ‘yan sandan Najeriya sun kama wani kakakin jam'iyyar PDP a jihar Akwa Ibom, Ewa Okpo bayan an shigar da korfinsa.
‘Yan sandan Najeriya sun cafke Ewa Okpo ne saboda zargin bata suna da wasu laifuffukan da suke da alaka da amfani da dandalin sada zumunta.
Wani tsohon sanata a Akwa Ibom, Effiong Bob ya zargi kakakin PDP da bata masa suna da kalamai da ya yi a Facebook.
Asali: Legit.ng

