Ndume Ya Musanta Zargin Shiga tsakani da 'Yan Bindiga, Ya Nemi a Binciki Kaigama
- Sanata Ali Ndume ya fusata bayan an danganta shi da shiga tsakani tare da karban kudin fansa domin bai wa yan ta'addan da su ka yi garkuwa da mutane
- Ya bayyana cewa abin da ya yi shi ne sanar da DSS, NSA da sauran hukumomin tsaro bayan samun rahoton sace mutanen Ngoshe
- Sanata Ali Ndume ya bukaci jami'an tsaro su gudanar da cikakken bincike kan zarge-zargen da aka yi masa, domin a wanke sunansa daga zargin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Sanatan da ke wakiltar Borno ta Kudu a Majalisar Dattawa, Ali Ndume, ya yi fatali da zargin da Samaila Ibrahim Kaigama ya yi masa na cewa ya kasance mai shiga tsakani tsakanin masu garkuwa da mutane da gwamnati.

Kara karanta wannan
Fadar shugaban ƙasa: 'Tinubu ya fitar da mara 'da kunya, ya kamata a saka masa a 2027'
Ya bayyana cewa babu wani lokaci da ya taba shiga takanin yan ta'adda da gwamanti ko wasu mutane wajen batun kudin fansa.

Source: Facebook
Ndume ya yi wannan bayani ne a wata hira da ya yi da Arise News, bayan Kaigama ya zarge shi a wata hira a rediyo da kuma wasu bayanai da kungiyar BOSYA ta fitar.
Ikirarin da aka yi kan Ndume
Jaridar News ta wallafa cewa Kaigama ya yi ikirarin cewa an biya N5bn domin kubutar da mata da yara 416 da aka sace daga Ngoshe a jihar Borno, tare da zargin cewa wani bangare na kudin ya salwanta.
Sai dai Ndume ya ce tun lokacin da Kaigama ya tuntube shi kan wani bidiyo da ake zargin Boko Haram da ISWAP sun fitar, ya tuntubi Mai Bai Wa Shugaban Kasa Shawara kan Tsaro (NSA), DSS da rundunar soji domin su dauki mataki.
Ya ce:
"Ban taba, kai tsaye ko a kaikaice na zama mai shiga tsakani tsakanin masu garkuwa da mutane da gwamnati ko wasu mutane. Ko kadan."
Sanatan ya ce yana da dukkannin sakonnin da suka shafi tattaunawarsa da Kaigama, kuma tuni ya mika batun ga hukumomin tsaro domin bincike.
Ndume ya fara 'tona asirin' Kaigama
Ndume ya bayyana cewa Kaigama ya nemi ya zama hanyar isar da kudin fansa, amma ya ki amincewa saboda matsayinsa na kin tattaunawa da 'yan ta'adda ko biyan su kudin fansa.
Ya ce:
"Na gaya masa cewa ba zan shiga wannan lamari ba. Mafi abin da zan iya yi shi ne hada shi da hukumomin da suka dace."

Source: Original
Sanatan ya kara da cewa Kaigama daga baya ya bukace shi ya bayar da gudunmawar kudi domin fansar wadanda aka sace, lamarin da ya sa ya fara zarginsa.
Dangane da ikirarin cewa an biya N5bn, Ndume ya ce ba shi da masaniya ko an biya kudin ko a'a, yana mai cewa gwamnati ko Kaigama ne ya kamata su yi bayani kan wannan batu.
Ndume ya aika sako ga gwamnati
A baya, kun samu labarin cewa Sanata Ali Ndume ya ce sabon harin da aka kai makarantar Borno ya nuna bukatar gwamnati ta kara daukar karin matakai kan rashin tsaro da ya hana jama'a zaman lafiya.
‘Yan bindiga sun sace dalibai da malamai a lokacin da ake zana jarrabawar NECO a Lassa, yayin da sojoji suka ceto wasu daga cikinsu, amma kuma an riga an yi nisa da wasu ba a gano su ba.
Sanata Ali Ndume da ke wakiltar Borno ta Kudu ya bukaci jami’an tsaro su kara kokari wajen kubutar da sauran wadanda aka sace tare da dakile hare-haren da ka iya zuwa nan gaba.
Asali: Legit.ng

