Juyin Mulki: Gwamnatin Tinubu Ta Kawo Shaidu 30 da Za Su ba da Shaida a Kotu

Juyin Mulki: Gwamnatin Tinubu Ta Kawo Shaidu 30 da Za Su ba da Shaida a Kotu

  • Kotun Tarayya da ke Abuja za ta saurari shari’ar wasu mutane shida da ake zargi da shirya juyin mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu
  • Gwamnatin tarayya ta gabatar da jerin shaidu 30 da suka hada da jami’an bincike, masana fasahar bincike, jami’an bankuna
  • Masu gabatar da kara sun ce za su gabatar da takardu, bayanan banki da na’urorin sadarwa domin tabbatar da zarge-zargen

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Gwamnatin tarayya ta shirya gabatar da shaidu 30 domin su bayar da shaida kan zargin juyin mulki.

Gwamnatin ta shirya gabatar da su ne a gaban kotu kan wasu mutane shida da ake zargi da kitsa yunkurin hambarar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Za a ci gaba da shari'ar wadanda ake zargin da yunkurin juyin mulki
Wanda ake zargi da kitsa juyin mulki, Kanal Ma'aji da Shugaba Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Wadanda ake zargi da yunkurin juyin mulki

Wadanda ake tuhuma sun hada da tsohon Manjo Janar na soja Mohammed Gana, tsohon Kyaftin na ruwa Erasmus Victor, sufeton ‘yan sanda Ahmed Ibrahim, Zekeri Umoru, Bukar Goni da Abdulkadir Sani, cewar Premium Times.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Gwamna ya rage albashin ma'aikata suna sa ran za a kara masu

A bara, an bayyana sunayen jami’an tsaro da fararen hula sama da 40 da ake zargi da hannu a cikin wannan makirci.

Tuhume-tuhumen da ake yi musu sun hada da cin amanar kasa, tallafa wa ayyukan ta’addanci, kin bayyana bayanan da suka sani da kuma wanke kudaden haram.

Takardun shaidun da aka gabatar a Kotun Tarayya da ke Abuja sun nuna cewa masu gabatar da kara za su dogara da shaidu daga jami’an bincike, jami’an bankuna, masana binciken fasahar zamani da kuma wasu fararen hula.

A cewar ofishin Antoni Janar na Tarayya, ana zargin wadanda ake tuhuma sun hada baki da Kanal Mohammed Ma’aji da wasu da ke gudun hijira domin tayar da rikici a Najeriya.

Gwamnatin Tinubu ta gabatar da shaidu 30 kan shari'ar juyin mulki
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Sunayen wadanda za su zama shaidu

Daga cikin shaidun akwai jami’an binciken da suka gudanar da binciken farko tare da tattara muhimman takardun da ake sa ran za a gabatar a kotu.

Haka kuma jami’ai daga bankuna 13 za su gabatar da bayanan bude asusu, bayanan ma’amaloli da sauran takardun kudi masu alaka da shari’ar.

Kara karanta wannan

Yadda aka nemi ceto malamar Islamiyya amma mutane suka taru suka kashe ta

Masana binciken fasahar zamani za su yi bayani kan yadda suka fitar da bayanai daga wayoyin hannu tare da nazarin abubuwan da suka samu, cewar The Guardian.

Wasu fararen hula irin su Aminu Abdullahi, Abdulganiyu Ahmed, Moses Opata da Peter Gambo za su bayar da shaida kan wasu mu’amaloli da ake zargin suna da alaka da lamarin.

Wakilan otal uku da suka hada da Brookville Hotel & Suites, Greenland Luxury Apartments da Hotel 17 Kaduna za su yi bayani kan tarurrukan da ake zargin an gudanar.

Haka kuma wasu manyan jami’an soji za su bayar da shaida kan batutuwan da suka shafi makamai, harsasai da kuma motocin soja da ake dangantawa da binciken.

Juyin mulki: Ma'aikacin Villa ya yi tone-tone

A wani labari, an ji cewa wani ma’aikacin fadar shugaban ƙasa ya bayyana rawar da ya fara taka wa a shirin juyin mulki da aka so kitsa wa domin hambarar da gwamnatin Bola Tinubu.

Wanda ake zargi Zekeri Umoru ya tabbatar wa da kotu cewa shi ne wanda aka nema da ya tara sojoji da jami’an DSS domin shirin juyin mulkin har cikin Aso Villa.

Ya yi bayani dalla-dalla a kan shirin da aka fara yi wajen kashe wutar lantarkin Aso Rock Villa domin sauƙaƙa aiwatar da shirin bayan ya shiga da sojojin a boye.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.