Dan Takarar Shugaban Ƙasa Ya Faɗi dalilin da Ya Sa Tinubu ke Son Komawa Ƙarfi da Yaji
- Dan takarar shugaban ƙasa a SDP, Adewole Adebayo ya zargi Bola Tinubu da neman sai koma mulki karfi da yaji
- Dan takarar ya yi hasashen karin tsadar man fetur da tabarbarewar tattalin arziki, tare da tsananin wahalar rayuwa
- Adebayo ya bukaci ’yan Najeriya su shirya daga matakin unguwa, su yi watsi da rarrabuwar kawuna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar SDP a zaben 2023, Adewole Adebayo, ya caccaki Bola Tinubu kan neman tazarce.
Adebayo ya zargi Shugaba Bola Tinubu da fifita zama a fadar shugaban kasa da tara dukiya kan magance matsalolin ’yan Najeriya.

Source: Twitter
Adebayo ya bayyana hakan ne a Ibadan yayin gabatar da kundin tsarinsa mai taken “Bankwana da Talauci da Rashin Tsaro”, inda ya bukaci ’yan Najeriya su shirya daga matakin kasa, cewar Vanguard.
Zargin da Adebayo ke yi wa Tinubu
Dan takarar SDP ya zargi Tinubu da rashin mayar da hankali kan ayyukan shugaban kasa, ciki har da kula da ministoci, tattaunawa da jama’a da samar da ilimi da kiwon lafiya.
Ya ce Tinubu ba ya son zama shugaban Najeriya, ba ya son yi wa jama’a hidima ko magana da su, sannan baya son kula da ayyukan ministocinsa.
A cewar Adebayo, shugaban yana nan ne kawai saboda yana son tara kudi, yana mai cewa bai nuna sha’awar gudanar da aikin shugaban kasa yadda ya kamata ba.
Adebayo ya kuma yi zargin cewa Tinubu ya fara harkokin siyasa ne da nufin tallafa wa wasu mutane su samu mukamai domin samun ribar kudi daga gare su.
Ya ce daga baya Tinubu ya yanke shawarar neman shugabancin Najeriya da kansa bayan ya fahimci cewa kudin da yake samu daga tallafa wa wasu ‘yan siyasa bai wadatar ba.

Kara karanta wannan
Tinubu na da cikakkiyar lafiyar da zai ci gaba da mulkin Najeriya? An samu bayani
Adebayo ya kuma yi zargin cewa shugaban ba ya damuwa sosai da samun ilimi, kiwon lafiya da sauran muhimman ayyuka ga ’yan Najeriya.
Ya bukaci jama’a su daina kallon mutane kawai, su kuma fahimci cewa suna da alhakin irin shugabannin da suke zaba a lokacin zabe, cewar Daily Post.
A cewarsa, idan ’yan Najeriya suka ci gaba da zabar shugabannin da ake zargi da cin hanci da rashawa, ya kamata su duba irin rawar da suke takawa.

Source: Twitter
Ya yi hasashen matsin tattalin arziki
Adebayo ya yi gargadin cewa karin shekaru karkashin gwamnatin Tinubu na iya kara tsananta matsin tattalin arziki, yana hasashen man fetur zai iya kaiwa N5,000 kan lita.
Ya ce tattalin arzikin Najeriya na iya durkushewa, lamarin da zai sa mutane su rike miliyoyin naira amma su kasa sayen muhimman kayayyaki saboda faduwar darajar kudinsu.
Adebayo ya ce hauhawar farashin kayayyaki na ci gaba da rage darajar kudaden da masu sana’o’i, ’yan kasuwa, makanikai da sauran ma’aikata ke samu.
Dan takarar SDP ya fadi shirinsa kan Tinubu
Mun ba ku labarin cewa dan takarar SDP, Adewole Adebayo, ya ce ya fahimci matsalolin da Najeriya ke ciki da kuma kura-kuran da yake ganin gwamnatin Tinubu ta yi.
Adebayo ya ce duk wanda ya karɓi mulki dole ya ɗauki alhakin nasarori da matsalolin da ya gada daga gwamnatin da ta gabata.
Dan takarar SDP ya ce gwamnatinsa za ta mayar da hankali kan ci gaba da ayyukan gwamnati maimakon ɓata lokaci wajen zargin wanda ya gabace shi.
Asali: Legit.ng

