Trump Ya Ji Zafin Kisan Sojojinsa da Iran Ta Yi, Zai Karbi Gawarwakinsu a wani Biki a Amurka

Trump Ya Ji Zafin Kisan Sojojinsa da Iran Ta Yi, Zai Karbi Gawarwakinsu a wani Biki a Amurka

  • Shugaba Donald Trump zai halarci karɓar gawarwakin sojojin Amurka huɗu da aka kashe a Gabas ta Tsakiya
  • Sojojin sun mutu a hare-haren makamai masu linzami da jiragen yaƙi marasa matuƙa na Iran a Jordan da kuma wani harin drone a Iraq
  • Tun bayan fara yaƙin Iran a watan Fabrairu, sojojin Amurka 18 sun mutu, yayin da Trump ya sha alwashin mayar da martani kan duk wani hari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington DC, US - Shugaban Amurka, Donald Trump zai halarci bikin karɓar gawarwakin sojojin Amurka huɗu da aka kashe a Gabas ta Tsakiya.

Za a gudanar da bikin a sansanin sojojin saman Dover Air Force Base domin mika gawarwakin ga iyalansu cikin girmamawa.

Trump zai karbi sojojin da Iran ta kashe masa
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump da sabon jagoran addini na kasar Iran, Mojtaba Khamenei Hoto: Andrew Caballero-Reynolds, Reza B.
Source: Getty Images

Fadar White House ta bayyana cewa wannan na daga cikin muhimman nauyin shugaban ƙasa a matsayin babban kwamandan rundunar soji, cewar Al Jazeera.

Kara karanta wannan

Mai shekara 60 ya rasu bayan zuwa otel da budurwa, an samu maganin jima'i

Trump zai karbi gawarwakim sojojin Amurka

Wannan ne karo na uku da Trump zai halarci irin wannan biki tun bayan fara yaƙin Iran a watan Fabrairun 2026.

Wani jami'in gwamnatin Amurka ya ce gawarwakin sojojin biyu da suka mutu sakamakon harin makamai masu linzami da jiragen yaƙi marasa matuƙa na Iran a Jordan za su isa sansanin domin bikin.

Jami'in ya kuma bayyana cewa za a dawo da gawar wani soja da ya ɓace bayan harin Jordan, wanda yanzu ake kyautata zaton ya rasu.

Haka kuma za a dawo da gawar wani soja da aka kashe a Iraq sakamakon fashewar wani jirgin yaƙi mara matuƙi na Iran.

Shugaba Donald Trump ya ce zuwa Dover domin karɓar gawarwakin babban abin girmamawa ne a gare shi.

Ya bayyana haka ne yayin ganawa da manema labarai a Fadar White House ranar Talata, cewar rahoton NBC Philadelphia.

Trump zai karbi gawargwakim sojojin Amurka da Iran ta hallaka
Jagoran addini a Iran, Mojtaba Khamenei da Shugaba Donald Trump na Amurka. Hoto: Imam Mojtaba Khamenei, Donald J Trump.
Source: Facebook

Sojojin Amurka da suka rasa rayukansu

Ma'aikatar Tsaro ta Amurka ta bayyana sunayen sojojin da suka mutu a Jordan da suka haɗa da Tyler James Feehan mai shekaru 25 daga Hawaii da Isabella Gonzales mai shekaru 19 daga Texas.

Kara karanta wannan

Kamfanin da Atiku ya dauko haya sun fara kai bayanan Tinubu wajen Trump a Amurka

Haka kuma ma'aikatar ta ce Angel S. Rampersad mai shekaru 28 daga New York, wanda ya ɓace bayan harin Jordan, yanzu ana kyautata zaton ya mutu.

An kuma tabbatar da mutuwar Michael Emmanuel Swinton mai shekaru 30 daga North Carolina a Iraq.

Trump ya ce sojojin Amurka sun dakile kusan dukkan hare-haren da aka kai Jordan, amma wasu makamai sun tsallake kariya.

Ya ƙara da cewa duk lokacin da Iran ta kashe wani soja ɗan Amurka za ta fuskanci martani mai tsanani. Ya ce hare-haren da Amurka ke kai wa Iran na daga cikin girmama waɗanda suka rasa rayukansu.

Rahotanni sun nuna cewa tun bayan fara yaƙin ranar 28 ga Fabrairu, sojojin Amurka 18 sun mutu.

A yayin bikin karɓar gawarwakin, za a sauke akwatunan da aka lulluɓe da tutar Amurka daga jirgin soji kafin a kai su cibiyar adana gawarwaki domin shirya jana'izarsu.

An bayyana cewa Feehan da Swinton za a ƙara musu matsayi bayan rasuwarsu tare da ba su lambobin yabo irin su Bronze Star, Purple Heart da Combat Action Badge saboda bajintarsu a bakin aiki.

Kara karanta wannan

Sojoji sun yi babban kamu a Borno, sun cafke ɗan kasar waje dake tallafawa ISWAP

Trump ya sake barazana ga Iran

A wani labarin, an ji cewa shugaban Amurka, Donald Trump ya ce Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za ta taba mallakar makamin nukiliya ba.

Donald Trump ya yi barazanar lalata gada ko tashar samar da wutar lantarki a duk lokacin da Iran ta kai hari kan jirgi a mashigar Hormuz Shugaba.

Trump ya kuma bayyana cewa Amurkawa ba sa adawa da yakin da Amurka da Isra’ila suka kaddamar kan Iran.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.