Kasar Iran Ta Gindaya Sharuda 7 ga Amurka kan Maganar Bude Mashigar Hormuz
- Iran ta ce ba za ta sake buɗe mashigar Hormuz ba har sai Amurka ta cika wasu sharudda bakwai da aka cimma
- Kakakin Majalisar Iran, Mohammad Baqer Ghalibaf, ya ce Tehran ta yi watsi da matsin lambar Amurka, tana mai dagewa kan sharuɗɗanta
- Ministan Harkokin Wajen Iran ya ce za a iya buɗe mashigar cikin kwanaki bakwai idan Amurka ta amince da sharuɗɗan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Tehran, Iran - Iran ta ce ba za ta sake bude mashigar Hormuz ba har sai an cika wasu sharudda bakwai da Iran ta gindaya a yarjejeniyar wucin gadi da Amurka.
Kakakin Majalisar Iran, Mohammad Baqer Ghalibaf, ya ce Amurka ta gabatar da wasu shawarwari ta hannun mai shiga tsakani, amma lokacin matsin lamba ya ƙare.

Source: Getty Images
Araghchi ya bayyana hakan yayin ganawa da jakadun ƙasashen waje da jami’an diflomasiyya a Tehran, inda ya ce Iran ta bayyana sharuɗɗanta, cewar Times of Israel.
Ya ce matsayin Iran a kan batun a bayyane yake, kuma ba za a buɗe Mashigar Hormuz ba har sai an cika sharuɗɗan.
Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi, ya ce shirin da Tehran ta gabatar na warware takaddamar da Washington zai iya kai ga sake buɗe mashigar cikin kwanaki bakwai.
Ya ce sharuɗɗan suna da alaƙa da wasu alkawura da Amurka za ta amince da su kafin Iran ta sake buɗe mashigar.
Ministan ya ce Tehran na fatan Washington za ta zaɓi hanyar diflomasiyya domin warware rikicin da ke tsakaninsu maimakon komawa ga amfani da ƙarfin soja.
Sai dai ya yi gargaɗin cewa idan Amurka ta sake zaɓar hanyar soja, Iran ta shirya tsaf don mayar da martani da kare kanta.
Araghchi ya ce Iran ta fi shiri a yanzu fiye da baya, kuma za ta ɗauki duk matakin da ya dace domin kare kanta idan aka kai mata hari.
Karin bayani na tafe....
Asali: Legit.ng
