To Fa: Abin da Kashim Shettima Ya Bukaci 'Yan Najeriya Su Yi Wa Tinubu
- Kashim Shettima ya ce tattalin arzikin Najeriya na dab da durƙushewa kafin cire tallafin fetur da daidaita farashin musayar kuɗi
- Ya roƙi ’yan Najeriya su yi haƙuri da Shugaba Bola Tinubu, yana mai cewa matakan da ya ɗauka sun taimaka wajen kare tattalin arzikin ƙasar
- Shettima ya amince cewa ’yan Najeriya na fuskantar wahalhalu, amma ya ce gwamnati na shirya wasu shirye-shiryen rage musu matsin rayuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Legas - Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya kare sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta aiwatar, yana mai cewa Najeriya na dab da durƙushewa kafin cire tallafin man fetur da daidaita farashin musayar kuɗi.
Shettima ya kuma buƙaci ’yan Najeriya su kasance masu haƙuri da Shugaba Tinubu, wanda ya ce ya ɗauki matakan da suka ceci tattalin arzikin ƙasar.

Source: Facebook
Mataimakin Shugaban Ƙasar ya yi wannan magana ne bayan wata ganawa da Tinubu a gidansa da ke Legas ranar Asabar, 3 ga watan Oktoban 2026, cewar rahoton jaridar Vanguard.
“Muna ci gaba da tuntubar Tinubu”
Shettima ya ce gwamnatin ta ci gaba da kasancewa cikin tuntuba da Shugaban Ƙasa a lokacin da yake balaguro a ƙasashen waje.
Ya ce shugabannin gwamnati suna sanar da Tinubu abubuwan da ke faruwa a Najeriya duk da cewa ba ya cikin ƙasar, jaridar The Punch ta kawo labarin.
“Mun yi matuƙar farin ciki da ya dawo bakin aiki, kuma mun kasance muna tuntubar juna a kai a kai a duk lokacin da yake balaguro a ƙasashen waje."
“Ci gaban kimiyya da fasaha ya sa shugaba zai iya yin tasiri a jagoranci a duk inda yake. Saboda haka, mun kasance muna tuntubar juna. Muna magana kusan kowace rana, muna kuma sanar da shi abubuwan da ke faruwa,” in ji Shettima.
Ya ce Tinubu ya ceci tattalin arziki
Shettima ya ce cire tallafin man fetur da daidaita tsarin musayar kuɗi na daga cikin manyan matakan da gwamnatin Tinubu ta ɗauka domin hana tattalin arzikin ƙasar shiga cikin matsala mai tsanani.
Ya ce lokacin da gwamnatin ta karɓi mulki, ajiyar kuɗin waje na Najeriya ya yi matuƙar ƙasa, inda ya kai dala biliyan 3.9.
A cewar mataimakin shugaban kasar wannan kuɗin bai isa a shigo da man fetur na tsawon wata guda ba.
“Lokacin da muka karɓi ragamar mulki, ajiyar kuɗin waje namu ya yi matuƙar ƙasa, dala biliyan 3.9 ne kawai. Wannan bai isa a shigo da man fetur na wata guda ba."
“Ya kasance yana da ƙarfin hali da yakinin ɗaukar matakai masu tasiri. Cire tallafin man fetur da daidaita tsarin musayar kuɗi daban-daban sun kasance manyan matakai,” in ji shi.
“Tattalin arzikin na dab da durƙushewa”
Mataimakin Shugaban Ƙasa ya ce a wancan lokacin tattalin arzikin Najeriya na gab da durƙushewa.
"A zahiri, tattalin arzikin yana dab da durƙushewa. Ya ceci tattalin arzikin. Ina son ’yan Najeriya su fahimci wannan muhimmin batu."
“Muna kan hanyar zama Caracas. Ya ceci tattalin arzikinmu. Ya ceci ƙasar daga durƙushewa.” In ji shi.
Shettima ya kuma yi kira ga ’yan Najeriya da su kasance masu sassaucin ra’ayi ga Tinubu bisa irin matakan da ya ce ya ɗauka domin kare tattalin arzikin ƙasar.
Ya amince da wahalhalun da ’yan Najeriya ke ciki
Duk da kare manufofin gwamnatin, Shettima ya amince cewa al’ummar Najeriya na fuskantar matsin rayuwa sakamakon sauye-sauyen tattalin arziki.
Ya ce gwamnati tana sane da wahalhalun da jama’a ke ciki kuma tana shirin wasu shirye-shiryen tallafa musu.
“Mun fahimci irin wahalhalun da ’yan Najeriya ke ciki, amma lokutan wahala ba sa dawwama har abada. Masu ƙarfi kuwa suna dawwama,” in ji Shettima.

Source: Facebook
Shettima ya gana da tawagar su Rarara
A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanata Kashim Shettima, ya buƙaci ƙwararrun masu sana’o’in nishaɗi da fasaha da ke Arewa su marawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya domin ya sake lashe zaɓen 2027.
Shettima ya bayyana haka ne yayin da ya karɓi wata tawaga ta masu fasahar nishaɗi daga Arewa ƙarƙashin ƙungiyar Triple-R a ofishin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar APC da ke Abuja.
Asali: Legit.ng


