NSCIA: An Fadada Majalisar Kula da Harkokin Addinin Musulunci Ta Najeriya
- Majalisar Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA) ta sake tsarawa tare da fadada Majalisar Zartarwarta ta Kasa
- Ta nada sabbabin mataimakan babban sakatare hudu a bangarori daban-daban, sannan ta nada Umar Jibrilu Gwandu a matsayin jami’in hulda da jama’a na kasa
- Shugaban NSCIA na kasa, Mai alfarma Sarkin Musulmi ya yi kira ga musulmi da su mutunta hakki da ’yancin mabiyan sauran addinai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA) ta ce ta sake tsarawa tare da fadada Majalisar Zartarwarta ta Kasa.
Abbas Jimoh, jami’in hulda da jama’a na majalisar NSCIA ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, 3 ga watan Oktoba, 2026.

Source: Facebook
Jaridar The Cable ta ruwaito cewa ya bayyana cewa matakin ya biyo bayan shawarwarin da aka cimma a babban taron majalisar harkonin musulunci da aka gudanar a Abuja ranar Juma’a, 2 ga Oktoba, 226

Kara karanta wannan
Ba ɓoye ɓoye, Gwamna Sule ya faɗi jihohi 3 da APC ke fuskantar babban ƙalubale gabanin 2027
Jimoh ya ce shugabannin Musulmi sun halarci taron, ciki har da sarakunan gargajiya na musulmi da kuma manyan limaman masallatan Juma’a na jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya (FCT).
NSCIA ta nada sababbin shugabanni
A cewarsa, taron ya amince da sake fasalin da fadada shugabancin majalisar na kasa, inda aka nada Mahfouz Adedimeji a matsayin mataimakin babban sakatare na kasa da Salisu Shehu a matsayin mataimakin babban sakatare na harkokin kasa da kasa
Sai kuma Abeny Mohammed a matsayin mataimakin babban sakatare na harkokin kamfanoni, sannan Bala Muhammad a matsayin mataimakin babban sakatare mai kula da harkokin gudanarwa.
Sauran nade-naden sun hada da Umar Jibrilu Gwandu a matsayin jami’in hulda da jama’a na kasa (PRO), yayin da Hajia Sekinat Lawal aka nada mataimakiyar jami’in hulda da jama’a (DPRO).
An nada Mairo Mandara a matsayin jami’ar raya kasa, yayin da Abdullahi Musa PenAbdul aka nada shi mataimakin jami’ar raya kasa mai kula da harkokin fasaha.
Haka zalika Fatimah Abdulkarim kuma an nada ta jami’ar kula da harkokin iyali.
Sarkin Musulmi ya yi jan hankali
Fadada majalisar ta zo ne a daidai lokacin da Sarkin Musulmi kuma shugaban majalisar NSCIA, Muhammadu Sa’ad Abubakar III ya yi kira ga zaman lafiya da hakuri tsakanin mabiya addinai a babban taron.

Source: Facebook
Abubakar ya ce babu wanda ya kamata a tilasta masa karbar Musulunci, yana mai cewa ya kamata musulmi su mutunta hakkoki da ’yancin mutanen da ke bin sauran addinai.
Sarkin Musulmi ya garhadi yan siyasa
Kun ji cewa Sarkin Musulmi ya ce bai dace a yi amfani da kudaden da aka samu ta hanyar cin hanci da rashawa wajen daukar nauyin mutane zuwa aikin Hajji ba.
Ya bukaci shugabannin addinai su hada kai da hukumomin yaki da cin hanci domin dakile rashawa da kuma tabbatar da bin doka ba tare da nuna bambancin siyasa ko addini ba.
Sarkin Musulmi ya kuma gargadi malaman addini da su kula da kalaman da suke yi a kan mimbari, musamman a lokacin gudanar da zabubbuka.
Asali: Legit.ng
