Babu Bambanci: Gwamna Ya Yi Addu'ar Samun Tikitin Kirista da Kirista a Najeriya
- Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule, ya yi magana kan samun tikitin Kirista da Krista a siyasar Najeriya
- Ya ce kundin tsarin mulki bai tanadi addini wajen rabon mukamai ba, yana mai cewa ya fi mayar da hankali kan kwarewa da wakilci
- Gwamnan ya ce mataimakinsa Emmanuel Akabe Kirista ne saboda kwarewa, yayin da ya yi martani kan sukar Rabiu Kwankwaso
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Lafia, Nasarawa - Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule, ya yi magana game da siyasar Najeriya ba tare da tsoma addini ba.
Gwamna Sule ya ce yana addu'ar ranar da Najeriya za ta samu tikitin shugaban kasa da mataimakinsa dukkansu Kiristoci, kuma su yi nasara a zabe.

Source: Facebook
Sule ya bayyana haka ne ranar Talata 21 ga watan Yulin 2026 yayin wata hira da ya yi a shirin Politics Today na tashar talabijin ta Channels.
Gwamna ya ƙare tsarin Musulmi da Musulmi
Sule ya mayar da martani kan kalaman da Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da ya yi korafi kan tikitin addini guda a zaben 2027.
Gwamnan ya yi watsi da ikirarin cewa tikitin Musulmi da Musulmi na APC ya nuna wariya ta addini, yana mai cewa Najeriya ma ta kamata ta gwada tikitin Kirista da Kirista.
Sule ya tuna cewa marigayi Cif Moshood Abiola ya taba tsayawa takarar shugaban kasa da tikitin Musulmi da Musulmi a zaben 1993, yana mai cewa irin wannan tsari ya taba samun nasara.
Ya ce:
"Ina addu'ar wata rana Najeriya za ta samu tikitin Kirista da Kirista, kuma zai yi nasara. Wannan shi ne abin da nake fatan gani.
"Kamar yadda kuka gani, zabukan da aka yi da tikitin Musulmi da Musulmi sun yi nasara."

Source: Twitter
Kalaman Kwankwaso sun ba Gwamna Sule mamaki
Gwamnan ya ce ba abin mamaki ba ne Kwankwaso ya soki tsarin tikitin APC saboda yana cikin 'yan adawa, yana mai cewa babu wani gwamna a APC da ya taba bayyana irin wannan ra'ayi.
Ya ce yana girmama Kwankwaso, amma matsayinsa na dan adawa ne ya sa yake magana haka, domin ba zai yi wa APC magana mai kyau ba.
Sule ya ce Sashe na 14(3) na kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadi a tabbatar da wakilci da hada kan dukkan sassan kasa ba tare da nuna wariya ba.
Ya kara da cewa Sashe na 15 ya shafi tsarin federal character dangane da kabilanci, amma babu inda kundin tsarin mulkin ya ambaci addini wajen rabon mukaman gwamnati.
Lokacin da aka tambaye shi ko mataimakinsa Kirista ne, Sule ya amsa da eh, yana mai cewa Emmanuel Akabe ya kasance mataimakinsa tun lokacin da ya hau mulki.
Ya ce"
" A kullum ina da mataimaki Kirista. A Nasarawa haka abin yake tun farko."
Da aka tambaye shi dalilin zaben mataimaki Kirista, Sule ya ce ba don daidaita addini aka yi hakan ba, illa saboda Akabe mutum ne mai kwarewa.
Ya kara da cewa tsarin siyasa ya bambanta daga jiha zuwa jiha, yana misalta Enugu da Bayelsa, inda ya ce akwai shugabanci da mataimaki dukkansu Kiristoci.

Kara karanta wannan
'Na shirya a yi tonon silili': Pantami ya bugi kirji kan abubuwan alheri da ya yi
Gwamna ya magantu kan nasarar APC
A wani labarin, an ji cewa Gwamna Abdullahi Sule ya ce APC ta yi nasara a zaɓen cike gurbi na Sanatan Nasarawa ta Arewa saboda tana samun karbuwa.
Abdullahi Sule ya tarin ƙuri'un da jam'iyyar APC ta samu a zaben cike gurbin da aka yi a Nasarawa ya nuna irin karɓuwar jam'iyyar a jihar.
Hukumar zabe ta kasa (INEC) ta ayyana ɗan takarar APC, Danladi Envulu-Anza, a matsayin wanda ya lashe zaɓen da ƙuri'u 45,362.
Asali: Legit.ng

