An Ji Labarin Abin da Aka Tattauna da Peter Obi Ya Zauna da Jakadan Kasar Switzerland

An Ji Labarin Abin da Aka Tattauna da Peter Obi Ya Zauna da Jakadan Kasar Switzerland

  • Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar LP, Peter Obi, ya tattauna da Jakadan Switzerland
  • Mista Patrick Egloff yana kokarin ganin an fitar da 'yan Najeriya daga cikin kangin talauci da ake fama da shi
  • A bayanin da Obi ya yi, ya bayyana cewa ganawar tasu ta maida hankali ne kan muhimman ɓangarorin cigaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

FCT, Abuja - ‘Dan takarar shugaban kasar Najeriya a NDC idan Allah ya kai mu zaben 2027, Peter Obi ya hadu da Patrick Egloff.

Peter Obi ya yi zama na musamman da Jakadan kasar Switzerland a Najeriya watanni bayan ya samu tikitin takara a zabe mai zuwa.

Peter Obi
Peter Obi da Jakadan kasar Switzerland a Najeriya Hoto: @PeterObi
Source: Twitter

Peter Obi ya zauna da Patrick Egloff

Daga rahoton Tribune aka fahimci Peter Obi yana bayanin yadda wannan tattaunawa za ta iya taimakon Najeriya da mutanenta.

Mista Obi ya yi bayanin abin da zaman nasu ya kunsa, yake cewa zantawarsa da jakadan ta ba da fifiko ne ga cigaban Najeriya.

Kara karanta wannan

Babu bambanci: Gwamna ya yi addu'ar samun tikitin Kirista da Kirista a Najeriya

Daga cikin abubuwan da aka ba karfi akwai harkar ilmi, kiwon lafiya da rage talauci, ‘dan siyasar ya fitar da jawabi a dandalin X.

‘Dan takaran shugaban Najeriya ya kuma yi wa Gwamnatin Switzerland godiya saboda gudumuwar da ta bada wajen gyaran kasar nan.

“Jiya na yi zama da Jakadan Switzerland a Najeriya, Mista Patrick Egloff, kma mun yi tattaunawa mai fa’ida da magana a game da tarihin cigaban kasarku musamman a kan muhimman harkokin da suke kawo cigaba: ilmi, kiwon lafiya da fito da mutane daga talauci.

Obi ya yabi kokarin gwamnatin Switzerland

Obi yana ganin Switzerland ta yi abin yabo wajen wanzar da zaman lafiya da taimakon al’umma a yankin Arewa maso gabas.

Yankin Arewa maso gabas musamman jihohin Borno, Yobe da Adamawa sun yi ta fama da rikicin Boko Haram a shekarun baya.

Tsohon gwamnan na Anambra ya kuma ce zaman da aka yi ranar Talata ta maida hankali wajen ganin yadda za a karafi jama’a.

Obi ya hadu da baturen ne lokacin da shi da Rabiu Kwankwaso suke shirye-shiryen 2027 a tafiyar NDC.

Kara karanta wannan

'Ko makiyana sun san ni ke da Kano,' Kwankwaso ya yi martani ga Ali Modu Sheriff

“Na mika godiya ta a game da gagarumar gudumuwar Gwamnatin Switzerland wajen cigaban Najeriya, musamman wajen taimaka wa muhimman harkoki; manufofin al’ada, taimakon ‘dan adam da na sake gina kasa, musamman a Arewa maso gabas.

Ba a nan kadai aka tsaya ba, taron ya kawo muhimmancin hada-kai da kasashen duniya.

Takarar Obi za ta kai labari a 2027?

Rahoton nan ya ce tsohon shugaban Jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya kalubalanci Rabiu Musa Kwankwaso da Peter Obi masu takara a NDC/

Ya nemi su bayyana ayyukan a-zo-a-gani da suka yi lokacin suna gwamnoni, yake cewa jam'iyyar adawa ta NDC ba za ta iya kai labari ba a zaɓen shekarar 2027.

Ganduje ya ƙara da cewa 'yan Najeriya za su ci gaba da goyon bayan jam'iyyar APC saboda irin nasarorin da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ke samu a mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng