An Raunana Sanata Yari a Zamfara, Yan Majalisa 8 Sun Yi Murabus daga APC
- ’Yan Majalisar daga jihar Zamfara sun fice daga APC, suna zargin jam’iyyar da gazawa wajen magance matsalar tsaro
- ’Yan majalisar sun ce rashin tsaro a yankunan karkara ya ƙara muni, yayin da suka zargi gwamnatin Dauda Lawal
- Sakataren yaɗa labaran APC a jihar ya ce jam’iyyar ba ta samu takardun murabus a hukumance ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Gusau, Zamfara - ’Yan Majalisar Dokokin Jihar Zamfara takwas sun yi murabus daga jam’iyyar APC, suna zargin ta da gazawa wajen magance matsalar tsaro da wasu ƙalubale.
’Yan majalisar, ciki har da wani jigon da ke goyon bayan tsohon gwamna Abdul’aziz Yari sun ce sun fice saboda rashin tsaro, rashin adalci da sauran matsaloli.

Source: Twitter
A wata sanarwa da Daily Trust ta samu, ’yan majalisar sun ce ba za su iya ci gaba da kasancewa cikin jam’iyyar da ta kasa tabbatar da isasshen tsaron jama’a ba.

Kara karanta wannan
Duk da matsalar da ake ciki da Wike, APC ta bayyana shirin da ta yi saboda Tinubu
Dalilin murabus din yan majalisa a Zamfara
Sun bayyana rashin gamsuwa da abin da suka kira gazawar jam’iyyar wajen magance matsalolin jihar, musamman yadda matsalar tsaro ke ƙara muni a halin yanzu.
’Yan majalisar da suka yi murabus sun haɗa da Aliyu Ango Kagara, mai wakiltar Talata Mafara ta Kudu, da Ibrahim Tukur Bakura, mai wakiltar Bakura.
Sauran sun haɗa da Faruk Musa Dosara, mai wakiltar Maradun I, da Barrister Bashir Abubakar Masama, mai wakiltar Bukkuyum ta Arewa.
Haka kuma, Muktaru Nasiru Kaura mai wakiltar Kaura ta Arewa, Nasiru Abdullahi na Maru ta Arewa, Bashar Bello na Bungudu ta Yamma da Bashar Aliyu na Gummi I.
Murabus ɗin nasu ya ƙara dagula al’amuran siyasa a APC ta Zamfara, yayin da rashin jituwa da sauye-sauyen siyasa ke ci gaba da bayyana gabanin zaɓen 2027.
’Yan majalisar ba su bayyana jam’iyyar da za su koma ba bayan ficewarsu daga APC, lamarin da ya bar makomarsu ta siyasa a buɗe.

Source: Original
Martanin APC kan lamarin da ya faru
Da aka tuntubi jam’iyyar APC, sakataren yaɗa labaranta na jihar, Ibrahim Danmadamin Birnin Magaji, ya ce ba a sanar da su hukumance ba.
Ya ce suna jiran takardun murabus daga sassan jam’iyyar na mazabunsu, bayan an tura su ga shugabannin ƙananan hukumomi domin daga bisani a aika musu.
Danmadamin ya ce jam’iyyar ta ga takardun murabus ɗin ne kawai a shafukan sada zumunta, kamar yadda sauran jama’a suka gani, cewar Vanguard.
Ya ƙara da cewa idan jam’iyyar ta samu kwafin takardun a hukumance, za ta bayyana matsayinta kan batun da kuma matakin da za ta ɗauka.
Da aka tambaye shi ko lamarin na da alaƙa da rikicin cikin gida a APC, Danmadamin ya ce jam’iyyar ba ta san wata ƙorafi ba, cewar Vanguard.
A nasu ɓangaren, ’yan majalisar da suka yi murabus sun zargi gwamnatin Gwamna Dauda Lawal da rashin ba matsalar tsaron yankunan karkara isasshen muhimmanci.
Kagara ya ce sun yanke shawarar ficewa daga APC ne saboda jam’iyyar ta kasa magance matsalar tsaro yadda ya kamata, tare da kin wasu yarjejeniyarsu.
Ya ce abin da suke ƙalubalantar gwamnatin Gwamna Dauda Lawal a kai yanzu ya fi muni fiye da baya, don haka ba su ga dalilin ci gaba ba.
Sakon gwamna Dauda ga masu mukamai
An ki cewa Gwamna Dauda Lawal ya ce jami’in da yake ganin bai amfana da gwamnatinsa ya kamata ya yi murabus daga mukaminsa.
Dauda Lawal ya ce gwamnatinsa ta aiwatar da ayyukan more rayuwa sama da N20bn a kowace ƙaramar hukuma cikin shekaru uku.
Gwamnan ya yi kira ga ’yan APC da su daina rarrabuwa zuwa gidajen siyasa tare da haɗa kai a ƙarƙashin jam’iyya guda.
Asali: Legit.ng

