Sanatan Borno Ya yi wa Ministan Tinubu Barazanar Tsige Shugaban Kasa a Majalisa
- Mohammed Tahir Monguno ya gargadi Gwamnatin tarayya cewa rashin aiwatar da kasafin kudi ya saba wa doka
- Sanatan na Borno ta Arewa ya fada wa Ministan kudi hakan babban laifi ne da zai sa a iya tsige shugaban kasa
- ‘Dan majalisar ya bukaci Taiwo Oyedele ya yi bayanin inda kudin shigar kasar da aka ce ana samu yake tafiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Mohammed Tahir Monguno ya soki matsalar da gwamnati take samu wajen aiwatar da kasafin kudi a Najeriya.
Sanata Mohammed Tahir Monguno mai wakiltar Borno ta Arewa a Majalisar dattawa ya yi kaca-kaca da Gwamnatin tarayya.

Source: Getty Images
Sanata Tahir Munguno sun zauna da Ministan kudi
Legit Hausa ta ci karo da bidiyon Sanatan yana wannan bayani a shafin wani Sulaiman Uwais Idris a dandalin X ranar Talata.

Kara karanta wannan
Da gaske gwamnatin Tinubu ta karbo bashin Naira tiriliyan 80? Minista ya yi martani
Sanatan ya ce kin fitar da kudin ayyuka na kasafin kudi laifi ne da ya bayyana da wanda zai iya jawo ga tsige mutum daga ofis.
Wannan barazana ta fito ne da Kwamitin tattalin arziki ya yi zama da Ministan kudi, Taiwo Oyedele a Majalisar tarayya.
Da Taiwo Oyedele yake yi wa sanatoci bayani a ranar Litinin, ‘yan majalisar sun nemi jin ina kudin shigar da aka samu.
Tahir Munguno ya soki yadda aka tsawaita lokacin aiki da kasafin kudi zuwa watan Satumba saboda a aiwatar da ayyuka.
An nemi minista ya fadi ina aka kai kudi
"Ina kudin shigar nan idan ba za a aiwatar da kasafin kudin 2025 ba har sai da muka kai 70% na kasafin 2025 zuwa 2026 da alkawarin cewa za a aiwatar da wannan 30% kafin watan Maris?
"Har Maris ta wuce, ko wannan 30% ba a aiwatar ba."
- Sanata Tahir Monguno
Muddin ba a aiwatar da abin da yake cikin kundin kasafin kudi, Tahir Munguno yana ganin cewa gwamnati ba ta da wani amfani.
Sanatan ya ce:
"Duk hukumomin tsaron da mu ke zantawa da su suna fada mana cewa ba su samu ko sisi a cikin kudin yin manyan ayyuka ba."
Da ya gama sauraron jawabin Ministan kudi, Munguno ya ce maganarsa ta yi dadin ji amma ba a ji inda kudi suka shiga ba.
Sahara Reporters ta rahoto sanatan ya na mai neman jin ina kudin da aka samu suka shiga.
Monguno ya koka cewa duk abubuwan da suke faruwa, ba a ma fara zancen kasafin kudin wannan shekara ta 2026 ba.
"Tambaya ta kenan. Meyasa ba a aiwatar da kasafin kudi? Domin saba wa doka ne kuma za su iya kai wa ga tsigewa."
- In ji sanatan
A kokensa, Munguno ya ce a watan jiya, Gwamnatin Najeriya ta ce an samu N3.7tr amma N2tr kadai aka raba wa kowa.
Sanatan ya tambayi Taiwo Oyedele hikimar rike N1.7tr, ya nemi jin meyasa gwamnati ba ta raba duka N3.7tr din ba.
'Ka fi karfin kujerar’, In ji kanin Ayo Fayose
An ji labari Isaac Fayose ya ce yana taya Ayo Fayose murnar nadin mukaminsa, amma ya ce gara ya ba ‘dan shi kujerar da aka ba shi a REA.
Isaac Fayose ya shawarci yayansa, tsohon gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose, da ya yi watsi da mukamin da Shugaba Bola Tinubu ya ba shi.
Matashin ya raina shugabancin majalisar da ke kula da aikin REA saboda yana ganin mukamin ya yi masa ƙanƙanta kuma zai zama lashe amai.
Asali: Legit.ng

