Fasto Ya Je Isra’ila bayan Korafin Kisan Kiristoci, Ya Yi Addu’a ga Netanyahu

Fasto Ya Je Isra’ila bayan Korafin Kisan Kiristoci, Ya Yi Addu’a ga Netanyahu

  • Fasto Ezekiel Dachomo na Plateau, wanda ya rasa ’yan uwansa a harin Riyom, ya ziyarci Isra’ila domin yi wa Najeriya addu’a
  • Dachomo ya ce ya yi addu’a ga Benjamin Netanyahu da gwamnatin Isra’ila, tare da roƙon Allah ya ba su nasara kan abokan gabansu
  • Faston ya kuma yi addu’a ga Bola Tinubu, Gwamna Caleb Mutfwang da shugabannin Afirka gaba daya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Tel Aviv, Israel - Fasto a Plateau, Ezekiel Dachomo, wanda ya sha magana kan kashe-kashen jihar, ya ziyarci Isra’ila.

Malamn ya ce ya je hakan ne domin abin da ya kira yawon wayar da kan Kiristoci na farko a ƙasashen waje.

Fasto Dachomo ya je kasar Isra'ila
Fasto Ezekiel Dachomo da Benjamin Netanyahu. Hoto: Rev. Ezekiel Dachomo, Marc Israel SELLEM/POOL/AFP.
Source: Facebook

Dachomo ya bayyana hakan a wani saƙon Facebook ranar Juma’a, inda ya ce yana Isra’ila domin yi wa Najeriya, shugabanninta da al’ummar ƙasar addu’a.

Kara karanta wannan

Ganduje: Yadda aka haifi Tinubu a Kano aka raɗa masa suna Ashiru

Ya ce:

“A yau ina Isra’ila ina addu’a ga Najeriya, shugabanninmu da al’ummarmu. Na yi imani da mu’ujizai, kuma na yi imani Ubangiji zai iya sauya abin da ake ganin ba zai yiwu ba.”

Faston ya ce yana haɗa imaninsa da na ’yan Najeriya, tare da yin addu’a ga mutanen da ke neman taimakon Ubangiji wajen magance matsalolin rayuwarsu.

A cikin wani bidiyo da ya wallafa tare da saƙon, Dachomo ya ce ya kuma yi addu’a ga Isra’ila, al’ummarta da shugabanninta.

Ya ce:

“A cikin kwanaki huɗu masu zuwa, Ubangiji zai iya ya buɗe ƙofofi, ya kawo waraka, ya samar da taimako, ya dawo da fata, kuma ya amsa buƙatun zukatanku bisa cikakkiyar nufinsa.”

Ya ambaci Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, majalisarsa da Rundunar Tsaron Isra’ila, yana roƙon Ubangiji ya ba su “nasara kan abokan gabansu.”

Dachomo ya kuma yi addu’a ga Shugaban Najeriya Bola Tinubu, Gwamnan Plateau Caleb Mutfwang da sauran shugabannin Afirka.

Kara karanta wannan

Ciwon zuciya ya yi kamari: Gwamnatin Tinubu ta nemo dabarun yaki da cutar

Ya ce:

“Ina addu’a ga gwamnatina, Bola Tinubu. Ina addu’a ga gwamnatina, Mutfwang a Plateau, ina addu’a Allah ya ba su nasara, Taraba. Ƙasashen Afirka, Afirka ta Kudu, muna addu’a ga Ghana da sauran ƙasashen Afirka.”

Dachomo ya yi fice wajen bayyana damuwarsa kan hare-haren da ake kai wa al’ummomi a Plateau, kuma a baya ya nemi ƙasashen duniya su ƙara mai da hankali kan kashe-kashen jihar.

An ruwaito cewa Dachomo ya yi zargin cewa an kashe mutum tara daga cikin ’yan uwansa yayin wani hari kan al’ummomi a ƙaramar hukumar Riyom a watan Yulin 2026.

Dachomo bai bayyana tsawon lokacin da zai yi a Isra’ila ba, kuma bai bayyana ƙungiyoyin da ke da hannu a wannan yawon wayar da kan Kiristocin ba.

Nnamdi Kanu: Fasto ya zargi Musulman Najeriya

An ji cewa Fasto Ezekiel Dachomo ya nuna damuwa kan ci gaba da tsare Nnamdi Kanu a gidan yarin Sokoto, yana mai danganta lamarin da addini.

Kara karanta wannan

Amaechi ya hango barazanar da ke fuskantar 'yan adawa idan Tinubu ya zarce a 2027

Dachomo ya yi addu’ar samun nasarar Kanu, tare da zargin cewa wasu Musulmi na shirin mamaye Kiristoci da Musulunci, yana mai cewa shirin zai tarwatse.

Faston ya yi ikirarin cewa Kanu zai fito daga gidan yari, yana cewa karfin Yesu Almasihu zai rusa duk wata makarkashiya da ake yi masa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.