Karamar Magana Ta Zama Babba: Oshiomhole Ya Nemi Akpabio Ya Yi Murabus
- Sa-in-sa da aka samu tsakanin Adams Oshiomhole da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya bar baya da kura
- Sanata Oshiomole ya bayyana cewa akwai bukatar a tsige Godswill Akpabio daga shugabancin majalisar dattawa
- Ya ce sababbin dokokin majalisar dattawa sun haifar da rikici yayin da wasu ke ganin ba a yi masu adalci a tsarin ba
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja –Sanatan da ke wakiltar Edo ta Arewa a majalisar dattawa, Adams Oshiomhole, ya bukaci shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, da ya yi murabus daga mukaminsa.
Ya nemi Akpabio ya sauka ne saboda rikicin da ya biyo bayan sauya dokokin Majalisar dattawa da ya yamutsa hazo a zaman majalisa.

Source: Facebook
Jaridar Punch ta wallafa cewa Oshiomhole ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a Abuja ranar Alhamis 7 ga watan Mayu na shekarar 2026.

Kara karanta wannan
Majalisa: Tirka tirkar da ta jawo zazzafan musayar yawu tsakanin Oshiomole da Akpabio
Sababbin dokokin majalisa sun fusata Oshiomhole
Vanguard ta wallafa cewa Oshiomhole ya ce sababbin dokokin da aka yi wa gyara suna da matsalar kuma sun tayar da tambayoyi kan gaskiya da adalci a majalisar dattawa.
Ya ce Akpabio bai kai matsayin cancantar ci gaba da zama shugaban majalisar ba idan aka yi amfani da sababbin ƙa’idojin da ake son tabbatarwa.
A cewarsa:
“Wannan doka tana da babbar matsala. Shugaban majalisar dattawa ya zama shugaban marasa rinjaye a wa’adinsa na farko. Yanzu kuma shi ne yake jagorantar sauya dokokin da za su hana waɗanda suka yi wa’adi ɗaya tsayawa takara.”
Ya ƙara da cewa idan aka amince cewa dole sai sanata ya yi shekara takwas a jere kafin ya zama shugaban majalisar dattawa, to Akpabio ya kamata ya sauka saboda bai cika wannan sharadi ba.
Oshiomhole ya tuno tsohon tsarin majalisa
Oshiomhole ya kuma yi magana kan tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark, yana cewa an ba shi damar shugabanci na tsawon shekara takwas ne bisa tsofaffin dokoki, don haka bai dace a sauya su saboda muradin wasu ba.

Kara karanta wannan
Majalisar Dattawa ta amince da bukatar Tinubu, ta tabbatar da nadin sababbin ministoci 2

Source: Facebook
Sababbin dokokin da majalisar dattawa ta amince da su ranar Talata 5 ga watan Mayu, 2026 sun tanadi cewa sai sanatan da ya yi wa’adi biyu a jere kafin ya cancanci neman manyan mukamai kamar shugaban majalisar dattawa.
Wannan mataki ya haifar da ce-ce-ku-ce a majalisar, inda wasu sanatoci suka ce an yi gaggawar sauya dokokin ne domin rage yawan masu neman shugabanci kafin zaɓen 2027.
Sai dai shugaban kwamitin shari’a na majalisar dattawa, Adeniyi Adegbomire, ya ce gyaran dokokin ba shi da alaƙa da fadar shugaban ƙasa, yana mai cewa gyaran na cikin gida ne kawai domin magance matsalolin kundin tsarin mulki.
A gefe guda kuma, shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa, Opeyemi Bamidele, ya bayyana cewa an sake duba wasu sassan dokokin saboda yiwuwar sabawa kundin tsarin mulki na 1999.
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Jibrin Barau, wanda ya jagoranci zaman, ya ce matakin gyaran wata hanya ce ta tabbatar da bin kundin tsarin mulki.
Sai dai Oshiomhole ya soki yadda aka yi gaggawar amincewa da dokokin tun farko, yana cewa akwai wasu masu ruwa da tsaki da suke son a hanzarta kammala lamarin ba tare da cikakkiyar muhawara ba.
Akpabio da Oshiomhole sun yi musayar yawu
A wani labarin, kun ji cewa Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya yi musayar yawu mai zafi da Sanatan Edo ta Arewa, Adams Oshiomhole.
Lamarin ya faru ne lokacin da Akpabio ke karanto bayanan zaman Majalisa na ranar Talata, wanda sanatoci suka gyara dokar neman shugabanci a zauren.
Sanata Oshimhole ya yi kokarin yin magana amma shugaban Majalisar ya hana shi, lamarin da ya jawo musayar yawu na akalla mintuna 15 kafin a sassauta.
Asali: Legit.ng
