Zaɓen 2027 da Magana: Goodluck Jonathan Ya Fara Yi wa APC 'Aiki'
- Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya nuna goyon bayansa ga ’yan takarar APC a Bayelsa bayan rasa takarar shugaban kasa
- Jonathan ya ce ’yan takarar za su iya wakiltar al’ummominsu yadda ya kamata, tare da bayar da gudunmawa wajen ci gaban Bayelsa
- Ya kuma bukaci ’yan takarar da sauran masu ruwa da tsaki su tabbatar da zaman lafiya, hadin kai da ci gaba a jihar Bayelsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Yenagoa, Bayelsa - Tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, ya bayyana goyon baya ga wasu yan takarar APC duk da bai cikin jam'iyyar.
Goodluck Jonathan ya bayyana kwarin gwiwarsa kan ingancin ’yan takarar jam’iyyar APC da ke neman kujeru a zaben 2027 a yankin Bayelsa ta Gabas.

Source: Twitter
Yan takarar APC sun ziyarci Jonathan

Kara karanta wannan
Doguwa ya fito da abubuwa 2 da za su ceci APC daga shan kaye a jihar Kano a zaben 2027
Jonathan ya bayyana hakan ne a gidansa da ke Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa, lokacin da wata tawaga ta kai masa ziyara tare da gabatar masa da ’yan takarar, cewar Vanguard.
Tawagar, karkashin jagorancin tsohon mataimakin gwamnan Bayelsa, Rear Admiral Gboribiogha John Jonah mai ritaya, ta kunshi shugaban APC na jihar, Warman Weri Ogoriba, da Daraktan NDDC, Samuel Ogbuku.
An ce ziyarar ta kasance domin gabatar da ’yan takarar APC ga Jonathan, wanda aka bayyana a matsayin wani fitaccen jagora daga yankin Bayelsa ta Gabas.
Jonah ya bukaci Jonathan da ya mara wa ’yan takarar baya, yana mai cewa suna da kwarewa, gogewa da halayen da ake bukata domin samar da ingantaccen wakilci.
Ya ce ’yan takarar za su kare muradun al’ummominsu tare da bayar da gudunmawa mai ma’ana wajen ci gaban yankin da jihar Bayelsa baki daya.

Source: Facebook
Yan takarar APC da aka nunawa Jonathan
’Yan takarar da aka gabatar sun hada da Israel Sunny-Goli, mai neman kujerar Sanata mai wakiltar Bayelsa ta Gabas, Jonathan Robinson Obuebite, mai neman wakiltar Brass/Nembe a Majalisar Wakilai; da Jude Amidator Rex-Ogbuku, mai neman kujerar Ogbia.

Kara karanta wannan
Ba ɓoye ɓoye, Gwamna Sule ya faɗi jihohi 3 da APC ke fuskantar babban ƙalubale gabanin 2027
Haka kuma, an gabatar da ’yan takarar APC na Majalisar Dokokin Jihar Bayelsa, wadanda suka hada da Oteigbanyo George Braah na Nembe 1, Edward Brigidi Irigha na Nembe 2 da Alalibo West na Nembe 3.
Sauran sun hada da Daniel Charles na Brass 1, Timi Agala na Brass 2, Abraham Ngobere na Brass 3, Ebiango Okoba Egain na Ogbia 1, Godknows Obein na Ogbia 2 da Gabriel Michael Ogbara na Ogbia 3.
Jonathan ya yaba da ingancin ’yan takarar, yana mai cewa kusan dukkaninsu mutane ne da za a iya amincewa da su saboda kwarewa, iya aiki da gogewarsu.
Ya yi wa ’yan takarar fatan alheri tare da karfafa musu gwiwar ci gaba da jajircewa wajen yi wa al’ummominsu hidima idan aka zabe su, cewar The Nation.
Tsohon shugaban kasar ya bukace su da su dauki siyasa a matsayin hanyar inganta rayuwar al’umma da jawo ci gaba mai amfani ga mazabunsu.
Alfarmar da Abacha ya yi wa Bayelsa
Mun ba ku labarin cewa Goodluck Jonathan ya ce al’ummar Bayelsa za su ci gaba da nuna godiya ga marigayi Janar Sani Abacha saboda ƙirƙirar jihar a 1996.

Kara karanta wannan
Babbar magana: An yi yunkurin kashe ɗan takarar gwamna na jam'iyyar PDP a Najeriya
Jonathan ya ce Bayelsa ta samu gagarumin ci gaba tun bayan ƙirƙirar jihar, duk da cewa har yanzu ba ta kai matsayin da ake fata ba.
Gwamna Douye Diri ya ce ƙirƙirar Bayelsa ta kuɓutar da al’ummar Ijaw daga abin da ya kira zalunci da rashin adalci.
Asali: Legit.ng