Duk da Matsalar da Ake ciki da Wike, APC Ta Bayyana Shirin da Ta Yi saboda Tinubu
- APC a Taraba ta sha alwashin tattara kuri’u domin Bola Tinubu da sauran ‘yan takararta a zaben 2027, duk da tashe-tashen hankulan siyasa
- Shugaban APC na jihar, Abubakar Bawa, ya ce jam’iyyar za ta kai yakin neman zabe gidaje, masallatai, coci-coci da kananan hukumomi
- Tompolo da Gwamna Agbu Kefas sun nemi al’ummar Taraba su sake bai wa Tinubu dama, suna cewa ci gaba da mulki zai karfafa ayyukan ci gaba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Jalingo, Taraba - Jam’iyyar APC a jihar Taraba ta bayyana shirin da ta yi game da zaben shekarar 2027 da ake tunkara.
Jam'iyyar ta sha alwashin tattara kuri’u domin samun nasarar Shugaba Bola Tinubu da sauran ‘yan takarar jam’iyyar a zaben 2027.

Source: Twitter
Shugaban APC na jihar, Abubakar Bawa, ya bayyana hakan ranar Asabar a Jalingo, yayin kaddamar da reshen Taraba na kungiyar PBAT Door-to-Door Movement, cewar Vanguard.
Kungiyar na gudanar da yakin neman goyon bayan sake zaben Shugaba Tinubu, inda ta ce za ta kai sakon jam’iyyar kai tsaye ga al’ummomin jihar.
Wannan mataki ya zo ne yayin da ‘yan siyasar da ke goyon bayan Tinubu ke amfani da dabaru daban-daban, ciki har da Rainbow Coalition karkashin Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike.
Wike ya ce babban burin hadakar shi ne tattara goyon baya domin sake zaben Tinubu, yayin da ya jaddada cewa PDP na da ‘yancin tsayar da ‘yan takara a zabukan gwamna da na majalisun tarayya da jiha.
Bawa ya ce APC na da kwarin gwiwa kan damar da take da ita a Taraba, kuma za ta yi amfani da tsarin jam’iyyar wajen samun nasara a dukkan matakan zaben 2027.
Ya ce shirin tattara jama’a daga tushe zai kai sakon jam’iyyar zuwa gidaje da al’ummomi daban-daban a fadin jihar.
Kungiyar za ta kuma gana da jama’a kai tsaye a gidaje, tare da gudanar da gangami a coci-coci, masallatai da kananan hukumomi.
Darakta-Janar na kungiyar yakin neman zaben Tinubu da Shettima a Taraba, Danladi Baido, ya ce APC za ta gina kan nasarar da ta samu a zaben shugaban kasa na 2023.

Kara karanta wannan
Doguwa ya fito da abubuwa 2 da za su ceci APC daga shan kaye a jihar Kano a zaben 2027
Baido ya nuna kwarin gwiwar cewa jam’iyyar za ta sake tattara gagarumin goyon baya ga Tinubu a Taraba a zaben 2027.
Wanda ya kafa kuma mai jagorantar PBAT Door-to-Door Movement, Government Ekpemupolo, wanda aka fi sani da Tompolo, ya bukaci al’ummar Taraba su goyi bayan Tinubu domin wa’adi na biyu.
Tompolo ya ce gyare-gyaren da gwamnatin Tinubu ke aiwatarwa na bukatar lokaci kafin su haifar da sakamako mai dorewa, yana mai cewa ci gaba da mulkin zai taimaka wajen karfafa manufofin.
Ya kuma danganta sake zaben Tinubu da ajandar ci gaban Gwamna Agbu Kefas, yana mai cewa wa’adi na biyu zai bai wa gwamnan damar ci gaba da aiwatar da shirye-shiryensa
Ya ce:
“Mun na ci gaba da tafiya bisa tsarin Renewed Hope Agenda na Mai Girma Shugaban Kasa."
Ya tabbatar wa mahalarta taron cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da aiwatar da kuma kaddamar da ayyukan ci gaba a fadin jihar.
Dubban yan adawa sun koma APC
An ji cewa dan takarar PDP, Hammed Taoreed Ademola, da ɗan takarar Accord, Adedapo Ojo, sun koma APC tare da magoya bayansu.

Kara karanta wannan
Ba ɓoye ɓoye, Gwamna Sule ya faɗi jihohi 3 da APC ke fuskantar babban ƙalubale gabanin 2027
Ademola ya ce bincikensa ya tabbatar masa cewa tikitin wata jam’iyya banda APC ba zai kai ɗan takara ko’ina a zaɓen 2027 ba.
Shugaban APC na Oyo, Moses Alake-Adeyemo, ya yi maraba da sababbin mambobin, yana mai ba su tabbacin samun dama.
Asali: Legit.ng
