Yadda Dalibar da ba Ta da Hannaye za Ta Gama Digiri a Jami'ar Gombe

Yadda Dalibar da ba Ta da Hannaye za Ta Gama Digiri a Jami'ar Gombe

  • Wata dalibar Jami'ar jihar Gombe da ba ta da hannaye, Maryam Umar, ta kammala karatun digirinta a sashen Economics
  • Maryam ta fuskanci ƙalubale da dama a lokacin karatunta, amma hakan bai hana ta cimma burinta na samun ilimi ba
  • An karrama Maryam saboda jajircewarta, inda wani ya ba ta N50,000, yayin da shugaban jami'ar ya ƙara mata N200,000.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Gombe – Wata dalibar Jami'ar Jihar Gombe, Maryam Umar, wadda ba ta da hannaye, ta shiga cikin ɗaliban da suka kammala karatu a jami'ar bayan ta shafe shekaru tana fafutukar ganin ta cimma burinta na samun ilimi.

Maryam, wadda ta karanci Economics, ta fuskanci ƙalubale da dama sakamakon yanayinta, amma ta ci gaba da karatunta har zuwa kammala digiri.

Kara karanta wannan

An yi wa tsohuwar shugabar matan APC kisan gilla a gidanta da ke Bauchi

Maryam Umar a GSU
Lokacin da aka karrama Maryam Umar. Hoto: MSSN Gombe State University
Source: Facebook

An wallafa hotunan Maryam a lokacin da ake walimar kammala karatu da kungiyar dalibai Musulmi ta shirya a shafin MSSN na Facebook.

An karrama Maryam

A yayin bikin karrama Maryam, wani mutum da ya je taron ya ba ta kyautar N50,000 domin yaba mata bisa jajircewa da ƙudurin da ta nuna wajen neman ilimi.

Sshugaban Jami'ar Gombe, Farfesa Sani Ahmed Yauta ya ƙara mata N200,000 domin taimaka mata wajen ci gaba da rayuwarta bayan kammala karatun jami'a.

Labarin Maryam

Kakakin Jami'ar Gombe State, Naphtali Hugu Ligari, ya bayyana labarin Maryam a Facebook, inda ya ce ya fara ganinta ne a wani gidan mai lokacin da take neman taimakon kuɗi.

Ya ce a lokacin da suka tattauna da ita, Maryam ta bayyana cewa ta nemi gurbin karatu a jami'ar, abin da ya sa aka fara tunanin yadda za a taimaka mata ta samu damar karatu.

Ligari ya ce akwai damuwa a farko kan yadda Maryam za ta iya gudanar da karatu, musamman kasancewar ba ta da hannuwa kuma tana amfani da ƙafafunta wajen rubutu.

Kara karanta wannan

Ba ɓoye ɓoye, Gwamna Sule ya faɗi jihohi 3 da APC ke fuskantar babban ƙalubale gabanin 2027

Ya ce duk da haka, jami'ar ta zabi ta mai da hankali kan abin da Maryam za ta iya yi maimakon kallon ƙalubalen da ke gabanta.

Yadda aka taimaki mata

A cewar kakakin jami'ar, Maryam ta kasance tana zuwa ofishin INTERDEV, inda aka rika ƙoƙarin kawar da matsalolin da za su iya kawo cikas ga karatunta.

Ya kuma yaba wa Ƙungiyar Malaman Jami'o'i ta Najeriya, ASUU, bisa tallafin karatu, sufuri da kwamfutar tafi-da-gidanka da aka bai wa Maryam.

Maryam Umar a GSU
Maryam Umar a wajen walimar MSSN a GSU. Hoto: MSSN Gombe State University
Source: Facebook

Ligari ya bayyana Maryam a matsayin misali na abin da haƙuri, jajircewa da imani za su iya haifarwa, yana mai cewa labarinta ya nuna cewa nakasa bai kamata ta hana mutum samun damar cimma burinsa ba.

Ya ce Maryam, wadda a baya take neman taimakon jama'a a kan titi ba tare da hannuwa ba, yanzu ta kusa zama wadda ta kammala karatun jami'a.

An sace dalibai a Imo

A wani labarin, mun ruwaito cewa masu garkuwa da mutane sun nemi Naira miliyan 950 a matsayin kudin fansa domin sakin wasu ’yan yi wa ƙasa hidima 19 da aka sace a Imo.

Kara karanta wannan

Babbar magana: An yi yunkurin kashe ɗan takarar gwamna na jam'iyyar PDP a Najeriya

Mutanen na cikin motocin bas biyu da suka taso daga Ibadan zuwa sansanonin NYSC na jihohin Abia da Akwa Ibom lokacin da ‘yan bindigar suka kai musu hari.

Rahotanni sun ce masu garkuwar sun tuntubi wasu iyalan waɗanda aka sace, inda suka nemi Naira miliyan 50 kan kowane mutum, lamarin da ya ƙara jefa iyalan cikin damuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng