Ibtila'i Ya Sauka kan Sojojin Israila a Kudancin Lebanon

Ibtila'i Ya Sauka kan Sojojin Israila a Kudancin Lebanon

  • Sojan rundunar IDF guda ɗaya ya samu mummunan rauni, yayin da wani jami’i ya samu matsakaicin rauni a wani hatsari a wurin aiki a kudancin Lebanon
  • Rundunar sojin Isra’ila ta ce an garzaya da sojojin zuwa asibiti domin samun kulawar lafiya, kuma an sanar da iyalansu
  • Ma’aikatar Tsaron Isra’ila ta ce jami’an tsaro 1,318 sun mutu tun bayan fara yaƙin Isra’ila da Hamas a ranar 7 ga Oktoba, 2023.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Tel-Aviv, Israila - Wani sojan Rundunar Tsaron Isra’ila (IDF) ya samu mummunan rauni, yayin da wani jami’i ya samu matsakaicin rauni sakamakon wani hatsarin aiki a kudancin Lebanon.

A cikin wata sanarwa da IDF ta fitar da safiyar Lahadi, rundunar ta ce lamarin ya faru ne ranar Juma’a yayin wani aikin soji.

Sojojin Israila sun samu raunuka a Lebanon
Wasu sojojin Israila a bakin aiki Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Rundunar IDF ta kasar Israila, ta fitar da sanarwar ne a shafinta na X a ranar Lahadi, ga watan Oktoban 2026.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Sabon rikici ya barke a Neja, an samu asarar rayuka

An garzaya da sojojin zuwa asibiti domin samun kulawar likitoci, yayin da rundunar ta tabbatar da cewa an sanar da iyalansu game da lamarin.

Jami’an tsaro 1,318 sun mutu tun 2023

A wani sabon bayani, Ma’aikatar Tsaron Isra’ila ta sanar da cewa jami’an tsaron ƙasar 1,318 sun mutu tun bayan fara yaƙin Isra’ila da Hamas a ranar 7 ga Oktoba, 2023, jaridar Jerusalem Post ta kawo labarin.

Adadin ya haɗa da jami’an Rundunar Sojin Isra’ila, ’yan sandan Isra’ila, hukumar leƙen asiri ta Shin Bet, jami’an kashe gobara da ceto.

Haka kuma, adadin ya ƙunshi masu kula da tsaro da mambobin ƙungiyoyin bayar da agajin gaggawa na yankunan da ake fama da rikici.

Ma’aikatar ta ce alkaluman sun haɗa da jami’an da suka mutu a dukkan wuraren da ake gwabza yaƙi, ciki har da Gaza, Lebanon da Yammacin Kogin Jordan.

Sojoji biyu sun mutu a Gaza

A makon da ya gabata, sojojin IDF biyu sun mutu bayan wani jirgi mara matuƙi da suke sarrafawa ya sauka tare da fashewa a cikin sansanin da suke a Arewacin Gaza.

Kara karanta wannan

Malamar addini ta fito ta gayawa Tinubu gaskiya kan halin da ake ciki a Najeriya

Sojojin, waɗanda suke aiki a ƙarƙashin Birged ta 16, an fara garzaya da su zuwa Barzilai Medical Center da ke Ashkelon.

Sai dai daga baya likitoci suka tabbatar da mutuwarsu. Sojojin su ne Manjo Nadav Kali mai shekaru 24, ɗan Har Halutz, da Manjo Ofek Moalem mai shekaru 23, ɗan birnin Jerusalem.

Ma’aikatar Tsaron Isra’ila ta ce sababbin alkaluman sun haɗa da jami’an tsaro da suka mutu a fannonin daban-daban na rikicin tun daga ranar 7 ga Oktoba, 2023.

Sojojin Israila sun samu raunuka a Lebanon
Firaministan Israila, Benjamin Netanyahu na jawabi a wajen taron UNGA Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Netanyahu ya ziyarci UAE a sirrance

A wani labarin kuma, kun ji cewa firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya ziyarci Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) a sirrance ranar Lahadi, 27 ga watan Satumban 2026.

Benjamin Netanyahu ya gana da Shugaban ƙasar, Sheikh Mohammed bin Zayed, a cewar wata majiya ta Isra’ila da ta san da ziyara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng