Yaki da rashawa a Najeriya
Hukumar korafe korafe da Yaƙi da cin hanci ta Kano (PCACC) ta kai samame wani sito inda ake zargin ana zazzage shinkafar da gwamnati ta bayar a matsayin tallafi.
Bayan tsawon lokaci yana wasn buya, EFCC ta tsare tsohon gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello bayan ya miƙa kansa a hedkwatar hukumar da ke Abuja.
Yahaya Bello ya mika kansa ga hukumar EFCC. An ce tsohon gwamnan na Kogi ya isa ofishin EFCC ne da safiyar Talata, 26 ga Nuwamba tare da lauyoyinsa.
Majiyoyi daga hukumar EFCC sun bayyana cewa hukumar ta fara binciken kongiloli a gwamnatin Edo da ta shude kuma an fara bibiyar motsin Godwin Obaseki.
Gwamnan Ebonyi, Francis Nwifuru, ya umarci a cafke ma’aikata shida da suka karkatar da takardun ma’aikatar Lafiya, kuma an mika su ga ‘yan sanda don bincike.
Hukumar EFCC ta gurfanar da Sulaiman Garba Bulkwang a gaban kotu kan zargin karkatar da N223,412,909 da kuma safarar kuɗaɗen haram daga hukumar REA,
Shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede ya kori jami'ai da aka kama da laifin cin hanci da rashawa. Shugaban ya ce za a cigaba da korar wadanda aka kama da laifi.
Tsohon gwamnan jihar Delta, Dr. Ifeanyi Okowa ya bayyana cewa wasu mutane ne suka cinno masa hukumar yaki da rashawa EFCC saboda wani burinsu na siyasa.
Hukumar yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa EFCC ta ba da belin tsohon gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, ta haramta masa fita zuwa wata ƙasa.
Yaki da rashawa a Najeriya
Samu kari