NNPCL Ya Zargi Dangote da Hadama, Ana Zarginsa da Neman Mamaye Kasuwar Mai

NNPCL Ya Zargi Dangote da Hadama, Ana Zarginsa da Neman Mamaye Kasuwar Mai

  • Kamfanin mai na Najeriya, NNPCL ya zargi matatar Dangote da kokarin mallake kasuwar mai ta Najeriya ita kadai ba tare da barin wasu su samu dama ba
  • Kamfanin ya ce dakatar da lasisin shigo da mai zai iya haddasa karancin mai da tashin farashi a kasar nan yayin da Dangote ya maka shi a gaban kotu
  • Rikicin shari’ar na zuwa ne gabanin shirin matatar Dangote na sayar da hannun jari a watan Satumba, 2026 domin kara habaka samar da fetur a Afrika

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Kamfanin man Najeriya, NNPCL ya zargi matatar Dangote da kokarin kafa karfen kafa a kasuwar man fetur ta Najeriya.

Wannan na zuwa ne bayan matatar Dangote ta kai kamfanin gaban kotu, ana kalubalantar tyadda aka bayar da lasisin shigo da mai da aka bai wa sauran ‘yan kasuwa.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi karin haske kan zargin shirin sauya sunan Najeriya, rusa shari'ar Musulunci

NNPCL ya kalubalanci Dangote
Alhaji Aliko Dangote da hoton wasu ma'aikata a kamfanin sarrafa mai Hoto: Dangote Group, NNPC
Source: UGC

Jaridar Premium Times ta wallafa cewa a cikin takardun da ya gabatar a gaban Kotun Tarayya da ke Legas, NNPCL ya bayyana cewa akwai matsala idan kotu ta amince da bukatar Dangote.

Kamfanin NNPCL ya kalubalanci Dangote

Jaridar Vanguard ta kawo labarin cewa NNPCL ya ce idan kotu ta amince da bukatar Dangote na soke ko takaita lasisin shigo da mai, hakan zai rage gasa a kasuwa tare da jefa kasar cikin matsalar karancin mai.

Kamfanin mai na kasar nan ya ce dan haka ta faru, za a samu tashin farashi da kuma barazana ga tsaron makamashi a fadin Najeriya

NNPCL ya ce barin Dangote ya samu yadda ya ke so zai kara hargitsa kasuwar mai
Motar dakon mai tare da wasu ma'aikatan kamfanin NNPC Hoto: NNPC Limited
Source: Facebook

NNPCL ya bayyana hakan ne a matsayin martani ga karar da matatar Dangote ta shigar a gaban kotu kan Babban Lauyan Tarayya.

Rahotanni sun ce hukumar NMDPRA da ke kula da daidaiton farashin mai a kasar nan ta nemi shiga cikin shari’ar saboda muhimmancin lamarin.

Yadda Dangote ya kai NNPCL kotu

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi tukwicin da zai saka wa 'yan Najeriya da shi idan ya koma Aso Villa

Wannan sabon rikici ya biyo bayan karar da matatar Dangote ta sake shigarwa a watan da ya gabata, inda take neman a soke lasisin shigo da mai da aka bai wa wasu dillalan mai da kuma NNPCL.

Shari’ar ta kara fadada muhawara kan manufofin shigo da mai a Najeriya da kuma tasirin matatar Dangote mai karfin tace ganga 650,000 a rana a kasuwar makamashi. Ana kuma kallon rikicin a matsayin wani babban batu gabanin shirin matatar Dangote na fitar da hannun jari ga jama’a a watan Satumba, 2026 lamarin da ya sake tayar da hankula kan dokokin kasuwa da gasa a bangaren.

A karar da ya shigar, Dangote ya yi zargin cewa lasisin da aka bai wa sauran dillalan mai yana kawo cikas ga kokarin bunkasa tace mai a cikin gida tare da karya tanade-tanaden Dokar Masana’antar Man Fetur ta PIA.

Sai dai NNPCL ya musanta hakan, yana sai cewa dokar ta bai wa hukumomi damar bayar da lasisin shigo da mai ga kamfanonin da ke da lasisin tace mai ko kuma gogewa a harkokin cinikin danyen mai da kayayyakin mai a kasuwannin duniya.

Matatar Dangote na kara habaka

Kara karanta wannan

Kadarar Dangote ta doshi $100m, fitaccen ɗan kasuwa zai kafa tarihi a Afrika

A baya, mun kawo labarin cewa fitaccen attajirin Afrika Alhaji Aliko Dangote ya ce kudin shigar da matatar tace mansa ta ke samu na iya zarce Dala biliyan 100 kafin shekarar 2030.

Ya bayyana matatar Dangote a matsayin daya daga cikin manyan ayyukan masana’antu mafi girma a duniya da aka samar domin wadata jama'a da fetur a jihar Legas da ke Kudancin Najeriya.

Dangote ya ce kamfanin zai mallaki kusan 10% na karfin tace mai na Amurka, kuma idan sabon hasashensa ya tabbata, zai karya kundin tarihin kudi a Afrika na yin jagora a wajen samun kudin shiga.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng