Jigo a Jam'iyyar APC Ya Ruga Amurka Roko wa Najeriya Iri

Jigo a Jam'iyyar APC Ya Ruga Amurka Roko wa Najeriya Iri

  • Tsohon mai neman takarar shugaban ƙasa a APC, Tein Jack-Rich, ya ce ana bukatar karin dankon zumunci a tsakanin Najeriya da Amurka
  • Ya bayyana cewa Najeriya a matsayin wata kafa da masu zuba jari a Amurka ke bukata idan suna son shigo wa cikin kasuwar yankin Afrika
  • Eric Trump ya ce Afrika na da babbar damar zuba jari, yana mai gargadin cewa wasu ƙasashe za su cike gurbin idan Amurka ta ja da baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Jigo a jam'iyyar APC kuma tsohon mai neman tikitin takarar shugaban ƙasa, Tein Jack-Rich, ya bukaci Amurka ta ƙara ƙarfafa alaƙar tattalin arziki da zuba jari da Najeriya.

Ya bayyana cewa cewa hakan zai hanzarta bunƙasar masana'antu, samar da ayyukan yi da kuma haɓaka tattalin arzikin Afrika baki ɗaya.

Kara karanta wannan

Amurka ta sake karfafa Saudiyya ana tsaka da yaki da Jamhuriyar Musulunci ta Iran

Tein Jack-Rich, ya nemi Amurka ta zuba jari a Najeriya
Tein Jack-Rich, Shugaban Amurka Donald Trump Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso/Donald J Trump
Source: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa Jack-Rich ya bayyana hakan ne a birnin Washington DC bayan karɓar lambar yabo a taron murnar cikar Amurka shekaru 250.

Jigon APC ya halarci taron Amurka

Jaridar The Nation ta kawo labarin cewa taron ya samu halartar fitattun 'yan siyasa da 'yan kasuwar Amurka, ciki har da Eric Trump, ɗan shugaban Amurka Donald Trump, da kuma wasu mambobin Majalisar Dokokin Amurka, ciki har da Jim Jordan.

Da yake jawabi bayan karɓar lambar yabon, Jack-Rich ya bukaci Amurka ta faɗaɗa kasuwanci, zuba jari da haɗin gwiwa a fannin fasaha da Najeriya da sauran ƙasashen Afrika.

Ya ce:

"Abin da Afrika ke buƙata shi ne damar da ta dace, haɗin gwiwa da kuma kyakkyawar alaƙa."

Kiran kusa a APC ga Amurka

Rack-Rich ya bayyana Amurka a matsayin abokiyar hulɗa mafi aminci ga Afrika, yana mai cewa ƙarfafa kasuwanci tsakanin ɓangarorin biyu zai amfani tattalin arzikin kowa.

Kara karanta wannan

Bauchi: Tsohon kwamishina ya zama mataimakin dan takarar gwamna a APC

Tein Jack-Rich ya ce Najeriya cibiya ce a Afrika
Shugaban Najeriya Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Getty Images

Jagora a APC ƙara da cewa idan Amurka ta mayar da Najeriya cibiyar harkokin kasuwancinta a Afrika, hakan zai haifar da juyin masana'antu, samar da dimbin ayyukan yi da inganta rayuwar miliyoyin mutane.

A cewarsa, arzikin man fetur, iskar gas, ma'adanai, noma da yawan matasa da Najeriya ke da su sun sanya ƙasar ta zama mafi dacewa ga masu zuba jarin Amurka.

Jack-Rich ya ce ƙarfafa alaƙar kasuwanci tsakanin Najeriya da Amurka zai taimaka wa ƙasar wajen cimma burin zama tattalin arziki na dala tiriliyan ɗaya, tare da buɗe sabbin damammaki ga kamfanonin Amurka.

Amurka ta tura sako ga Najeriya

A baya, mun wallafa cewa duk da turo dakaru da kai hare-hare wasu sassan Najeriya, Amurka ta ci gaba da matsa wa Najeriya lamba game da zargin kisan kiristoci ba bayan ta yi zargin ana sakaci da rayukan mutanen a baya.

A wata ganawa da aka yi tsakanin jami'an gwamnatin Trump da mashawarcin shugaba Bola Tinubu kan tsarim, Amurka ta sake dago maganar cewa akwai bukatar Najeriya ta kara zage damtse wajen hana kashe kiristoci.

Ya ce dole ne a dauki wasu matakai da za su kare rayukan kiristoci a Najeriya a lokacin da Garcia ya gana da manyan jami'an gwamnatin Najeriya da suka hada da Karamin Ministan Harkokin Waje, Ambasada Sola Enikanolaiye.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng