A Karon Farko Messi Ya Yi Magana kan Mutuwar Mahaifinsa Ya Tuno Wasu Abubuwa

A Karon Farko Messi Ya Yi Magana kan Mutuwar Mahaifinsa Ya Tuno Wasu Abubuwa

  • Lionel Messi ya yi jimamin mahaifinsa, Jorge Mese inda ya bayyana shi a matsayin mahaifi, aboki kuma wakilinsa
  • Messi ya ce ya yi kewar saƙonnin mahaifinsa bayan kowane wasa a gasar cin kofin duniya, yana mai cewa hakan ya fahimtar da shi tsananin rashin lafiyarsa
  • Kyaftin ɗin Argentina ya ce zai ci gaba da renon ‘ya’yansa bisa ɗabi’u da tarbiyyar da ya samu daga mahaifinsa da mahaifiyarsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Argentina - Lionel Messi ya yi ta’aziyyar rasuwar mahaifinsa, Jorge Messi, cikin yanayi mai cike da damuwa, inda ya bayyana shi a matsayin “mahaifinsa, abokinsa da wakilinsa”, tare da tuna muhimmiyar rawar da ya taka a tsawon rayuwarsa ta ƙwallon ƙafa

Jorge Messi dai ya rasu yana da shekara 68 a ranar 7 ga Agusta, 2026, a wani asibitin kula da lafiya da ke garinsu Rosario, Argentina, bayan doguwar jinya.

Kara karanta wannan

Fitaccen mawaki ya ɗauki abubuwan da ke faruwa a Najeriya ya kai gaban shugaban Amurka

Messi ya yi wa mahaifinsa bankwana
Lionel Messi tare da mahaifinsa bayan kammala wasa Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A cikin wani dogon saƙo da ya wallafa a Instagram a ranar Laraba, 12 ga watan Agustan 2026, Messi yi jimamin rasuwar.

Messi ya bayyana rashin yarda da rasuwar mahaifinsa, yana mai cewa har yanzu yana fama da wahalar amincewa da cewa ba za su sake magana ko ganin juna ba.

Kyaftin ɗin Argentina ya bayyana cewa mahaifinsa ya sha roƙonsa da ya sake buga gasar cin kofin duniya guda ɗaya, amma yanayin lafiyarsa ya ƙara tsananta kwanaki kaɗan kafin a fara gasar.

Messi ya tuna yadda yake fatan Argentina za ta kai wasan ƙarshe domin mahaifinsa ya samu damar tafiya ya kalle shi yana wasa, sai dai tabarbarewar lafiyarsa ta hana shi halarta.

Messi ya tuna shawarar mahaifinsa

Ya ce ya yi matuƙar kewar samun saƙonnin mahaifinsa bayan kowane wasa, abin da ya sa ya fahimci cewa halin da yake ciki ya yi tsanani.

Messi ya kuma bayyana cewa yana son ya lashe gasar cin kofin duniya domin mahaifinsa, ya kuma kai masa kofin, sai dai a ƙarshe Argentina ta sha kashi a wasan ƙarshe, kuma ya ji cewa jikinsa ba zai iya ƙara ba shi ƙarfi ba.

Kara karanta wannan

Da gaske Obi ya ce sojoji su yi wa Tinubu bore kan albashi?

“Lokacin da na dawo, kana ganin mun yi rashin nasara a bugun fenariti. Ba mu iya magana kan duk abin da ya faru ba. Ba ka samu damar jin daɗin komai ba,” Messi ya rubuta.

Ya ce mahaifinsa yana tare da shi tun farkon tafiyarsa a harkar ƙwallon ƙafa, yana kai shi atisaye bayan ya dawo daga aiki, kuma bai taɓa fashin kallon wasanninsa ba.

“Kuma tabbas, ba ka taɓa fashin ko wasa guda ba. Kai ne ka fi shan wahala wajen kallona ina wasa, kuma kai ne ka fi jin daɗinsa, duk da cewa ba ka cika yaba mini sosai ba,” in ji shi.

Messi ya bayyana mahaifinsa a matsayin mutumin da kullum ya san irin rawar da ya kamata ya taka a kowane yanayi, yana mai cewa shawarwarinsa sau da dama sun zama daidai duk da cewa a wasu lokuta suna samun saɓani.

Messi ya yi alkawarin ci gaba da tarbiyya

“Ka kasance mahaifina, abokina da wakilina. Kullum kana sanin ainihin wanda ya kamata ka kasance a kowane lokaci, kuma ba ka taɓa yin kuskure a kan komai ba,” ya rubuta.

Kara karanta wannan

An kuma: Matar aure ta hallaka mijinta yana cikin barci

Messi mai shekara 39 ya ce zai ci gaba da ɗaukar tasirin mahaifinsa a yadda yake renon ‘ya’yansa, ta hanyar bin ɗabi’u da tarbiyyar da shi da mahaifiyarsa suka ba shi.

“Zan yi kewarka sosai, amma za ka kasance tare da mu a kodayaushe, musamman ta yadda nake renon ‘ya’yana, domin ina koya musu kuma ina renonsu yadda kai da Mama kuka raine ni,” Messi ya rubuta.
Messi ya yi jimamin mutuwar mahaifinsa
Lionel Messi tare da mahaifinsa, Jorge Messi Hoto: leomessi
Source: Instagram

Ya kammala saƙon nasa mai cike da tausayawa da godiya ga mahaifinsa kan komai da ya yi masa, tare da roƙonsa ya ci gaba da kula da iyalinsa daga lahira.

“Ka huta lafiya kuma ka ci gaba da kula da mu daga sama, kamar yadda ka yi a nan. Na gode da komai. Ina son ka, Baba.” In ji shi.

Messi ya sharbi kuka

A wani labarin kuma, kun ji cewa Lionel Messi, ya yi kuka bayan tawagarsa ta Argentina ta sha kaye a wasan ƙarshe na gasar Kofin Duniya na shekarar 2026.

Bayan karɓar lambar yabo ta matsayi na biyu, kamarori sun ɗauki hoton Messi yana zubar da hawaye cike da ban tausayi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng