"Ka da Ku Kuskura"; Gwamna Radda Ya Yi Gargadi kan Matsalar Rashin Tsaro

"Ka da Ku Kuskura"; Gwamna Radda Ya Yi Gargadi kan Matsalar Rashin Tsaro

  • Gwamna Dikko Radda ya bukaci al’ummar Katsina su guji siyasantar da matsalar rashin tsaro da ake fama da ita a jihar
  • Dikko Radda ya ce ya kamata a kara addu’o’in samun zaman lafiya tare da bai wa jami’an tsaro hadin kai
  • Gwamna Dikko Radda ya ce gwamnatin Katsina ta dauki matakai domin karfafa tsarin tsaron jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya bukaci al’ummar jihar su guji siyasantar da kalubalen rashin tsaro.

Gwamna Radda ya kuma bukaci su kara addu’ar samun zaman lafiya mai dorewa tare da bai wa jami’an tsaro hadin kai.

Radda ya yi gargadi kan matsalar rashin tsaro
Gwamna Dikko Umaru Radda na jihar Katsina Hoto: Ibrahima Kaulaha Mohammed
Source: Facebook

Gwamnan ya yi wannan kira ne a ranar Asabar, 1 ga watan Agustan 2026 yayin bikin Yaumul Shukur na shekarar 2026, wanda aka gudanar domin tunawa da hade tsofaffin lardunan Katsina da Daura a shekarar 1934, kamar yadda hadiminsa ya sanya a Facebook.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya dura kan Tinubu bayan ya yi kalamai kan yunwa a Najeriya

Radda ya ce rashin tsaro kalubale ne da ya shafi kowa, wanda ke bukatar hadin kai, addu’a da hadin gwiwa, ba amfani da shi wajen neman wata riba ta siyasa ba.

Radda ya yi kira ga al’umma

Gwamna Radda ya ce bikin Yaumul Shukur ba taro ne kawai ba, illa wata al’ada ta godiya da magabata suka kafa.

“Wannan ba taro ne kawai ba. Al’ada ce ta godiya da magabatanmu suka kafa. Wannan ne ya sa muke gudanar da Yaumul Shukur a ranar 1 ga Agusta a kowace shekara domin gode wa Allah tare da neman kariyarsa ga jiharmu.”

- Gwamna Dikko Radda

Radda ya bayyana jihar Katsina a matsayin jihar da Allah ya albarkace ta da ’ya’ya maza da mata masu hazaka, wadanda suka bayar da gagarumar gudummawa ga Najeriya da sauran kasashen duniya.

Radda ya tuna da tsofaffin shugabanni

Gwamnan ya yi jinjina ga tsoffin shugabannin Najeriya, marigayi Umaru Musa Yar’Adua da Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi yadda za a hana gwamnoni amfani da 'yan sanda jihohi ba bisa ka'ida ba

Ya kuma yabawa fitattun alkalai da suka hada da Mai Shari’a Muhammadu Bello, Mamman Nasir da Umaru Abdullahi, tare da malamai da dama da suka yi fice wajen koyar da addinin Musulunci.

Radda ya ce sun bar gado mai dorewa na rikon amana da tabbatar da adalci.

Ya jaddada cewa gwamnatoci na zuwa su wuce, amma jihar Katsina tana nan, don haka ya zama wajibi kowa ya bayar da gudummawarsa wajen kare ta.

Gwamnati ta karfafa tsaro

Radda ya ce gwamnatin jihar ta kara karfafa tsarin tsaronta ta hanyar daukar ma’aikata, horaswa da samar da kayan aiki ga rundunar Katsina State Community Watch Corps.

Ya ce rundunar za ta rika taimaka wa jami’an tsaro na hukumomi wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Radda ya yaba da ayyukan tsaro

Gwamnan ya yabawa sojoji, ’yan sanda da jami’an Community Watch Corps kan hadin gwiwar da suka yi a wasu ayyukan tsaro na baya-bayan nan.

Ya ce ayyukan sun yi sanadin kashe ’yan bindiga fiye da 40, ciki har da wani fitaccen shugaban kungiyar.

Radda ya yi jawabi kan rashin tsaro
Gwamna Dikko Umaru Radda a wajen taron Yaumul Shukur Hoto: Ibrahima Kaulaha Mohammed
Source: Facebook

Radda ya gargadi ’yan siyasa da sauran masu ruwa da tsaki kan amfani da mutuwar fararen hula wajen neman wata riba ta siyasa.

Kara karanta wannan

An gano mutumin da ya taimakawa Adeyemi a badakalar hukumar bogi ta PFIPC

“Kada wani ya yi amfani da mutuwar mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba wajen neman mulki. Rayuwar dan Adam mai tsarki ce. Dole a ba tsaro muhimmanci fiye da komai.”

- Gwamna Dikko Radda

'Yan bindiga sun kai hari a kotu

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hari a wata kotun shari'a da ke jihar Katsina.

Alkalin kotun ya tsallake rijiya da baya bayan da ya samu ya tsallaka ta taga ya ruga da gudu domin tsira da ransa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng