Tsohon Gwamna Ya Nemi a Tsayar da Fanshonsa, Ya Fada Wa Gwamna Dalilin Yafe Miliyan 8.3

Tsohon Gwamna Ya Nemi a Tsayar da Fanshonsa, Ya Fada Wa Gwamna Dalilin Yafe Miliyan 8.3

  • Ibrahim Hassan Dankwambo ya sanar da gwamnatin Inuwa Yahaya cewa babu bukatar a cigaba da aiko masa da kudin fansho
  • Tsohon Gwamnan na jihar Gombe ya bukaci a tsaida biyan hakkokin shi bayan ya karbi albashin watanni hudu a majalisar dattawa
  • Sanata Ibrahim Hassan Dankwambo ya ce tun da ya bar mulki, gwamnatin Gombe ba ta taba biyan shi alawus din da aka ware ba

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Tsohon gwamna a Gombe, Ibrahim Hassan Dankwambo ya bukaci a dakatar da biyansa kudin fanshon da aka saba ba shi duk wata.

A ranar 4 ga watan Oktoba, Leadership ta ce Sanata Ibrahim Hassan Dankwambo ya aikawa gwamnatin jiharsa wasika a kan hakkokin na sa.

Kara karanta wannan

Gwamna Dauda ya cigaba da tona yadda Matawalle ya yi gaba da dukiyar gwamnati

A kowane wata ana biyansa N694,557 a matsayin tsohon Gwamnan Gombe, amma yanzu ya nemi tsaida karbar fanshon ganin ya zama Sanata.

Tsofaffin Gwamnonin Gombe
Tsofaffin Gwamnonin Gombe da su ke cin albashin Majalisa Hoto: @HEDankwambo
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ibrahim Hassan Dankwambo ya yafe fansho

Dokar fansho ta jihar Gombe ta ba Dankwambo da duk wani wanda ya rike kujerar Gwamna damar cin moriyar kudin wata ko bayan barin ofis.

Sanatan na Arewacin Gombe ya ce ya dauki wannan matsaya ne bayan ya tattauna da kungiyoyi masu zaman kan su da kuma wasu abokansa.

A sakamakon tattaunawar da ya yi da jama’a, ‘dan siyasar wanda ya yi shekaru takwas a kujerar gwamna zai dawo da kudin ya karba a baya.

Sanata Dankwambo ya tafi Majalisar Dattawa

Dankwambo ya zama Sanata mai wakiltar Gombe ta Arewa a majlisa a watan Yunin nan kamar yadda Danjuma Goje ya ke majalisa tun 2011.

Kara karanta wannan

Jerin sunayen gwamnoni da suka yi wa iyayen gidansu a siyasa karan-tsaye

A matsayin ‘dan majalisar dattawa, ‘dan siyasar ya na karbar albashi mai tsoka, baya ga sauran alawus da sauran alfarma na manyan motoci.

Punch ta ce Dankwambo ya nuna tun da Inuwa Yahaya ya shiga ofis, ba a biya shi wasu alawus ba duk da doka ta yi masa tanadi wasu kudi.

"Saboda haka na rubuta wannan domin in bukaci a dakatar da biyan fansho/alawus na wata-watan N694,557.82 da ake biya na a matsayin tsohon Gwamnan jihar Gombe.
Ya kamata a sani cewa tun da na bar mulki a 2019, ban taba cin moriyar wani alawus ko da rashin lafiya, kayan daki, zirga-zirga ko makamancin haka ba."

- Ibrahim Hassan Dankwambo

Rikicin Wike v Gwamna Fabura

Ana da labarin Gwamnonin PDP sun yi taro a Abuja su ka yabi yadda Bola Tinubu ya hana ayi waje da Gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara.

Bala Mohammed, Seyi Makinde, Caleb Mutfwang, Godwin Obaseki, Ahmadu Umaru Fintiri, Ademola Adeleke, Sheriff Oborevwori sun halarci taron.

Kara karanta wannan

Hadimin Buhari ya hango abin da zai faru idan Majalisa ta tsige Gwamnan Ribas

Asali: Legit.ng

Online view pixel