PFIPC: Shugaban Hukumar Bogi Ya Soki Binciken ICPC, Ya Aika Sako ga Shugaba Tinubu
- Shugaban hukumar bogi ta PFIPC, Adeniyi Adeyemi ya nuna rashin amincewa da bai wa hukumar ICPC umarnin bincikar badakalar ma'aikatarsa
- Ya bukaci a kafa kwamitin bincike mai zaman kansa domin gano gaskiya, yana zargin cewa gwamnatin tarayya ta riga ta wanke Femi Gbajabiamila
- Ana sa ran Adeniyi zai gurfana a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ranar Talata, 14 ga watan Yuli, 2026
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Badakalar hukumar Presidential Foreign Intervention Promotion Council (PFIPC) da ake zargin ta bogi ce ta dauki sabon salo bayan umarnin Shugaba Bola Tinubu na gudanar da bincike.
Shugaban hukumar ta bogi, Prince Adeniyi Adeyemi, ya bayyana cewa bai gamsu da binciken da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta ICPC ke gudanarwa kan rikicin kafa PFIPC ba.

Source: Facebook
Adeyemi ya bayyana hakan ne yayin da ya bayyana a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels tv a ranar Litinin, 13 ga watan Yulin 2026.
Adeyemi ya bukaci kafa kwamiti
A cewarsa, hanyar da ta fi dacewa wajen gano gaskiyar lamarin ita ce kafa kwamitin bincike mai zaman kansa, wanda ba shi da alaka da wata hukumar gwamnati.
Ya ce:
"Gwamnati ba zlla ta iya bincikar kanta ba. Shin kuna nufin ICPC za ta tuhumi shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila? Wannan ba zai yiwu ba."
Shugaban PFIPC ya aika sako ga Tinubu
Adeyemi ya yabawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan matakin da ya ɗauka na kafa kwamitin bincike, amma ya ce hakan bai isa ba, kamar yadda Daily Trust ta kawo.
"Ina godiya ga shugaban ƙasa saboda ya saurari koke-kokenmu ta hanyar kafa kwamitin bincike. Amma abin da muke buƙata shi ne kwamitin bincike mai zaman kansa. Fadar Shugaban Ƙasa ta riga ta wanke Gbajabiamila."
Adeyemi ya bayyana hakan ne cikin wata buɗaɗɗiyar wasiƙa da ya aika wa Tinubu, inda ya ce kwamitin dole ne ya kasance mai cin gashin kansa kuma ya haɗa bangarori daban-daban domin tabbatar da adalci.
Ya kuma ce ya kamata wakilai daga Majalisar Ɗinkin Duniya (UN), Amurka, Birtaniya, Tarayyar Turai (EU), ECOWAS da Tarayyar Afirka (AU) su kasance cikin masu sa ido.

Source: Twitter
"Rayuwata na cikin haɗari"
Sai dai Adeyemi ya yi zargin cewa ba za a iya samun cikakken adalci ba idan hukumar da ke gudanar da binciken tana ƙarƙashin gwamnatin da ake zargi.
Ya kuma bayyana cewa yana fargabar kashe shi idan ya miƙa kansa ga jami'an tsaro.
Ya ce:
"Na samu sahihan bayanan sirri cewa ana shirin kashe ni da zarar na bayyana a wurin da babu masu sa ido."
Za a gurfanar da Adeyemi a gaban kotu
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sandan Najeriya za ta gurfanar da Adeniyi Adeyemi a gaban kotu kan zarge-zargen da suka shafi kafa hukumar PFIPC.
Ana zargin Adeniyi Adeyemi da jagorantar wata hukuma mai suna PFIPC wadda gwamnatin taryy ta ce ba ta san da zamanta ba.
Rundunar 'yan sandan za ta gurfanar da Adeniyi Adeyemi a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja ranar Talata, 14 ga watan Yulin 2026.
Asali: Legit.ng

