2027: Martanin Kwankwaso ga Ali Modu Sheriff bayan Ya Ce Su Obi ba za Su Kai Labari ba

2027: Martanin Kwankwaso ga Ali Modu Sheriff bayan Ya Ce Su Obi ba za Su Kai Labari ba

  • 'Dan takarar mataimakin shugaban kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya caccaki Ali Modu Sheriff kan kalaman da ya yi game da Peter Obi da Arewa
  • Sanata Kwankwaso, wanda tsohon dan takarar shugaban kasa ne ya ce Peter Obi ya samu kusan kuri'u miliyan 2.8 a Arewa a zaɓen 2023 da ya gabata
  • Saboda haka ya wuce a raina tasirin da ya ke da shi a Arewacin Najeriya tare da bayyana yakinin cewa Kanawa da yan Arewa za su fitar da Obi kunya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – 'Dan takarar mataimakin shugaban kasa, Rabiu Musa Kwankwaso, ya mayar da martani ga tsohon gwamnan jihar Borno, Sanata Ali Modu Sheriff, kan kalaman da ya yi a kan Peter Obi.

Kara karanta wannan

Kwankwasiyya ta fadi gaskiya kan zargin Kwankwaso da NDC sun samu baraka

Daga cikin abubuwan da Ali Modu Sheriff ya yi magana a kai akwai tasirin Obi a Arewa, inda ya ce ba zai kai labari ba kuma shi kansa Kwankwaso ya samu matsalar magoya baya a jihar Kano.

Kwankwaso ya yi martani ga Ali Modu Sheriff
Sanata Ali Modu Sheriff, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Idon Mikiya/Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

A martanin da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Talata 7 ga watan Yuli, 2026, Kwankwaso ya bayyana cewa ya yi takaicin hirar Ali Modu Sheriff.

Kwankwaso ya dura kan Ali Modu Sheriff

A sakonsa Kwankwaso ya ce bayan dogon lokacin da tsohon gwamnan ya ɗauka ba ya yawan bayyana a bainar jama'a, ana sa ran zai fito da ingantattun bayanai da hujjoji, amma abin da ya gani ya saɓa da hakan.

A cewar Kwankwaso, Ali Modu Sheriff ya yi kuskure da ya yi ikirarin cewa Peter Obi ba zai iya samun gagarumin goyon baya daga al'ummar Arewacin Najeriya ba.

Ya ce abin mamaki ne yadda Sheriff ya ɗauki kansa a matsayin mai magana da yawun dukkannin al'ummar Arewa, yana mai tunatar da cewa a karon farko da Obi ya tsaya takarar shugaban kasa, ya samu kusan kuri'u miliyan 2.8 a yankin.

Kara karanta wannan

'Dalilin da ya sa Atiku ba zai yi nasara ba a zaben shugaban kasa na 2027'

Kwankwaso ya ƙara da cewa idan aka yi la'akari da matsin tattalin arziki da wahalhalun da 'yan Najeriya ke ciki, da kuma yadda mutane da dama ke nuna rashin gamsuwa da gwamnatin APC, tikitin OK jama'a za su bi.

Ba a kabilanci a Kano - Kwankwaso

Tsohon gwamnan jihar Kano, ya bayyana cewa Kanawa ba masu nuna bambancin ƙabila ko ƙin baƙi ba ne, yana mai cewa sun daɗe suna nuna cikakken amincewa da tafiyar Kwankwasiyya.

Kwankwaso ya shaida wa Ali Modu Sheriff cewa babu kabilanci a jihar Kano
Tsohon gwamnan jihar Kano Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

A cewarsa:

"Duk wani tikitin siyasa mai nagarta da tafiyar Kwankwasiyya ta mara wa baya za ta samu goyon bayan al'ummar Kano."

Kwankwaso ya shawarci Sheriff da ya fi mayar da hankali kan matsalolin tsaro da na jin ƙai da suka addabi jiharsa ta Borno, maimakon yin kalaman da za su haddasa rarrabuwar kai a kasa.

An karyata rikici tsakanin Kwankwaso da NDC

A baya, mun ruwaito cewa kungiyar Kwankwasiyya ya yi martani ga rahoton da ke cewa an samu sabani tsakanin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da shugabannin NDC a matakin 'kasa.

Habeeb Saleh Mohammed kakakin kungiyar ya bayyana mamaki a kan yadda ake samun bullar rahoton cewa ana samun mummunar baraka da za ta gurgunta jam'iyyar NDC reshen jihar Kano.

Kara karanta wannan

Yadda haduwa da Peter Obi zai jawo wa Kwankwaso asarar kuri'a a 2027

Game da zargin cewa Kwankwaso ya yi kokarin jan Peter Obi zuwa zuwa jam'iyyar PRP saboda 'baraka a NDC, Habeeb Saleh Mohammed ya bayyana cewa wannan rahoto ba shi da tushe ko kadan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng