2027: Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Magana kan 'Barazanar Kashe Peter Obi'
- Fadar Shugaban Kasa ta ce da'awar Peter Obi cewa gwamnatin tarayya na niyya ta kashe shi karya ce da ba ta da tushe
- Obi ya ce watakila ba zai rayu don ya tsaya takarar shugaban kasa a 2027 ba sanadiyyar barazanar da gwamnati ke yi masa
- Mai ba shugaban kasa shawara Bayo Onanuga ya kira Obi 'maƙaryaci' inda ya kara da cewa babu kamshin gaskiya a zargin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Fadar Shugaban Kasa ta yi watsi da zarge-zargen da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi, ya yi, inda ta bayyana cewa abin da ya fada na da nufin yaudarar jama'a ne ba kuma gaskiya bane.
Legit Hausa ta rahoto cewa Peter Obi ya ce ana shirin kashe shi a wata hirar da shahararren dan jarida, Chude Jideonwo ke gudanarwa.

Source: Facebook
Mai magana da yawun shugaban kaa, Bayo Onanuga ya wallafa martani a shafinsa na X jim kadan bayan hirar da Obi ya yi.
Barazanar kashe Peter Obi
A cikin hirar da ya yi, tsohon gwamnan jihar Anambra ya bayyana cewa matsin da gwamnatin tarayya ke yi masa ya kai wani matsayi da ba zai iya tabbatar da zai kasance da rai har zuwa lokacin zaben 2027 ba.
Ya ce:
"Ba a matsayin dan takara kadai ba, har ma rai ina da shakku a kansa. Duk abin da na yi don neman abinci, wannan gwamnati tana kawo mani cikas. Da gangan. Komai. Don haka akwai yiwuwar, idan sun sami dama, ba zan kasance da rai ba,"
Martanin fadar shugaban kasa
Mai magana da yawun shugaba Bola Tinubu, Bayo Onanuga, ya fitar da wata sanarwa ya karyata dukkan abubuwan da Obi ya ambata, ciki har da da'awarsa cewa an yi masa wani abin da ya shafi motar sa a filin jirgin sama.
Onanuga ya kira Obi da "maƙaryaci na yankan shakku" kuma ya ce yana mai nufin jayaya da sanya gwamnati cikin kowane mawuyacin hali da ya samu a rayuwarsa ta yau da kullum
Daily Trust ta rahoto Onanuga ya ce:
"A matsayinsa na maƙaryaci, Obi na son haɗa gwamnati da kowace matsala da ya samu a rayuwarsa, ya na ƙara gishiri da zargin da ba shi da tushe.
"Da'awarsa cewa watakila ba zai kasance da rai kafin zaɓen Janairun 2027 ba, da kuma cewa ana matsa wa mutane kan gayyatar shi taro, duk maras hujja ce, labarin gizo da koki ne."

Source: Twitter
Onanuga ya ƙara da cewa gwamnatin tarayya ba ta da wata bukata a kan bankin Fidelity, da aka ce Obi na da hannun jari mai yawa a ciki.
Ya jaddada cewa bankin na bunƙasa sosai a ƙarƙashin sauye-sauyen tattalin arziƙi da gwamnatin Bola Tinubu ta ƙaddamar da su.
An gargadi jami'an Tinubu
A wani labarin, mun kawo muku cewa wata kungiya mai rajin kare dimokuradiyya ta yi magana da babbar murya kan ma'aikatar bogi da aka kafa.
Kungiyar ta bayyana cewa akwai sakaci daga wasu manyan jami'an gwamnatin Bola Tinubu, inda ta bukaci su yi murabus daga mukamansu.
Ta yi kira da cewa ya kamata gwamnatin Najeriya ta gaggauta korar su idan suka yi gardamar sauka duk da badakala mai muni da aka gano.
Asali: Legit.ng

