Dara Ta Ci Gida, Sojan da ake Nema Ruwa a Jallo Ya Shigo Hannu
- Sojoji sun samu nasarar cafke wani jami'in rundunar da ake zargi ya na mu'amala da yan ta'adda tare da sayar masu da makamai ana kai hare-hare
- Sojojin sun kama jami'in mai suna Mohammed Yusuf a Maiduguri yayin da ake zarginsa da ƙoƙarin tserewa zuwa wata kasar domin gujewa hukuma
- Rundunar Sojin Najeriya ta ce bincike na ci gaba domin gano cikakken girman abin da ya aikata da kuma duk wanda ya taimaka masa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Maiduguri – Rundunar Sojin Najeriya ta tabbatar da kama wani soja mai suna Private Mohammed Yusuf, wanda a kwanakin baya aka ayyana ana nema ruwa a jallo.
Ana zarginsa da hannu da sayarwa da kuma isar da kayan aikin soja ga ’yan ta’adda da sauran masu aikata laifuffuka dake jawo rashin tsaro a Najeriya.

Source: Twitter
Jaridar Punch ta wallafa cewa wannan na kunshe a cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar ranar Lahadi, 26 ga watan Yuli 2026 bayan an yi fafutuka.
Rundunar soji ta kama jami'inta
A ruwayar Daily Trust, dakarun Operation Hadin Kai na rukunin 7 sun kama Yusuf a tashar mota ta Jidari da ke Maiduguri yayin da ake zargin yana ƙoƙarin tsallakawa zuwa Jamhuriyar Kamaru.
Mukaddashin Jami’in Yaɗa Labarai na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Gabas, Kyaftin Muhammed Goni, ya ce binciken farko ya nuna cewa Yusuf ya tsere daga rundunarsa tun ranar 7 ga Yulin 2026.
Daga nan ya koma Maiduguri inda ake zargin ya ɓoye a yankin Gomari Costain na ƙaramar hukumar Jere tare da taimakon wani abokinsa.
Sojoji tashi tsaye kan rashin tsaro
Sanarwar ta ce kama sojan wani ɓangare ne na ƙoƙarin da rundunar ke yi na rusa hanyoyin da ke bai wa masu laifi tallafi da kara masu karfi.

Source: Facebook
Ta ƙara da cewa an kama shi da misalin 6.30 na yammacin ranar 25 ga Yulin 2026 bayan samun sahihan bayanan sirri na cewa ya na neman guduwa.
A cewar Goni, an ayyana Yusuf a matsayin wanda ake nema tun ranar 23 ga Yulin 2026 saboda irin waɗannan zarge-zarge, kuma kama shi ya nuna yadda amfani da bayanan sirri ke taimakawa wajen gudanar da ayyukan tsaro.
Rundunar Sojin Najeriya ta ce Yusuf yana tsare a hannun jami'ai, inda ake ci gaba da bincike domin gano cikakken S ayyukansa da kuma gano duk wasu mutane da ka iya kasancewa cikin lamarin.
Sojoji sun kai wa yan ta'adda farmaki
A baya, mun wallafa cewa dakarun Operation Fansar Yamma sun fara kai hari tare da neman fitinannun 'yan ta'adda da su ka addabi mazauna jihar Zamfara da kewaye na tsawon lokaci.
Harin sama da na ƙasa sun tarwatsa yunkurin taruwar ɗaruruwan ‘yan ta’adda tare da kashe da dama daga cikinsu a lokacin da su ke tattaunawa kan yadda za su kai wa jama'a farmaki.
Sojojin sun samu nasarar kwato harsasai yayin da dakaru ke ci gaba da sintiri domin hana ‘yan ta’adda sake samun mafaka a yankin bayan an bi sawunsu a lokacin da su ka baje neman mafaka.
Asali: Legit.ng

