2027: Ana Zargin Jagoran NDC na Neman Takaita Tasirin Kwankwaso a Kano
- An gano cewa jam'iyyar NDC na fuskantar barazanar rikici kan rabon takarar Kano gabanin zaben 2027 lamarin da zai iya zama matsala
- Rahotanni sun ce har yanzu Sanata Rabiu Kwankwaso na neman cikakken iko kan takarar Kano, lamarin da ya fusata wasu jiga-jigan jam'iyyar
- Rahoton ya ce shugabannin NDC sun ce suna tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin warware rikicin kafin mika sunayen 'yan takara ga INEC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Jam'iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) na fuskantar yiwuwar rikici mai tsanani yayin da ake shirin babban zaben 2027, sakamakon sabani kan rabon takarar mukamai a jihar Kano.
Rahotanni sun nuna cewa rikicin ya samo asali ne daga takun-sakar da ake yi tsakanin tsohon dan takarar shugaban kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wanda yanzu shi ne dan takarar mataimakin shugaban kasa na NDC, da wasu tsofaffin jiga-jigan jam'iyyar.

Source: Twitter
Nigerian Tribune ta wallafa cewa majiyoyi sun bayyana mata cewa shugabancin NDC na kasa da jagoran jam'iyyar, Sanata Seriake Dickson, na kokarin takaita tasirin Kwankwaso a Kano.
Ana rikici a NDC ta Kano
Wata majiya ta shaida cewa shugabancin jam'iyyar ya shiga rudani kan ko zai bar Kwankwaso ya mallaki kusan dukkannin tikitin takara a Kano ko kuma ya ba wadanda suka kafa jam'iyyar tun farko damar samun wakilci.
Majiyar ta ce:
"Kwankwaso ya riga ya samu tikitin kujerun Sanata da na Majalisar Wakilai, sannan wanda yake goyon baya, Aminu Abdussalam Gwarzo, shi ne dan takarar gwamna. Haka kuma Nasiru Yusuf Gawuna da ya shiga NDC daga APC bai samu abin da yake bukata ba."
Ta kara da cewa duk da haka, Kwankwaso har yanzu yana neman damar zabar 'yan takarar dukkannin kujeru 44 na Majalisar Dokokin Jihar Kano.
Rikicin da ya danno cikin NDC
Majiyar ta ce shugabancin NDC ya yi mamakin yadda Kwankwaso ya ki amincewa da bukatar da aka yi masa ta mika kujeru biyu na majalisar jihar domin sulhu.

Source: Facebook
Rahotanni sun ce yayin da sabanin ke kara kamari, Kwankwaso ya fara tattaunawa da shugabannin jam'iyyar PRP, inda ake zargin wasu daga cikin magoya bayansa sun karbi fam din takara a karkashin jam'iyyar.
Wata majiya ta ce ana zargin Kwankwaso ya yi kokarin jawo dan takarar shugaban kasa na NDC, Peter Obi, zuwa PRP, yana mai cewa jam'iyyar ta fi shahara a Arewacin Najeriya.
Sai dai majiyar ta ce Peter Obi bai amince da wannan shawara ba, saboda yana ganin lokaci ya kure don sake shiga wata jam'iyya tare da fafatawa da Donald Duke.
Haka kuma, wasu jiga-jigan NDC a Kano sun fara barazanar ficewa daga jam'iyyar saboda abin da suka kira gazawar shugabancin kasa wajen shawo kan rikicin.
Yan NDC sun yi korafi
A baya, mun kawo labarin cewa 'yan jam'iyyar NDC da ke Kudu maso Gabas sun yi gargadin cewa akwai matsala gagaruma idan aka ci gaba da kakaba masu 'yan takara gabanin babban zaben da ke tafi.
'Yan jam'iyyar da suka yi magana da murya daya sun ce jinkirin fitar da sakamakon zaɓen fitar da gwani na iya haifar da sabon rikici saboda zargin za a yi masu rashin adalci kafin zaɓen 2027.
Ƙungiyar yankin Kudu maso Gabas ta bukaci a mutunta dimokuraɗiyyar cikin gida tare da miƙa sunayen waɗanda suka yi nasara a sahihin zaɓe ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC.
Asali: Legit.ng


