Sojoji Sun Gano Manyan Kamfanonin Kera Makamai a Filato, An Yi Ram da Mutane

Sojoji Sun Gano Manyan Kamfanonin Kera Makamai a Filato, An Yi Ram da Mutane

  • Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar rage hada miyagun makam sun gano haramtattun wuraren ƙera makamai biyu a jihar Filato
  • Rahotanni sun bayyana cewa jami'an sun samu nasarar kama mutane biyar tare da ƙwace bindigu da kayan aikin ƙera makamai a kamfanonin
  • Sojoji sun ce suna ci gaba da farautar sauran makamai da harsasai da ke hannun miyagun yayin da ake kokarin shawo kan matsalar tsaro a yankin

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Plateau – Dakarun rundunar gaggawa ta Quick Response Force (QRF) ƙarƙashin Operation "Enduring Peace' sun gano wasu haramtattun wuraren ƙera makamai guda biyu a Vom da ke ƙaramar hukumar Jos ta Kudu a jihar Filato.

Kara karanta wannan

Malami zai san matsayar dukiyoyinsa da gwamnati ta kwace a kotu

Sojojin sun kuma kama wasu mutane biyar da ake zargi tare da ƙwace tarin makamai da harsasai daga wuraren da ake gudanar da aikin ƙera makaman.

Sojojin Najeriya sun kama masu hada makamai a Filato
Wasu daga cikin sojojin Najeriya a bakin aiki Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa da yake gabatar da waɗanda ake zargin a hedkwatar Operation 'Eduring Peace', kakakin rundunar, Kyaftin Polycarp Oteh, ya ce nasarar ta samu ne bayan haɗin gwiwa da kuma ƙoƙarin jami’an tsaro.

Jami'an sojoji na aiki a Filato

Kyaftin Polycarp Oteh, ya bayyana cewa farmakin wani ɓangare ne na matakan da rundunar ke ɗauka domin katse hanyoyin samar da haramtattun makamai tare da kare rayuka da dukiyoyin jama’a a yankin da suke aiki.

A cewarsa:

“Wannan samame ya biyo bayan bayanan sirri da aka tattara tare da sa ido na musamman, wanda ya kai ga gano wuraren ƙera makamai guda biyu ba bisa ƙa’ida ba.”

Sojoji sun kwato makamai

Daga Daily Post aka fahimci Kyaftin Oteh ya ce yayin farmakin da sojojin suka kai, an kama mutane biyar da ake zargi suna tsaka da ƙera muggan makamai.

Kara karanta wannan

Alkawarin da sabon ministan makamashi ya dauka kan faduwar turakun wutar lantarki

Sojojin sun gano wurare biyu da ake hada makamai
Taswirar jihar Filato inda aka gano wurin hada makamai Hoto: Legit.ng
Source: Original

Ya ce binciken da aka gudanar a wuraren ya kai ga gano makamai da dama tare da kayan aikin masana’antu da ake amfani da su wajen ƙera su.

A cewarsa, kayayyakin da aka ƙwace sun haɗa da bindigun AK-47 guda tara da aka ƙera, bindiga ƙirar gida guda ɗaya, mujallu huɗu na AK-47 marasa harsasai da kuma wasu sassan bindigun AK-47 guda bakwai.

Sauran kayayyakin sun haɗa da ƙundun bindiga guda 10, kwanson harsasai 36 na alburusai masu girman 7.62mm, injinan revolver guda huɗu, maƙullan bindiga guda 14, injinan huɗa ƙarfe guda shida, injinan goge ƙarfe guda tara da kuma na’urorin walda guda huɗu.

Kara karanta wannan

Tofa: Kotu ta bada umarnin kwace wasu kadarorin tsohon ministan Najeriya, Sylva

Kakakin rundunar ya ƙara da cewa ana tsare da waɗanda ake zargin tare da kayayyakin da aka ƙwace domin ci gaba da bincike.

Ya ce sojojin suna ci gaba da gudanar da wasu sirrikun ayyuka domin tattara sauran makamai da harsasai da ke hannun masu aikata laifi.

An shirga karya kan harin Filato

A wani labarin, wasu rahotanni da suka yadu sun nuna cewa 'yan bindiga sun kai hari a wani wurin jana'iza a Plateau inda aka ce sun kashe mutane da tayar da hankulan jama'a.

Sai dai, an gudanar da bincike wanda ya bankado dalilin da ya sa aka yada batun kai harin na 'yan bindiga, inda aka gano hannun wasu masu aikin kungiyar masu zaman kansu wajen shirya lamarin.

Hakazalika, rundunar 'yan sandan jihar Plateau ta fitar da sanarwa inda ta yi bayani kan hakikanin abin da ya faru tare da tabbatar da cewa babu wasu yan bindiga da suka kai hari kan masu jana'izar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng